← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 128

Sashe 52

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Nazili na isowa bakin kofa bafade ya bud'e mata kofa bayin ta suka tsaya a waje, Sultan da dawowar shi kenan yana kokarin cire necktie d'in shi a parlour kafin ya karasa bedroom, Nazili ta shigo fad'ad'a murmushin ta Nazili tayi tana takowa cikin tafiyar ta me Jan hankali har ta karaso gaban Sultan rike waist d'in shi tayi tare da yi mashi light kiss a kumatu cike da shagwaba tana cewa, "tunda baka nemana yau na zo da kai na" smile Sultan yayi har dimple d'in shi na lomawa tare da furta "Nazili! ciki honey voice d'in shi ya cigaba da cewa, "ba haka bane aiki ne ya min yawa shiyasa" tsare Sultan da ido Nazili tayi wani kyan Sultan na kara rud'a ta musanman da yayi murmushin me kashe ta, gashi kullun kara kyau yake ya Allah Nazili furta a zuciyar ta tare da cewa, "kullun haka kake cewa se ka ce agogo sarki aiki" ta ida zancan tana tsare Sultan da ido da yake fama kokarin cire necktie, murmushi ta yi ta kara matsowa kusa da shi har suna jin saukar numfashin juna su ga wani kamshi turaran Sultan daya rikitata lalacewa tayi gurin kallan shi musanman da yayi kasa da idanuwan shi eyelash din shi sukayi kamar yasa, cikin kisa da kisisi na tace, "lamme help you," murmushi sultan yayi yana cewa, "ba se ki tayani ba," ya ida zancan yana cire necktie din ya zauna saman kujera tab'e baki Nazili ta kumayi tare da cewa, "Ni fa zuwa nayi musha coffee kwana biyu bamu sha tare" murmushi Sultan yayi yace, "kamar kisan shi zan had'a yanzu kafin nayi taking bath had'a mana" da Sauri Nazili ta nufi dining area jiki ta har rawa yake, kananan cups ta dauko tasa saman karamin tray tare da janyo flanks ta zuba ruwan zafi cikin k'ananan cups din kamala had'e coffee din tayi, a hankali ta zura hannu ta cikin gaban rigar ta, ta ciro kulin maganin da Gimbiya jalila ta bata, tana waigen Sultan dake ta fama latsa waya hankalin shi baya kanta, da sauri ta juye mashi duka maganin cikin coffee d'in da ta had'a ta juya da spoon dauko tray da ta yi yayi dai-dai da shigowar Nihal ta na sakarwa Nazili malalacin murmushi tace, "Sultan har ka dawo? dago da sexy eye ball d'in shi yayi yana karewa Nihal kallo Wanda shi kan shi be san yana yi ba of coz he can't resist to stop looking at her beauty face, ringing din wayar shine ya katse mashi tunanin, lokacin yayi dai-dai da mika mashi cup da Nazili ke kokarin yi Nihal ta amsa da Sauri tana cewa, "Nazili be kamata mutum na tare da yunwa ba yasha coffee ya kamata ya fara yin lunch sannan ko" ta ida zancan ta na tsare Nazili da ido tana addu'ar Allah yasa kar Sultan ya juyo ya watsa ta Nazili ce ta katse mata tunani da cewa, "amma dai kin san ina da ilimi bana yin abu up head," murmushi Nihal tayi tare da kallan Nazili hannu ta rik'e da cup din coffee d'in Nihal da Nazili na kallan-kallo Nazili tare da jefa ma juna su kallo me cike da tsana sakin cup din hannun ta Nihal tayi ya fad'i kasa tana murmushi mugunta Waro ido Nazili tayi tare da cewa, "Nihal ! Idanuwan ta waje Dukawa Nihal tayi tana cewa, "wayo Allah na, nayi barna" Sultan da tunda suka abun su hankalin shi na kan wayar da ya ke, kara mashewar cup ne yasa Sultan juyowa da sauri tare da katse wayar daya ke yana kallan Nihal wadda ke duke tana kokarin tatare glass cup, din dake a kasa tana faman ba Nazili hakuri, kamar bada gangan tayi ba, yankewa da Nihal tayine ya sata sakin yar kara da sauri Sultan ya karaso gaban ta tare da rike hannu Nihal dake zubar da jini kuka Nihal tasa cike da shagwaba tana kallan Nazili ta kasan ido hura mata iskar bakin shi Sultan yake yana cewa, "sorry! yana tsare ta da idanuwan shi ma su rikitata kallan juna suka shigayi, Nazili dake tsaye akan su tana kallan yadda Sultan duk yabi ya damu ji tayi kamar tayi hauka idanuwan ta taf da kwala cike da tsanar Nihal. ganin haka yasa Nazili fita daga part din sultan da gudu tana kuka Wanda cikin su ba Wanda ya lura da ita.

