← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 128

Sashe 17

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

*******
Nihal da yaya ke tafiya suna fira har sai da suka k'araso kwanar gida sannan ya Ciro kud'in ta cif har da k'ari ya bata, murmushi Nihal tayi tare da jerawa yaya godiya, sannan ta daga kafa a dai-dai bakin kofa taci karo da mudi wanda yasha ya bugu sai warin wiwi yake. fad'ad'a murmushin shi yayi tare da fisgo Nihal ta fada fafadan kirjin shi yana wani cije lips a razane Nihal ta dago suna kallan nuna ido cikin ido tana mutsu mutsu tana neman kwacewa a jikin shi, wani irin karfi ne ya zo mata ta bangaje shi ta shige gida da saurin tana zancan zuci, "ta rasa mike damun mudi da alama barasar da yake sha ta fara gaya mashi karya" muryar gwoggo ce ta katse mata tunani da cewa, "tunanin uban mikike ko sallama babu saboda yanzu kin k'una baki tara k'wari ko, to yayi kyau ki zo ki bani kudi na, kafin na matso nan na maki wulak'anci." gaban Nihal ne ya yanke ya fad'i da Sauri ta tura kula da yaya ya bata cikin bokitin koko ta aje a gefe, simi-simi Nihal ta k'araso ta mik'awa gwoggo kudin rank'washi gwoggo ta sakarwa Nihal a kai idanuwan Nihal ruwa suka kawo sosa kanta take Wanda take jin zafin rakwashin gwoggo har tsakar kanta, daka mata tsawa gwoggo tayi cikin kakakausar murya tace, "maza-maza ki bani guri ga wanke-wanke na can na jiran ki idan kin gama ga talla rana na jira shashashar banza," Nihal na hawaye ta qarasa wajan wanke-wankyen Wanda rana ta haska wajan tarwai babu alamar inuwa a hankali ta mik'e ta jawo ruwa a rijiya ta zuba a roba ta fara wanke kwanukan tanayi tana had'a zufa, sai da ta gama wanke-wankyen tas sannan tayi wuf ta d'auke kula dake cikin bokitin koko ta shige d'akin su da Sauri, umma na kwance saman ta barma kamar kullun sai faman zarni ke tashi saboda tasha ruwa da yawa shiyasa tayi fitsari sosai inda Allah ya taimaki Nihal batayi kashi ba, murmushi Nihal ta saki tare da jinginar da umma zaune, cikin fara'a Nihal tace cike da shagwaba, "Allah sarki umma na, nasan kin gaji da kwanciya ko ? Girgiza kai umma tayi alamar a'a k'ara fad'ad'a murmushi Nihal tayi tace, "umma kin ga abinda yaya ya bani yace muci Wanda nake baki labarin shi Dan birinin nan me hankali," cikin zakuwa Nihal ta kuma cewa kamar yasan muna fama da horan yunwa umma, gaskiya yaya na da kirki" ta idda zancan tana washe baki, murmushi umma ta saki me nuni da jin dad'in ta tace cikin sanyin murya, "Rabin raina ki dai kama kanki kinga maza ba abin yadda bane Nihal ina tausayawa rayuwar ki Nihal" Umma ta idda zancan hawaye na wanke mata fuska, daurewa Nihal tayi tare da hadiye hawayan dake mak'ale a idanuwan ta, a hankali tasa hannu tana gogewa umma hawayan ta cikin rawar murya Nihal tace, "umma bana so kina zubar da hawayan ki idan kina zubar da hawayan ki hakan na karyar min da zuciyar umma na, hakan na jefa ni cikin wani hali, nasan cewa Allah yana tare da mu umma na, insha Allah se mun fita daga cikin k'uncin nan da rashin gatan nan umma na" Nihal ta idda zancan tana had'iye wasu hawaye dake San sulalo mata, cikin rawar jiki Nihal ta fara bude kula da yaya ya bata saboda tsabar yunwar dake dawainiya da ita, lafiyayan soyayya doya ce tsoman akwai da pepper chicken a sama tun kafin su fara ci miyan su ya tsinke idan zasu iya tunawa raban da suci abinci me lafiyar haka tun Abba na da rai, a hankali Nihal ta shiga bama umma itama tanaci har suka cinye sannan Nihal ta ba umma ruwa itama tasha, tana sakin murmushi tace, "umma na bari nayi sauri na tafi talla rana kafin gwoggo ta biyo ni," "to Nihal Allah ya tsare min ke", "amin umma na"

Bud'e labilan Nihal ke da wuya aka wanke ta da lafiyayyan mari har guda uku gabaki d'aya wutar jikin Nihal d'aukewa tayi tana ganin wasu taurari bin gwoggo da idanuwa Nihal tayi wasu hawaye na wanke mata fuska, se huci gwoggo take kamar kumurci wata uwar tsawa ta dakawa Nihal tace, "dan uwar ki ban hanaki Shiga da kin wannan tsinaniyar uwar taki ba idan na saki aiki ba,? in ban da wulak'anci sai kin gama taba k'azamar uwar taki sannan se ki zo ki taba min kayan sana'a," fisgota gwoggo tayi tare da wurgi da Nihal kanta ya daki bangwan tsakar gida, sulalewa Nihal tayi tare da sakin wani irin kuka me cin rai, gwoggo bata saurara mata ba, haka ta rufe Nihal da duka kamar zata kashe ta umma dake d'aki sai kuka take tana jiyo irin wulak'anci da Nihal ke fuskanta, sai da gwoggo ta mata lilis Wanda ko motsi da kyar take sannan ta sake ta, tana sauke ajiyar zuciya, cikin masifa gwoggo tace, "maza-maza ki d'auki farantin nan kafin na taka maki ruwan ciki na k'arasa ki, ita kuma uwar taki zata gane kuranta tunda saboda ita kike yin yadda kikaga dama da ba ita ai da Baki rink'a tsalake min dokokin dana shinfid'a maki ba," wani irin kuka Nihal take har murya ta bata fita jan jiki Nihal tayi tare da d'aukar faranti talla baki ta sai zubar jini yake, a haka ta fita tana dingishi jiri na dibarta.
Chapter 17 · 0% Book details