Sashe 73
Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Nazili dake zaune a kujera office din ta ta daura kafa daya kan daya tana sanye cikin white shirt da jeans blue kafarta na sanye cikin boot gashin kanta ya wani nanad'e ya zubo har gadan bayan ta, murmushi take tana juya kujera tana tunanin yanzu duk halin da ake ciki an aika Nihal lahira, ringing din wayar tane ya tashe ta zaune number BS data ganine ya sata sakin murmushi saboda ta san by now sun aika Nihal lahira hannu tasa ta dauka tare da kara wayar a kunne abinda Nazili taji ne ya sata mikewa tsaye tana cewa what..! kuna mi haka ta faru, shit what a fuch is this kun watsa min tsarin yanzu shi Tj yana hannu yan'sanda, na shiga uku..! katse wayar hannu ta Nazili tayi tare da aje ta saman table tana cewa, "shit..! shit..! Wannan wani irin shirya me ne" barbaza gashin kanta tayi tare da furta, "na shiga uku asirri na ya tonu, ya Allah wannan wani irin bazan ci ne irin na matsiya ta, suna mi har police su kama su" da sauri Nazili ta dauki car key din ta da handbag din ta tana cigaba da cewa, "ya kamata na tsaida Tj kafin ya tonamin asirri ya kamata nayi wani abu" tana fitowa ta ci karo da sakatariyar ta cikin ladabi tace, "Boss ina zaki je saboda inda an zo neman ki na fadawa masu neman ki" harara Nazili ta maka mata tace, "be zama dole duk inda zani se an sanarwa duniya ba kawai ki ce bana nan" haka Nazili ta baro cikin office din ta ta wuce parking space ta shige motar tare da fisgar motar da karfi kamar zata tashi saman.
Ashad ne ya shigo part din Gimbiya jalila yana cewa, momi..! momi..! Gimbiya jalila da bayi ke mata tausa alamar tayi masu da hannu su fice sannan Ashad ya shigo bedroom yana kallan ta rike da kugu yana cewa, "i now it by this time zan same ki ciki nishadi da an nashuwa, tunda kin sa a kashe matar sultan ba tare da sanina ba..! mikewa Gimbiya jalila tayi zaune tana cewa, "bangane statement din ka ba kara maimaitawa na ji" dariya Ashad ya saki tare da fadawa saman sofa yana cewa, "yanzu dai tana asibitin plan din ki ya rushe se ki kara wani," harara Gimbiya. Jalali ta makawa Ashad tana cewa, "ban san shashanci ni yaushe na samu damar aika ta hakan bayan bana kasar munyi tafiya da maimartaba da yaushe hakan ta faru,? sakatarere Ashad yayi yana kallan Gimbiya jalila yana cewa, "Momi karki ce min ba ke kika kaiwa matar sultan hari ba" girgiza kai Gimbiya jalila tayi tana cewa, "gaskiya bani bace amma waye ya rigamu aika ta abinda mukayi niya dama ba mu kad'ai ya zamar ma kadangaran bakin tulu ba," murmushi Gimbiya jalila tayi tare da mikewa tsaye tana cewa, "zan so naga kowa wanene ko dan mu had'a karfi da karfi mu tarwatsa wannan yaro, koma waye ze aikata haka" dariya Gimbiya jalila ta saki tana cewa, "baya wuce Nazili ita kadai ce na san zata aikatawa Nihal haka amma bamu da tabas, idan ko ita ce ta cika mai zafin nama," Gimbiya jalila ta ida zancan tana shekewa da dariya mugunta, "kasan wani abu my son nasan cewa yanzu bame labarin abinda ke faru saboda san bakin yaran nan da boye-boye baze so kowa ya sani ba, saboda shi gashi me wayau baya so Ammi ta sani ko hehehe, ko ba komai se na rikita gidan da wannan labarin se nasa ammi ta rud'e, bari na shiga cikin gida na watsa labarin kowa ya sani" Gimbiya jalila ta ida zancan tana kokarin fita ruko hannu ta Ashad yayi yana cewa, "momi karki je ina tunanin be kamata ki fadi ba, bana so ki fadi ciwan ammi ya tashi," murmushi takaici Gimbiya jalila tayi tare da makawa Ashad harara tana cewa, "kai har damuwa ka keyi da matar bata damu da kai ba, matar data bud'i baki zata ce sultan Ashe har yanzu tsanar ta bata ratsa zuciyar ka ba, duk wanda ya nuna d'ana ba kowa bane se nuna mashi iya karshi, ta dadi ciwan be tashi ba, idan ta tashi ta mutu, ni ba damuwa ta ba ce, nuna Ashad Gimbiya jalila tayi da yatsa tana cewa, "ka kiyaye ni " Gimbiya jalila ta ida zancan tana fisge hannu Ashad a jikin ta sannan ta fice daga part din ta.
