← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 128

Sashe 81

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Nazili dake tsaye gaban dressing mirror tana gwada kayan ta murda kofar da akayi ne ya sata juyowa Aziza ce ta shigo dauke da tray din abinci ta aje a center table tana cewa, "sannu da hutawa Gimbiya"
Juyowa Nazili tayi tana cewa, "yauwa zo ki zuge min zip din kayan nan ki shirya min komai nawa saboda anjima nima zani dinner" cike da gulma Aziza tace, "oh shiyasa dazu naga aunty Nihal na gwada wani dinki mai kyau kala naki Ashe itama dinner zata" juyowa Nazili tayi a fusace tana kallan Aziza cikin zafin rai tace, "se na haram ta mata zuwa dinner saboda bana anko da matsiyata a kan wani dalilin zan sa kaya iri daya da tallaka" tab'e baki Aziza tayi tana cewa, "dinkin ta ma naga ya so yafi naki Allah ya huci zuciyar ki" juyowa Nazili tayi tare da bigewa Aziza baki cikin masifa ta kankace ido tana cewa, "Allah ya sauwake ace wannan almajira kayan ta sunfi nawa, ya kamata ki iya bakin ki yar matsiya ta shashasha kawai" Aziza dafe da baki ta rakube a bango tana bin Nazili da kallo amma kamar masifa kullun tana like da Nazili, zagaye daki Nazili ta shigayi rake da kugu tana cewa, "ban san yaushe zan cin ma buri na a kan wannan shashar ba" murmushi Nazili ta saki tare da furta "se na haram ta maki sa kayan nan, Aziza ina so ki san duk yadda za kiyi ki dauko min kayan nan ki kawo min su a hannu na" Nazili ta ida zancan tana waigowa murmushi Aziza ta saki tare da cewa, "angama ranki ya dade" sannan ta fice

Su Nihal na gama gwada kaya suka wuce part din mom dan dauko sauran kayan da za'a rabawa yan'mata amarya a dinner.

Hakan ya ba Aziza damar shiga dakin Nihal linke ta ga kayan Nihal saman bed dauka tayi da sauri ta wuce da su dakin Nazili, lokaci Nazili na zaune zaman jiran ta amsar rigar Nazili tayi tana murmushi tace, "kin kyauta Aziza kin min dai-dai" lighter Nazili da dauko a bedside drewar tare da kunawa kasan rigar wuta, kama ci da huta rigar tayi se da tayi rabi Nazili tayi wurgi da rigar kasa tare da cewa, "bani ruwa Aziza" ruwa Aziza ta mika mata a glass cup ta zubawa rigar sannan tace, "ki maida ki aje inda kika dauke ta, ina so na sata bakin ciki a wannan daran se taje dauka taga ta kone" Nazili ta ida zancan tana dariya, daukar rigar Aziza tayi tare da cewa, 'idan ta gane ke ce fa Gimbiya"
"Ko ta gane babu abinda zata iya kije ki kai mata ki aje kamar yadda nace maki"

A gajiye likis Nihal ta dawo part din Ammi bedroom din ta kawai ta wuce ko lura da abinda akayi ma kayan ta ba tayi ba ta dauka ta wuce part din sultan, saman sofa ta aje kayan ta shiga toilet wanka Nihal ta sheke ta fito sanye da towel lotion kawai Nihal ta shafa kasancewar yamma tayi me make up na part din mom tana jiran ta rigar kawai Nihal ta janyo ta saka abinda ta ganine yasa Nihal shock tsare rigar tayi ta ido tare da damke ta a hannun ta tasan ba me aikata mata haka se Nazili saboda ita kad'ai ce ta tsane ta a gidan hawayan takaici ne suka fara zubowa Nihal share hawayan tayi tare da daukar rigar ta fita da sauri.

