Sashe 67
Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Fitowa Nihal tayi daga hall tare da zuwa wajan wata resting chair ta zauna tana kallan students dake wuce wa,nana ce ta karaso tare mikawa Nihal hannu suka gaisa murmushi Nana ta saki tare da zama kusa da Nihal tana cewa, "kema baki zuwa break ne" girgiza kai Nihal tayi tana cewa, "bana jin yunwa shiyasa"
"Kamar ni kenan" daga mata kai Nihal tayi hira suka taba sama-sama sannan aka koma exam hall nan ma basu wani dade ba, exam tayiwa Nihal dadi sosai tare da Nana suka fito lokacin driver ta ya zo daukar ta kallan Nihal tayi tare da cewa, "tunda gida zaki tafi why not muyi dropping naki" murmushi Nihal tayi tana cewa, "na gode sosai Nana amma munyi da yaya na ze zo dauka ta" daga kai Nana tayi tare da cewa, "toh shikenan ki gaida gida"
"Ze ji" Nihal ta fad'a a takaice, har Nana ta bale murfin mota ta juyo tana cewa, "gashi ban amshi number ki ba"
"Eyya Nana bani da waya"
"Toh shikenan se mun had'e gobe" murmushi Nihal tayi sannan Nana ta shige mota, guri Nihal ta samu ta zauna tana kallan mutane masu wuce wa, ta dau lokaci mai tsaho tana zaune zaman jiran Sultan shuru be zo ba.
Motocin Sultan ne suka jeru dan zuwa makaranta daukar Nihal, daya daga cikin yaran Tjee ne dake jingine jiki bishiya ne ya leko ganin motocin Sultan ya sasa watsa busoshi kan titin ji kake tayoyi na bada tas! tus! Suna fashewa Sultan dake zaune a bayan seat ne ganin mota ta tsaya yasa Sultan cema musa driver "mike faruwa.! cikin ladabi yace, "ranka yadade taya ce ta bashe.! b'ale murfin motar Sultan yayi ya fito a tare suka fito da Alex kallan juna sukayi da Sultan sannan Alex, yace, "Sultan ya kamata ka shige mota wajan nan akwai matsala," ya ida zancan yana dukawa yana duba busar dake zube a kasa, shima sultan dukawa yayi tare da kallan busar sannan ya kalli agogan dake makale a hannun shi wayar shi ya ciro da sauri ya shiga Kiran driven shi na gida tare da shigewa cikin mota ya zauna yana duba agogan dake makale a hannun shi gaban shi na kara faduwa, ganin lawali driver be dauka ba yasa Sultan kiran layin Ammar bugu daya zuwa biyu be dauka ba, bangaran Ammar ko yana theater room hakan ne ya hana shi daukar kiran Sultan, hakan yasa dole Sultan ya jira aka gama gyara motar shi badan ya so ba.
Iya kar kuluwa Nihal ta kulu ganin Sultan be zo daukar ta ba har students sun watse, dama yace ta jirashi ne dan ya shanya ta agogo dake makale a hannun ta Nihal ta kalla kusan karfe 12:30am dan siririn tsaki Nihal ta saki yanke shawara Nihal tayi kara ta hau kekenapap ta koma gida, dagowar da Nihal zatayi taga wani kato a kanta juyawa Nihal tayi daniyar canza hanya wani katan ne ya tare ta kallan su Nihal ta shigayi na rashin fahimta tsoro na kara shigarta, duk da tsoran da Nihal ke ji hakan be hanata kokarin rabawa ta gefe ta wuce ba, TJee ne ya damko hannun ta a razane Nihal ta juyo tana kokarin banbare hannun Tjee cike da tsiwa Nihal tace, "malam lafiya zaka rike min hannu" Nihal ta ida zancan tana kiciniyar banbare hannun TJee bud'e mata gaban rigar shi yayi tare da nuna mata bindigar dake sakale a kugun shi zaro ido Nihal tayi kafin ta iya furta komai BS ya shaka mata fara hoda, take a nan Nihal ta sulale jikin TJee a sume daukar ta yayi ya daura a kafad'a shi ya tura a mota, sannan shima ya shige suka fisgi motar da karfi suka bar harabar makarantar.
