← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 105 OF 128

Sashe 105

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dakin da aka kwantar da Alex herry ya gwadawa sultan da murmushi sultan ya murd'a handle din kofar hannu shi daya na makale dana Nihal, Alex dake zaune saman gado jingine hannu shi daya na daure, daya hannu shi na rike da Qur'ani yana kara bita karatun da aka koya mashi, murmushi ya saki yace, "sultan..! tare da aje Qur'ani sama bedside drewar da sauri sultan ya karasa wajan shi ya kai mashi hug yana cewa, "I miss you dude ya jiki? jiya na samun labari ka fito daga como"
"kwana na biyu da fitowa jin kana tare da Gimbiya ne, na hana a fadama ka, amma na kira Ammar na fada mashi yauma ya bar kasar nan muna tare da shi" murmushi sultan ya saki Nihal dake gefe tace, "ya jiki..!
"da sauki ran ki ya dade..! zama Nihal tayi saman kujera sultan na saman gado yana cewa, "wannan jinyar haske ta karama Alex har wata kiba kayi" Sultan ya fada cikin sigar zolaya dariya Alex yayi yana cewa, "ba dole nake yin haske ba tunda na bar duhu na dawo haske, Allah na gode maka daka ganar dani, ban fada maka ba, na zancan suna yanzu na tashi daga Alex na koma Ahmad"
"oh my godness am happy to her that Alex oh Ahmad..! Lalai Allah abin godiya ne Allah yasa mu cika da imani"
"Amin..! murmushi Sultan ya saki yana nuna jin dadin shi yace, "Amma na ji dadi sosai da SAUYIN RAYUWA daka samu Ahmad, har wani gemun sunna ka aje kana ta karatu, na lura sai ma ka fimu zama malami" dariya Ahmad ya saki yana cewa, "No.! No..! ina ni ina kama kafar ku, am just trying naga na iya karatun da Ammar ya koya min" murmushi sultan ya saki nurse ce ta shigo rike da tray din abinci Sultan ya mike ya amsa yana cewa, "yau ni zanyi feeding dude tunda na zo" murmushi Ahmad ya saki da kan shi sultan ya taimakawa Ahmad ya ci abinci Nihal na gefe tana kallan su shi dai sultan yana da hali mai kyau sai ka zauna da shi zaka gane hakan ko yarda yakeyi da friends na shi ze nuna maka mutumin kirki ne, bayan ya gama bashi abincin ya aje tray din yace, "Ahmad bari mu je masaukin mu ko can bamu je ba daga airport direct nan muka zo"
"Eyya sultan ka bar Gimbiya da yunwa ko abinci baku tsaya kun ci ba kun huta,"
"bana iyawa kullun da tunanin ka nake kwana shiyasa ina jin labari na taho"
"Na gode da kulawar da kake nuna" harara sultan ya bala mashi yace, "bana san haka kuma ka sani, after all wannan abun daya faru saboda dani ya faru"
"OK, ok naji bazan kara ba ni da kai ai duk daya ne, kai ma bana so kana fadin, saboda kai something like that..! na matsu na warke na dawo Nigeria jina nake duk a takure"
"Sai ka warware sosai zaka koma" sultan ya fada yana cewa, "hayaty muje ko" mikewa Nihal tayi Ahmad ya bisu da ido ba wace ta fado mashi a rai sai Nazili sanda ya dauke ta garden iska mai zafi ya furzar ya lumshe ido zuciyar shi na wasu tunane-tunane.

Gidan Mr president suka sauka part na musanman aka basu cikin gidan 2 bedroom da parlour sannan Mr president yace idan sun gama abinda suke so fito ayi dinner da su, to kawai sultan yace matar Mr president sai yaba kyan Nihal take har tana cewa sultan be kyau taba da bai fada masu yayi aure ba ashe ma ya dade da yin aure hakuri kawai sultan ya basu sannan suka wuce masaukin su.

Nihal ce tsaye gaban dressing mirror tana kokarin cire dan kunna dake kunna ta rungume ta sultan yayi tabaya yace, "hayaty..! cikin honey voice din shi yana kallan ta ta cikin mirror murmushi Nihal ta saki tana cewa, "kallan fa? na canza maka ne love,? kumatun Nihal sultan ya ja yana cewa, "bana gajiya da kallan ki hayaty, kullun burin na be wuce na jini makale dake ba kina shayar dani soyayyar ki da kaunar ki" murmushi Nihal ta saki ta juyo suna facing juna hannu tasa tana cire mashi necktie tana cewa, "shiyasa nafi kowa ce mace sa'ar miji, Allah ya barmu tare love"
"Amin..! sultan yace tare da sakar mata light kiss a goshi

Knocking din kofar da akayi ne yasa sultan zamewa daga jikin Nihal ya karasa bakin kofa Nani ce rike da wasu kaya a hannu ta, amsa sultan yayi ya shigo da su lokacin har Nihal ta shige toilet kara ruwa ne ya tabatarwa sultan wanka take murmushi ya saki tare da ficewa.