Tana isa bedroom nata saman bed ta fad'a tare da sakin kuka tana cewa amma wannan anyi tsinaniya natsane ki Nihal natsane ki mekewa Nazili tayi tana mai cigaba da cewa lokaci yayi da ya kamata muyi fito na fito ba boka ba malam Nihal se na kashe ki, se na kona fuskar dakike takama da ita wadda take daukewa Sultan hankali se na kona ta share hawayan ta Nazili tayi tare da janyo wayar ta dake bedside drawer

********************

Ammar ne da Basmal cikin wani park suna zaune sama wasu resting chair suna facing juna tsakiyar su table da roba ice cream Ammar ne ya tsare Basmal da ido yana aika mata da kallan so tare da daura hannun sa saman na Basmal yace, "My love ni fa yanzu a shirye nake, so na ke su maimartaba su san muna tare nasan zasu ji dadin hakan, na matso na ganki a gida na" ammar ya ida zancan yana rike da hannun Basmal, murmushi ta saki har fararan hakuran ta na baya tare da cewa, "nima haka Darling amma zan fi so na kamala karatuna tunda saura shekara daya" bata fuska Ammar yayi yana cewa, "gaskiya baby bana iya hakuri har se shekara daya, ni fa idan san samu nane ayi bikin nan cikin satin nan" Ammar ya ida zancan yana d'an matse mata hannu yar kara Basmal ta saki tana cewa, "ya Ammar abun har da keta kuma" dariya Ammar yayi tare da cewa "Ni na isa nayima my princess keta" ya ida zancan yana smile tare da daukar spoon d'in ice cream yana feeding din Basmal yana bata tana amsa tare da zuba mashi shagwaba, haka suka rinka zuba soyayya mai cike da kauna.

***

Bayan sun gama dinner da dare kowa ya wuce part d'in shi tsaye Nihal take gaban dressing mirror tana sharce gashin kanta a hankali tana kallan mirror, sultan da fitowar shi daga toilet kenan ya kafe bayan Nihal da kallo jin kamar ana kallan ta, ta baya ya sata juyowa karaf suka had'a ido da sultan sun dau lokaci me tsawo suna kallan juna su Wanda basa iya fassara kallan na minene kasa da idanuwan ta Nihal tayi tana wasa da gashin kanta kauda kai sultan yayi, karasawa Nihal tayi baki drawer zata Ciro blanket mika hannu Nihal tayi tana kokari janyowa amma ta kasa se dage takeyi Sultan ne ya karaso dai-dai lokaci Nihal ta daura hannu ta saman blanket din shima Sultan ya daura hannun shi saman lalausan hannun ta juyowa sukayi a tare suna kallan juna har a lokacin hannun Sultan na saman na Nihal janye hannun ta Nihal tayi da sauri tana gyara gashin kanta, kauda kai sultan yayi tare da mikawa Nihal blanket, yayi gaba se da ya hau saman bed sannan Nihal ta iya furta "na gode" shuru Sultan yayi kamar be jita ba ya ja blanket tare da kashe haskyan d'in kwantawa Nihal tayi saman sofa tayi lamo kamar me bacci haka shima Sultan sun dau lokaci mai tsaho kafin bacci ya dauke su.

*Washe gari*

Shiryawa Sultan yake cikin armani royal black suit da white inner tie d'insa kala daya da suit d'in ta kama jikin sa har wandon pencil ne, ya saka cufflinks nashi masu diamond royal silver stone kafar shi na sanye da black cover shoe, wayar shi ya janyo dake saman bedside drawar layin Ashad ya fara kira ya mashi kusan 3 miss call ba'a dauka ba d'a siriri tsaki ya saki yana kokarin daukar breafcase din shi karaf suka had'a ido da Nihal wadda ke sanye cikin wata gwan blue dai-dai gwiwa santala-santala kafafuwan ta a bayane kallo daya zaka masu kasan kafafun masu taushi ne tun daga kafafuwan ta Sultan ya fara binta da kallo har ya sauke su kan fuskar Nihal, kallan gashin ta dake baje a kafad'ar ta se shining yake dauke kai Sultan yayi da sauri tare daukar briefcase din shi ya fice, tabe baki Nihal tayi tana cewa mutum kullun cikin bakin rai kamar fir'auna mtsww.

Daga labile window parlour shi Ashad yayi yana leka Sultan dake mikawa Alex briefcase d'in shi tsaki Ashad ya saki tare da cewa, "shashasha se ka gane kuran ka" wayar shi dake saman kujera ya dauka yana sakin murmush mugun ta number ya shiga kira bugu daya aka dauka tare da Sallama murmushi Ashad ya saki tare da cewa, "Nas ina so ka canza alururin da za'ayi ma Alhaji Adamu kafin a shigar da shi theater ka tabata kayi min aiki da kyau"
"toh" Nas yace tare da kashe wayar yana kashewa ya wuce office d'in Sultan a hankali ya murd'a kofar ya shiga ya canza alururi ya fito da sauri.
Chapter 52 · 0% Book details