Nihal bata zame ko ina ba se dakin Nazili tana shiga ta banka kofar da karfi Nazili dake zaune ce ta mike hannu ta nad'e a kirji tana bin Nihal da kallan wulakanci batayi auni ba Nihal ta dauke ta da mari har so biyu ji kake tas, tas........

```Taku har kullun salma mas'ud nadabo```
[1/11, 10:19 AM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
*Story*
*And*
*Writing*✍🏾
*By*
*Salma mas'ud nadabo*👑

🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
(```We are the best among the rest```)

*Page: 101_102*

*_wannan page din naki ne ke kad'ai aunty Khadija Hamu kiyi yadda kike so da shi,🤗 godiya ta musanman gare ku masoya SAUYIN RAYUWA yawan comments yawan posting_*🤪

azabure Nazili ta mike tana maida numfashin dafe da kunci sakwamakwan baccin daya dauke ta tayi mumuna mafarki Nihal ta tsinka mata mari maida gashin kanta tayi baya tana cewa, "god for bit..! da sauri ta duro daga saman gado kofar dakin ta ta murd'a tare da leka main parlour iska me zafi Nazili ta furzar dawowa tayi cikin dakin tare da daukar jug ta tsiyaya ruwa cikin glass cup ta shanye tas tana kallan mirror tana duba kuncin ta cikin zafi rai tace, "amma dai anyi mayar mata har ciki bacci bata saurara min ba, kafi ta ci mun fuska ni zan fara aikata mata hakan..! Nazili ta ida zancan tana zagaye dakin ta jin an murda kofa ne ya sata juyowa a razane tana kallan kofar, Ammi ce ta shigo tsare ta da ido Nazili duk tayi zuru-zuru kamar mara gaskiya Ammi ce ta matso gaban ta tana cewa, "what wrong with you naga kinyi suku-suku dake" juya baya Nazili tayi tana cewa, "nothing Ammi daga bacci na tashi shiyasa" Nazili ta ida zancan tana zama saman gado matsowa Ammi tayi bakin gadan ta zauna tana cewa, "har yau ba ki daina halin kwanciya da yamma ba ko bayan kin san hakan ba kyau, yan'mata se shirwa suke ban ganki a cikin su ba" tab'e baki Nazili tayi tare da cewa, "yanzu zan shirya Ammi" ta ida zancan zata mike ruko hannun Nazili Ammi tayi tare da cewa, "Nazili ina san magana dake..! maida hankali Nazili tayi kan Ammi, Ammi ta cigaba da cewa, "Nazili ya kamata ace kema by now kin fido miji kinyi aure na lura dake har yanzu kamar aure baya gaban ki, ki duba ki gani duk sa'anin ki suna gidan mijin su wayanda basu yi ba suna da tsayaye amma ke ba ko daya" zame hannun Ammi Nazili tayi tana cewa, "oh my goodness Ammi how many time zan fada maki ban shirya yin aure ba impact ma har yanzu ban ga namijin daya dace dani ba..! Nazili ta ida zancan zata shige toilet maganar da Ammi tayi ne yasa Nazili tsayawa cak "Nazili ya kamata kiyi ma kanki fada idan ma sultan kike zaman jira ya zo ya aure ki ya kamata ki farka daga wannan mafarkin, da be ce yana san ki ba se yanzu da yayi aure ze dawo maki Nazili, kuskure anriga da anyi shi Nazili ya kamata ki gane hakan" juyowa Nazili tayi rai bace tana kallan Ammi hannu ta nad'e a kirji tace, "yanzu na gane me ya kawo ki Ammi kin shigo daki nane saboda ki bata min rai, idan har kin san haka ne kofa a bude take kina iya fita, dan kowa nayin aure what ever bashi ze sa ki tirtse ni dole se nayi aure ba, koma me ya faru ai laifin ki ne me yasa baki hana sultan yin auran ba, bayan kin san da cewa ina san sultan tun tasowata amma kika rufe ido kika ba almajira, kika cusawa sultan san Nihal, mi yasa baki cusawa sultan so na ba,? baki da wannan amsar amma ni ina da ita saboda ba kya sona cikin jikokin ki, tunda kika aikata haka aikin riga kin rabani da sultan saboda i can't stay under the same roof with almajira Ammi" murmushi Nazili ta saki tare da matsowa kusa da Ammi suna kallan juna tace, "let me tell you something Ammi ni yanzu sultan baya gaba na saboda yana san matar shi Ammi a kan wani dalilin zan zauna zaman jiran shi, ke ma Ammi kinyi gaskiya da kika ce sultan be ce yana so na da ba se yanzu..! Nazili ta ida zancan hawaye na sulalo mata a kunci rungume ta Ammi tayi tana cewa, "Am sorry for that Allah ya maki albarka da kika gane hakan, amma dan Allah ki daina cewa bana san ki Nazili ina sanki Nazili ina jin ki har cikin zuciya ta" Ammi ta ida zancan tana shafa kumatu Nazili idanuwan ta cike da kwalla, rungume Ammi Nazili tayi kamar tayi sanyi ta saduda, murmushi Nazili tayi cikin zuciyar ta tana cewa, Ammi kenan kina tunanin zan zuba ido ne ina kallan su, nayi hakan ne kawai dan na fita daga zargi ko da na aikata wani abun baza a ganeni ba..! Nazili ta ida zancan zuci tare da numfasawa zame jikin ta Ammi tayi tana murmushi itama Nazili murmushi ta saki tare da cewa, "Ammi bari na shige toilet nayi wanka, ki daina tunanin san sultan ne ya hanani fida mijin kawai ban samu wanda muka daidaita bane" Nazili ta ida zancan tana shafa kumatun Ammi kissing hannu ta Ammi tayi sannan ta fice d'an siririn tsaki Nazili ta saki tare da shigewa toilet.
Chapter 81 · 0% Book details