Kukan munafirci Gimbiya jalila ta saki tare da shigewa part din Ammi tana cewa, "mun shiga uku yau kuma abun be tsaya kan sultan ba har da matar shi," ta ida zancan tana saki kukan gulma, Ammi da mom dake zaune suna hira mikewa sukayi a tare dafe da kirji musanman mom da hantar cikin ta kad'a kuka mom ta saki ta san cewa har shi ma Sultan din ba lallai ya tsira ba, wannan wace irin rayuwa ce aita farautar rayuwar d'an ka kamar wani naman daji, Gimbiya jalila ta cigaba da cewa, "sun kashe mu wannan wace irin rayuwa ce, yanzu haka suna Asibitin rai a hannu Allah yarinya karama da ita tasha harsashi tun yanzu bata tsiraba ta fara shiga taskwan rayuwa, shima sultan din ace ya gigice dan har karamar hauka yake, mun shiga uku" Gimbiya jalila tana zancan tana kallan Ammi da ta kasan ido take anan numfashin Ammi ya fara sama-sama tana dafe da kirji hayaniyar da Basmal ta jine ya fito da su ita da jakadiya taro Ammi sukayi ganin zata sume saboda tsabar rikici zauna da ita sukayi saman kujera har a lokacin dana maida numfashin ruwan Dara ta kawo mata a glass cup jikin ta na rawa ta amsa ta sha tana cewa, "na san ba abinda ze sami jika na Sultan da matar shi me yasa Sultan ze boye mana wannan rudanin shiyasa tun jiya hankali na yaki kwanci da rashin ganin su kusa dani, Allah ka tsare min su ya Allah" Ammi ta ida zancan tana sharbar kwalla, mom kuwa mutuwar zaune tayi tana tunanin wani hali ya'yan nata suke ciki, hawaye na gangaro mata, a hankali Basmal ke lallashin ta itama tana matar kwalla, Dara se goge hawaye take Allah sarki Nihal fita, da kyar mom ta iya cewa a kira driver ya kai su asibitin Ammi gani take har da laifin sultan da yaki sanar da su se dai su ji labari daga sama me yasa sultan yake haka ne hawayan idanuwan ta Ammi ta goge, kafin ka ce mi magana ta zagaye gidan, maimartaba dake fada shima labari ya cin masa iya kar rud'eni ya shiga dan kusan a tare suka dunguma zuwa asibiti har da waziri da Adda.
Sultan dake tsaye bakin theater room ta glass door yana hango operation din da akewa Nihal a hankali ya daura hannu shi saman kofar yace, "Allah ya tashi kafadu kin Nihal" juyowa da sultan zeyi ya hango su maimartaba suna nufa shi, rudewa sultan yayi da sauri ya shiga goge hannun shi mai dauke da jini jikin white shirt din shi, ya goge hawayan shi yana kokarin janyo jarumtar shi baya su ko dan su gane halin da ake ciki, murmushi sultan ya kakaro yana kallan Ammi dake nufo shi zuciyar shi na tsana ta harbawa Ammi na isowa wajan shi ta dauke shi da lafiyayan mari dafe kunci sultan yayi, ya kallan Ammi, kuka Ammi ta saki tana, cewa, "mi yasa kake boye mana abinda ke faruwa da kai a tunanin ka bamu sani bane yaushe zaka fara fadin halin da ka shiga, tir da wannan zurfin cikin naka" Ammi ta ida zancan tana kuka tare da rungume sultan gam tana cewa, "bana san na rasa ka sultan dan Allah ka daina boye mana alamarin ka" shima sultan hayawe ne suka shiga yi mashi zarya a hankali Sultan yake cewa, "Ammi ki yafe min duk yadda na so na kare Nihal kar ta shiga wani hali nayi ina tsoran na fada maki bana so ki shiga wani hali amma ki yafe min Ammi," sultan ya ida zancan hawaye na mashi zarya ya cigaba da cewa, "me yasa duniya bata so na Ammi me na aikata haka ake bibiyar rayuwa ta, na tsani duniyar da abinda ke cikin ta" Sultan ya ida zancan yana rushewa da kuka, gabaki daya kowa na wajan se daya zubar da hawaye musanman mom da maimartaba ta, janyo mom maimartaba yayi a jikin shi musanman yadda yaga tana kuka har neman shid'ewa take saboda tausayin d'an nata shafa mata kai maimartaba yayi yana cewa, "ya isa kukan haka, Allah yana tare da d'an ki addu'ar mu kawai yake nema," sauke ajiyar zuciya mom tayi tana cewa, "yaushe ne d'a na ze samu SAUYIN RAYUWA ka duba ka gani tun yanzu an fara bi takan iyallan shi yaushe ne ze samu farin ciki me daurewa," mom ta ida zancan tana kuka tana cewa, "anjefa rayuwar yarinya a hadari saboda d'a na"