Koda Nihal ta fito daga toilet bata sami sultan a dakin ba murmushi ta saki ganin kayan dake saman bed wata dark blue gwon daga rigar Nihal tayi tana jona ta a jikin ta a fili tace, "love baya gajiya da yimin hidima, dubi rigar nan me kyau..! shiryawa tayi cikin dark blue rigar tayi mata masifar kyau rigar ta fito da shape din ta sosai daga kasa an tsaga rigar, zaunawa Nihal tayi ta tsantsara make up bakin ta yasha maroon jan baki sai shining yake gashin ta tatare ta maida shi gafe ta saka sarkar ta mai tsadar gaske wanda akayi da zala diamond, ita kan ta Nihal data kalli kanta a mirror ta sheda kyan data zuba, murda kofar da akayi ne yasa Nihal juyowa karfa suka hada ido da sultan, yana shirye cikin Ash suit din shi ta kama jikin shi yayi kyau har ya gaji sajan shi ya kwanta luf-luf cike da kallan so sultan ke bin Nihal da kallo dan ba karamin kyau ta zuba mashi ba, a hankali ya tako yana kara bin ta da fitinan kallan shi mai kashe mata jiki murmushi kawai Nihal ke saki tayi kasa da kanta, cikin murya shi me dadin saurare sultan yace, "wow hayaty kinyi kyau sosai"
"Na gode love kai ma kayi kyau sosai" murmushi sultan ya saki tare ciro wayar shi yana daukar su hoto ringing din wayar shine ya katse mashi tunani ganin suna Mr president, "oh har an fara kira na muje hayaty" kallan Nihal sultan yayi lokaci daya kishi ya rufe shi yama za'ayi Nihal ta fita haka suyi dinner haka kawai turawa su gane mashi mata idan ko haka zata fita kara a fasa dinner, trolley ya bude Nihal dai bin shi da kallo kawai take blue veil ya ciro ya tako gaban ta Nihal dai na bin shi dana mujiya hannu yasa ya nanad'e mata gashin ta yayi ganmo da shi ya yafa mata veil din a kai yayi sannan ya dan ja baya yana kallan ta murmushi ya saki a fili yace, "hakan ya fi" murmushi Nihal ta mashi sannan suka fice a tare.

Fadin tsaruwar wajan bata lokaci ne haduwar wajan takai haduwa wani kayatacan dinner Mr president ya hadawa sultan, wanda shi kan shi be san da ita ba acewar shi wannan ce kad'ai gudumuwar da ze bawa sultan tunda yayi aure, manya-manya masu kudi na kasar sun halara da likitoci sultan da Nihal suna nufo wajan dinner wani tartsatsi me kyalkyali ne ya shiga watsowa har abin ya so ya firgita Nihal jawota jikin shi sultan yayi yana saki murmushi yanayin yarda suka shigo wajan sai ya bada salo na daban, mikewa muta nan wajan sukayi suna tafi wajan ya dauka flowers na zubowa su Nihal ta ko ina Nihal kuwa lallacewa tayi tana kallan tsaruwar wajan ko ba'a fada mata ba ta san kudi yayi kuka, kowa da zaka gani a wajan yana makale da matar shi har suka karaso wajan da aka tanadar masu na musanman Sultan sai murmushi yake yana kara makale Nihal a jiki shi Nihal ma haka murmushi take daga sama wani hadadan cake yake saukowa yana ta kyalkyal mamakin duniya kuwa ya ishi Nihal tana kallan ikwan Allah har cake din ya tsaya saitin su wuka Mr president ya mikawa sultan, murmushi sultan yayi ya amsa, kama hannu Nihal yayi suka yanka cake din a hankali ya gutsuro ya bata a baki, itama ta bashi tafi wajan ya dauka raf, raf camera sai haska su take duk inda suka juya camera na biye da su, sai da Mr president yayi jawabi sannan sultan shima yayi tare da nuna godiya shi a kan dinner da Mr president ya hada masu, abokan arzikin da suka halari dinner mikawa Sultan hannu suke da Nihal suna cewa congratulation suna mika masu gift, sannan aka fara cin abincin kid'a mai taushi yana tashi har a lokacin Nihal bata daina amsar kyauta ba tana mikawa security's dake take masu baya suna ajewa, bayan kowa ya gama bada gift din shi, mawaki na musanman ne ya shiga raira waka mai sanyi ta masoya, kowa mikawa matarshi hannu yayi suka shige fili Nihal sai murmushi take tana kallan rawar turawa a kunne sultan ya rada mata, "hayaty ko kema zakiyi rawar..! murmusawa Nihal tayi tace, "love ban iya ba"
"zan koya maki..! Girgiza mashi kai Nihal tayi duk yadda Nihal tayi da sultan ya kyale ta amma yaki dole ta mika mashi hannu ta ya kama suka shiga fili suka fara a hankali sultan ya daura hannu shi saman waist din ta ya daura nata saman kafadar shi ya kama daya hannu ta a hankali suka shiga rawar duk abinda sultan yayi Nihal nayi wani irin juya ta sultan yayi cikin salo Nihal ta dawo saman kirjin shi gabaki daya kallo ya koma kan su, kunya kuwa ta rufe Nihal tafi kawai ake masu saboda birge muta ne da salan su ayin ciye-ciye da lashe-lashe taro ya watse cike da murna sannan sultan da Nihal suka wuce masaukin su a gajiye likis koda suka koma sauya kaya sukayi suka bi lafiya gado.
Chapter 105 · 0% Book details