← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 128

Sashe 26

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da kyar jabir ya k'araso wajan Ashad yana dafe da ciki yana maida numfashi a hankali zame abinda ya rufe fuskar shi da shi yayi, kan shi Sunkuye yace, "Ran ka yadad'e" juyowa Ashad yayi tare da zame hula Alkyabba dake kanshi yana shu'umin murmushi, ganin halin jabir yake ciki yasa Ashad had'e rai tare da cin kwalar jabir cikin huci yana cewa, "karka ce min ba abinda ya sami Sultan, yanzu na aika ka lahira tunda kai ka kasa" dariya jabir ya saki duk da zafin da yake ji ya zame hannu Ashad daga Wuyan shi yace, "ban tab'a zuwa aiki na dawo ba nasara ba kuma bazan fara a kan Sultan ba" yana maganar yana cije hak'ora ya cigaba da cewa, "se dai wannan jarumi ne munyi kare jini biri jini nasan yanzu in dai ba'a kawo mashi d'auki gagawa ba nasan ya mutu, so d'aya ya caka min wuk'ar ji halin da na Shiga bale shi har sau biyu kuma da karfi na, na caka mashi" dariya Ashad ya bushe da ita yana shafa gemun shi kamar na bunsuru yace, "aiki ka yayi kyau jabir'' jakar kudi Ashad ya mik'awa jabir yana cewa, komai da komai na cikin jakar gobe da Asuba flight din ka ze tashi sannan ka tabata ba Wanda ya San wannan magana zan turo ma da likitan sirri ya duba ka ga car key dina akwai driver a waje yana ganin ka ze gane," sannan ya bibigi kafad'ar shi yana cewa, "Good job my man" ya maida hula Alkyabba shi ya bar wurin da sauri.

*Washe gari*

Yau sadakar uku da rasuwar umma sai dai mu ce Allah ya ji k'anta yan'uwan umma ne zaune a parlour baffa su duka har dama baffa Aunty Aisha ce tayi magana kasancewar daga umma se ita se k'anna su maza biyu Aunty Aishi a birni kano take aure kuma mijin ta d'an kasuwa ne yana da rufin asirri cikin sanyin murya aunty Aisha tace, "mi zai hana tunda umma ta rasu abani Nihal mu tafi birni tare zan bata kyakyawar kulawa kamar yadda zan ba ya'ya na" gwoggo ce ta rushe da kuka tayi tsale ta dire ta ce ba inda Nihal zata, tabar dangin uban ta koma na uwar ta to mi akayi kenan, baffa ne ya share kwalla munafirci yace, "Haba Aishatu kika dauke min Nihal ai baki kyauta min ba ita zan rink'a gani ina jin sanyin ina tunawa da d'an uwana, Aisha karfa ki manta mu ka d'ai ne ke Raye se diyar Dan uwan nawa idan kin ga Nihal ta bar hannu na to se dai aure na mata" baffa ya ida maganar yana rushewa da kukan k'arya, Nihal dake gefen aunty Aisha wasu hawaye na wanke mata fuskar tabas yau ta tabatar da tsanar da su gwoggo suke masu itama so suke bak'in cikin su ya kashe ta kamar yadda ya kashe umma kuka Nihal ta saki sosai tare da fita daga pralour da gudu, gwoggo tab'e Baki tayi tana zancan zuci, da Nihal ta je birni ta waye tayi wayau k'ara ta nak'asa ta, ko tun wuri su samo wani kwakin su bata, Aunty Aisha ce ta katse mata tunani da cewa, " toh shikenan baffa naji maganar ka kuma na tausaya maka Allah ya ji k'an magabata, sannan insha Allah zan rink'a waiwayar Nihal dani da su khabir sannan in baza Ku damu ba Nihal zata rink'a zuwa mana Hutu birni" kad'a kai baffa yayi yace, "indai wannan ne baku da wata matsala kuma ai Nihal d'in yar ku ce, Dan dai ban iya jurewa rashin ta kusa da nine" ya ida zancan yana matsar kwalla kad'a kai aunty Aisha tayi tare da curo dubu ashirin a jaka ta, ta mik'awa baffa se faman antayo mata godiya yake sannan suka fito direct dakin da Nihal ta shiga aunty Aisha ta bita jiki ba kwari, a hankali ta dafa Nihal d'ago rinanin idanuwan ta Nihal tayi tana kallan aunty Aisha, murmushi Aunty Aisha ta saki Wanda iya karshi lab'an ta ta janyo Nihal jikin ta, ta daura kanta saman cinyar ta tana cewa cikin sanyin murya, "ban san Nihal d'ita da rashin tawakali ba, kuma basan Nihal d'ita da karya ba, bana so ki boye min duk abinda ke damunki Nihal ko bakya jin dadin zama da su baffa ne? idan har haka ne ni kuma na maki alk'awarin daukar ki mu tafi ko da hakan ze janyo cece kuce," murmushi Nihal ta k'ak'oro tana kallan aunty Aisha tace, "babu abinda su baffa ke min kawai dai ina kewar umma nane, kuma naso na biki ko Dan naga su ikilima," kallan ta Aunty Aisha take tana San karantar wani Abu amma Nihal tak'i bata fuskar hakan tashi tayi tare da janyo trolley d'in ta, sannan ta curo takada ta rubuta number wayar ta tace, "Nihal ga wannan number ta ce duk abinda ke damunki ki kirani ki fad'a min kinji d'iya ta," d'aga kai Nihal tayi sannan ta amshi trolley din a hannu Aunty Aisha suka fito su gwoggo na tsakar gida, washe da baki gwoggo tace, "Allah ya kiyaye hanya"
"Ameen" har bakin kofa gida Nihal ta rako ta su baba khabir na tsaye bakin kofar mota, murmushi baba khabir ya saki yana cewa, "k'araso mana yar leleta" murmushi Nihal ta saki idanuwan ta taf da hawaye ta shige jikin baba khabir, shafa kan ta yayi yace, "insha Allah da anyi hutun makaranta zanzo daukar ki muje Hutu ko," Nihal dake ji kin baba khabir mamaki ne ya kamata saboda irin k'aryar da baffa ya sharto mashi zame jikin ta, tayi tana murmushi tace, "toh baba"
"Yauwa yar albarka" baba sani yace, "Ni wallahi Nihal d'in duk sai naga ta wani yamutse ta k'oke" ya fad'a yana kallan aunty Aisha tabe baki tayi tace, "Hmmm" tare da mik'awa baba sani trolley Aunty Aisha ta mik'awa Nihal 1k cikin hannu ta tace, "gashi kin sha sweet" bude baki Nihal tayi zata mata godiya, daura yatsanta Aunty Aisha tayi tare da girgiza mata kai murfin mota suka bude suka shige, