← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 128

Sashe 19

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sultan na zaune saman kujera har yanzu idanuwa shi a lumshi Alex ne yace, "Sultan you need to rest, be kamata kasa ma ranka tunani ba gode ma Allah ya kamata kayi, Asiya kuma kanta tayi mawa akwai yan'mata da yawa wayan da zasu so ka because of god you have to cool down my man" daga kai kawai Sultan yayi tare da hawa saman bed Alex ya ja mashi blanket ya kashe haskyen dakin ya fita ya Dade yana juye-juye kafin bacci b'arawo ya sace shi.

*****

Ko da Nihal ta koma gida su gwoggo basu nan hakan ya mata dadi tana aje hijabin ta, aka fara kiraye-kirayan sallah magrib hakan ba k'aramin dadi ya mata ba ta San yau ba talla dare, alwala ta dauro ta fara jera salolin da ake binta bayan ta idar ta fito da umma da kyar ta zauna da ita a tsakar gida sannan ta shige daki, ta fara sharewa da gyarawa se da tayima dakin fes sannan tasa ruwa ta wanke simintin dakin ta fido tabarma umma ta wanke ta tas da abin shinfidar, bayan ta kamala ta jawo ruwa a rijiya ta juye a bokitin wankan ta cirewa umma kaya, ta mata wanka tare da wanke mata kai ta nanade ta da sani sannan itama ta ja ruwa ta shige toilet ta fara wanka se da ta wanke jikin ta tas sannan ta kwance dankwalin kanta gashin ta ya zubo har gadan baya sabulu tasa ta wanke gashin tas, dama duk ya ishe ta da tsami jima take kamar ta yanke shi ta huta, wani irin dadi ya lulube ta data fito wanka wani irin wasai taji idan zata iya tunawa rabanta da wanka ta kai sati biyu kunya ce duk ta rufe ta a fili tace, "yaya dai yana shan kamshi" hhhh lol😂, tana gama shiryawa aka fara kiraye-kirayen sallah isha sallah ta gabatar sannan ta janyo ledar tsiran umma dana magunguna ta sai da suka ci suka koshi har da gatsa sannan Nihal ta debo ruwa tasha magani, kasancewa yau anyi tsaf ta kuma dama gashi cikin magunguna har Dana sa bacci kafin kace mi wani lafiyayan bacci ya sure ta.

*Asuba ta bari*

A hankali yasa hannu ya zame blanket din dake jikin shi, tare da sauko da santala-santala kafafuwan shi k'asa wata iska ya murzar tare tura hannu shi cikin sumar kanshi yana barbazawa sannan ya mike yana kallan mirror tare riqe k'ugu, bude kofar da akayi ne ya sasa juyowa sinbul ne da barma Kansu a sunkeyi be ce masu k'ala ba ya fara cire bottle din rigar shi ya mik'a hannu Sinbul ya bashi bathrobe ya saka sannan ya shige toilet, kafin ya fito bayi mata har sun gyara part din sai kamshi yake da zanyin AC a hankali ya fito daga toilet yana goge jikin shi da k'aramin towel, yadda aka gyara dakin ya mashi kyau sosai dressing mirror ya nufa tare da zama saman sofa ya janyo lotion ya fara shafawa bayan ya gama, ya tsaya barma ya karaso riqe da suit din shi dark blue da yar riga ciki light blue riga barma ya fara saka mashi sannan ya bar Sultan yasa bottle din rigar da kanshi kusan dai da taimakwan su barma Sultan ya shirya sannan ya feshe jikin shi da turaran shi me kamshi da tsada Al-Haramain tuni dakin ya gauraye da kamshi dadi, zama yayi Sinbul ya sa mashi covered shoes din shi black, ya Allah Sultan looks breathtaking handsome, mikewa yayi Barma ya bashi briefcase din shi masha Allah wani irin kyau Sultan ya zuba ga sajan face din shi ya kwanta luf-luf dan siririn glass din shi ya zura tare da sa agogo shi silver na azurfa da zube.

