← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 128

Sashe 40

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Wurgi da wayar hannun ta Nazili tayi sakwamakwan ganin pictures d'in Sultan da Nihal Wanda Aziza ta turo mata dukewa tayi a wajan tare da fashewa da kuka tana cewa, "nooo! Sultan ni kad'ai ce na dace da kai" da gudu ta shige cikin gida ta wuce aunty lusi dake parlourt ta haura upstart's tana me cigaba da kuka drawer ta bud'e ta Ciro trolley d'in ta, ta fara loda kaya kamar mahaukaciya tana kuka aunty lusi ce ta biyo ta a baya tana cewa, "what wrong with you? Why are you crying? What happened to you? Haka aunty lusi ta rink'a jerawa Nazili tanbaya lokaci d'aya amma ko juyo ta k'iyi se kuka take tana faman had'a kaya cikin trolley, juyo da ita aunty lusi tayi suna facing juna, fad'awa jikin aunty lusi Nazili tayi tare da saki matsanan cin kuka tana cewa, " why Sultan! tana kuka tana cigaba da cewa, "se na kashe koma wacece ta auri Sultan se naga bayan ta bazan tab'a barma ta Sultan ba" tana fad'i zancan tana shashek'ar kuka, a lokacin ne aunty lusi ta gane halin da Nazili ke ciki lalashin ta shiga yi tare da zaunar da ita bakin gado tana cewa, "ya isa kukan haka kin ji daughter ai ba shi kad'ai bane namiji da zaki d'agawa kanki hankali ba, akwai maza da yawa masu kyau da mulki da komai wayan da suka fishi, kuma kema kina kyan nan zaki sami wanda ya fishi, tunda ki kaga haka Allah ya nufa ba mijin ki bane" mik'ewa Nazili tayi tare da jefawa aunty nata wani mugun kallo tayi, sannan t shigewar ta toilet tana wanka tana kuka da sanbatu, haka aunty lusi tayi zaune tana zaman jiran fitowar ta, tana fitowa ko kallan ida take batayi ba lotion ta shafa tare da janyo rigar ta doguwa peack colour me dogwan hannu sannan ta daura black veil ta saka takalman ta masu tsini ta manna bakin glass a idanuwan ta duk da ba wata make up a fuskar tatta tayi kyau sosai, trolley d'in ta ta janyo aunty lusi tace, "ina zaki da yamma nan Nazili? Take it easy mana" Nazili wadda ta juyawa aunty lusi baya tace, "Nigeria zan koma a yau se na katse masun jin dad'in se na watsa farin cikin da suka tanadar wa daran yau," sannan ta ja trolley d'in da karfi ta fice daga gida ko saurara aunty lusi ta k'iyi, zama Aunty lusi tayi saman gado tare da dafe kanta, direct airport Nazili ta wuce.

Kasancewar yau ta kama walima cikin wata bleu Alkyabba aka shirya Nihal tayi kyau sosai kamar ita tayi kanta saboda tsabar kyau, da rana malama ta zo tayi wa'azi mai shiga rai akayi ciye-ciye da lashe-lashe.

Bangaran ango ko yana zaune da friend's d'in shi a part nashi se had'a kaya suke saboda yau suke so subi flight d'in karfe 4:00pm su wuce Abuja wasu kuma su bar k'asar se godiya Ammar ya ke masu kan namijim k'ok'arin da sukayi na zuwa haka shima Sultan d'in ya rink'a zuba masu godiya kamar gaske, bayan sun kamala had'a kayan su Sultan ya kira Sinbul da Barma su fida kayan waje, har bakin mota ya rako su hannu shi na zube cikin aljihu yana murmushi, Alex ya kira wadda ke tsaye daga gefen yace, ya wuce da su airport, murmushi Alex yayi tare da bud'e masu murfi mota suka shige suna tsokanar Sultan wai se sun zo suna, dariyar shak'iyanci Ammar yake yana kallan sultan yace, "gashi zaku tafi ko bari yakiyi ku ga amaryar duk ya tatare ta ya b'oye" dariya su Ahmad suka saki suna cewa, "idan ta tsufa ya bari muganta" murmushin yak'e Sultan yake yana shafa lalausan sumar shi, har suka bar harabar gida harara ya makawa Ammar yace, "wallahi zan ma rashin M idan kana min haka" sultan nata kunfar baki har suka shige part d'in shi.

**********

Bayan yan'biki kowa ya watse gida ya rage hayaniya, Nihal ce zaune saman gado babu abinda take se aikin tunanin da aiyana wa ranta baza juri walakanci da Sultan ze mata tunda itama ba san shi take ba daraja Ammi yaci ta aure shi, wulak'anci da tasha a hannun su gwoggo ya isa, wata gwagwamar ajiyar zuciya ta saki tana bin su yasmin da kallo da suke gyara d'akin ta, Jakadiya ce ta shigo d'akin hannun ta dauke da Alkyabba maroon da doguwar riga maroon a sama kallo Nihal ta bita da shi idanuwan ta taf da kwalla Dan tasan zancan, murmushi Dara ta saki tare da cewa, " ta so mana" shagwabe fuska Nihal tayi ba yadda ta iya haka tabi jakadiya toilet wanka ta mata tare da sata cikin tsimin turare, bayan sun fito dak'i ta zauna da Nihal saman kujera dake facing d'in dressing mirror wata madara ta dauko a cup ta mik'ewa Nihal ta shanye ta tas sannan ta shafe mata jikin ta da wani lotion me fitinan kamshi, a hankali jakadiya ta janyo doguwar riga ta zurawa Nihal maroon colour ce me stones daga gaban rigar zuwa bayan ta wani zare ne hakan se yasa ana ganin na fulanin ta sosai tun daga bayan rigar har zuwa k'ugunta zare ne, make up akayi mata tayi wani masifar kyau bakin nan yasha Jan baki ya k'ara k'ank'ancewa parking d'in gashin ta akayi ya wani nanad'e kamar taliya saman gashin an jera wasu abubuwa masu kyalkyali se daukar idanuwa suke, ita kanta se da ta yaba kyan da ta zuba se dai rigar da aka sa mata kunya take bata Alkyabba maroon Jakadiya ta sa mata tare da feshe ta da turare me kamshi da sanyin dad'i, ammi ce ta shigo tare da washe baki tace, "Masha Allah gaskiya Dara ya kamata na baki tukwici" Nihal ko kunya ta hanata had'a ido da Ammi bayan Ammi ta mata nasiha sosai kamar yadda tayima Sultan sannan tace, a wuce da Nihal part d'in Sultan jikin Nihal ne yayi mugun sanyi ji tayi idanuwan ta sun ciko da kwalla janyo hula alkyabba jakadiya tayi ta rufewa Nihal fuska, yasmin da bariri na bayan Nihal Jakadiya na gaba, Basmal ce ta zo saitin kunnan Nihal tace, "Nasan yau zaki rud'a yayana" waro idanuwan Nihal tayi kamar za tayi kuka tana bin Basmal da kallo, sai da akaje part d'in mom da Gimbiya jalila sannan aka wuce da Nihal part d'in Sultan suna zuwa bakin kofar jakadiya tacewa bafadan bakin kofar ya sanar da Sultan an kawo mashi Amaryar shi, ko minti biyu bafadan beyi ba ya fito yana cewa ya ce Ku shiga kama hannun Nihal jakadiya tayi tare da cewa, "Allah ya bada zaman lafiya" ta saki hannun Nihal a parlour sannan tace ki shiga daga ciki.
Chapter 40 · 0% Book details