Tunda Sultan ya nufo hanyar makarantar gaban shi ke tsanata faduwa har suka karaso harabar makarantar, ganin duk ba students yasa zuciyar Sultan kara tsinkewa har suka isa bakin hall din makarantar isar su tayi dai-dai da lokacin ana kokarin rufe hall din, bud'e murfin mota sultan yayi da sauri ya fito tare da yima security din dake kokarin kule kofar sallamah murmushi malam tukur yayi tare da cewa, "bakar da zuwa yallabai Allah yasa lafiya ai da ka karasa office din principal yana ciki" jikin Sultan ne yayi sanyi cikin honey voice din shi yace, "yariyar na zo dauka yau ta zo zana exam" sakatarere malam tukur yayi yana kallan sultan tare da gyara tsayuwa yana cewa, "Toh fa ai students din da suka zana jarabawa tun kusan karfe 12:00pm suka gama zana pepper, se kuma ta gobe idan Allah ya kai mu" shuru Sultan yayi yana nazari can kuma yace, "baka ga wata yarinya fara ba, yar siririya bata da tsaho sosai"
"Gaskiya ban ga kowa ba tunda na zo nan wuri se dai ka dan zagaya cikin makarantar may be tana wani waje tana zaman jiran ka" godiya ya Sultan yayi ma malam tukur tare da komawa cikin mota, juyowa Alex yayi yana kallan sultan yace, "Allah yasa lafiya" shuru Sultan yayi tare da ce ma Alex su zagaya cikin makarantar ko zasu ganta haka suka zagaye makaranta tas ba Nihal ba alamar ta, ko da Sultan yaje office din principal yayi mashi bayani shima ce mashi yayi bega Nihal ba, iyakar tashin hankali Sultan ya shiga da kyar ya iya karasawa cikin mota zuciyar na tsanata harbawa, da kyar ya iya cewa Alex su koma gida may be Nihal din ta koma gida ya ida zancan tare da maida kan shi setin window
*******
A cikin wani daji motar su TJee ta faka sannan yasa yaran shi ya dauki Nihal ya kai ta cikin wani gida sama da kasa da alama gidan ya dade ba'a shige shi ba, yana shiga ya aje Nihal saman kujera tare da daure mata hannuwan ta ya fice TJee ya shigo kujera ya ja ya zauna yana facing Nihal da har a lokacin sume take, ruwan dake kusa da shi na sanyi a bokiti ya janyo ya watsa wa Nihal a fuska wata irin ajiyar zuciya Nihal ta sauke a hankali ta sauke idanuwan ta saman fuskar TJee, TJee murdadan mutum ne dogo chocolate colour yana sanye cikin black jean da t-shirt White kafarshi na sanye da black boot, Hannun shi na rike da sigari yana busawa, kara maida ido Nihal tayi ta lumshe saboda har a lokacin idanuwan ta sun mata nauyi biji-biji take gani, dukan table din da TJee yayi ne yasa Nihal razana tana kallan TJee cikin sanyi murya Nihal tace, "inane nan, mi ya kawo ni nan, mina maku? Nihal ta ida zancan a raunane tare da cigaba da cewa, "please let me go! please" Nihal ta ida zancan tana kallan Tjee kamar za tayi kuka tana jijiga kujera da take bisa, matsowa kusa da ita TJee yayi yana murmushi rainin hankali yace "kina tunanin zan barki ki koma gida wajan Sultan ne ko? Toh kinyi kuskure ke da Sultan kunyi hannun riga kina jina! Tjee ya ida zancan yana matsawa Nihal fuska baya Nihal tayi cike da tsiwa hakoran ta a had'e tace, "ka daina tabani! dariya TJee ya saki tare da kallan Bs dake gefen shi yana cewa, "ka ji fa na daina taba ta" dariya suka saki lokaci daya suna kallan Nihal fisgo mata gashin kanta TJee yayi wata irin kara Nihal ta saki saboda azabar daya ziyar ci kanta tana mutsu-mutsu danna kanta Tjee yayi cikin bokitin ruwan sanyi me kankara mutsu-mutsu Nihal take tana neman ceto kanta saboda numfashin ta dake kokarin daukewa, fisgo mata gashi Tjee yayi Nihal ta biyo shi idanuwan Nihal sunyi jawur, tari Nihal ta shigayi saboda shakewa da tayi da ruwa tana maida numfashi hawayan wahala na bi mata kumatu, Tjee na kokarin dan nawa Nihal sigari a wuya, ringing din wayar shi ya katse mashi hanzari ganin number Nazili yasa shi dauka tare matsawa gefe yana cewa, "yanzu haka muna tare da ita duk yadda kike so haka za'ayi"
"Zan kira ka Tj idan na gama tsara abinda na ke, yanzu haka nasa an kona kayan ta sannan zan turo maka Aziza da jakar kudi" murmushi jin dadi TJee ya saki yana cewa, "Allah ya ja da kwana Gimbiya" Amin Nazili tace a takaice tare da datse wayar tana murmushin ji dadi, har Tj ya gama wayar ya kashe Nihal na kallan shi tana sauke ajiyar zuciyar wahala