duk inda ya wuce bayi ke zubewa suna kai gaisuwa d'aga masu hannu kawai yake, part din Habibty ya fara shiga bayi nata hada-hada su minal cikin shirin su na zuwa school suka rugo da gudu suka rungume Sultan suna cewa, "morning yaya, morning too" pack ya Shiga yi masu d'aya bayan d'aya can se ya tsaya yana cewa, "ina Nasim? Minal ce tace, "yana dakin momi shi, ok oya kuyi sauri ku wuce school ku shafa min kan Nasim," to suka ce tare da ficewa da gudu daga parlour, k'arasawa dakin habibty yayi tana zaune saman wata kujera kamar gado tayi kwanciyar sarauta gashin ta ya baje saman kujera kayan ta sun baje har k'asa wani k'ayatacan murmushi Gimbiya Nadiya ta saki umma Sultan kenan, k'arasowa yayi tare da cewa, " habibty hannu ta mik'a mashi yayi kissing hannu tare da zama gefen ta yace, "Habibty ina kwana, shafa gefen face din shi habibty tayi tace, " lafiya lau Sultan, my boy kullun k'ara girma kake fa, kaga ammi har ta fara min magana kak'i fito da mata kayi aura" bata fuska Sultan yayi yace, "Habibty ni fa har yanzu ban shiryama aure ba har yanzu ban samu wadda hankali ya kwanta da ita ba habibty," harara wasa Gimbiya ta sakarwa Sultan tare da ja mashi kunne yar k'ara ya saki yana cewa, "aushhhh habibty am sorry" sakin kunnan tayi tace, "yadda kunnan ka yaji zafi haka nake so ka samu min inlow" d'aga kai Sultan yayi yana cewa, OK Habibty pack ya mata a cheeks nata sannan ya fita, direct part din ammi ya shiga tana dining area tana breakfast k'arasowa yayi tare da kissing forhead din ta yana cewa, "matar kinsha maganin ki kuwa harara ta aika mashi cike da tsiwa ammi tace, "bansha ba kuma bazan sha ba ni fa na gaji da wannan shaye-shayen anwani maidani kamar yar k'waya" yar dariya Sultan yayi har dimple din shi na lomawa yace, "yi hakuri please kisha kinji, Dara ya kwalawa kira wato jakadiyar gida da sauri ta k'araso tana washe baki, gaishe ta Sultan yayi sannan ya ce ta daukowa ammi magunguna ta, da sauri tashige daki ta kwasosu murmushi ya kuma saki tare da amsa yana kallan ammi wadda tayi kicin-kicin rai, balo su yayi tare da bata ruwa a cup yace, " please matar yi sauri ki hadiya" harara ta kuma watsa mashi tare da shan magunguna, pack ya mata a goshi yace, "good" ko k'ala bata ce ba ta cigaba da breakfast din ta

Nazili ce ta fito sanye da wado da riga riga, orange Wando milk irin budade me kamar fantalo yadin me laushi se riga me wuya me dan fadi gefe daya kafad'ar ta ta fito, gashin kanta tayi parking nashi waje daya tasha Jan bakin hannu rike da fost milk kafar ta na sanye da takalmi me tsini irin me igiyoyin dinan sai zubaba kamshi take cikin isa take takowa komai na jikin ta amsawa yake saboda yanayin tafiyar da take, bayi na gaishe ta, tana yamutsa fuska dining area ta nufa hango Sultan da tayi tsaye ya sata sakin murmushi tare da k'arasawa wajan Sultan hannu ta zagaya a waist din Sultan tare da yin dage tayi kissing goshin shi tana smile ta dan zame jikin ta tace, morning Sultan, morning Nazili, shafa cheeks din ammi tayi tana smile ta aje fost din ta saman table tare da daukar cup din coffee ta kai baki, ammi tace, "Har kin fito, Eh Ammi na fito ta fada tana k'ara kurbar coffee, ammi ta k'ara katse da cewa Nazili amma dai ba haka zaki fita ba, ya kamata ki sa veil kafin ki fita," kwabe fuska Nazili tayi tace, " Ni fa.. Wani kallo da Sultan ya watsa mata ne yasa ta yin shuru sannan yayi ma ammi pack ya fice, Nazili ta bishi da kallo.

Sara ce ta fito tana mika da misalin karfe 7:00am ware idanuwa tayi ganin murhu ba alamar wuta gwoggo ta fara kwalawa kira cikin tsiwa tana cewa, "gwoggo!! Gwoggo!!, gwoggo dake baccin gajiya jiya ce, ta tashi a zabure tana gyara zanin ta ta leko kamar an watso ta tana cewa, "lafiya Sara" murhu Sara ta shiga nunawa gwoggo wata uwar ashar gwoggo ta saki tana cewa, "kutumar uba amma yarinyan nan anyi tsinaniya kenan itama bacci take dan uwarta" Sara dake gefe tace, "shikenan gwoggo tajamin lati dama bakin ciki take da karatun nawa, ke takewa bakin ciki ko ni so take ta haram tamin cinikin safe".

Ruwan randa gwoggo ta juye a bokiti me sanyi ta nufi dakin su Nihal wage labilan dakin tayi tana kallan su Nihal suna ta shara bacci bokitin ta daga ta shek'a masu su Nihal a razane Nihal ta mike umma kuma nata zare ido.

```Taku har kullun Salma mas'ud nadabo ```
[1/7, 2:25 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞

*Story*
*And*
*Writing*✍🏽
*By*
*Salma mas'ud nadabo*👑

🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
(```We are the among the rest```)

*Page: 39_40*
Chapter 19 · 0% Book details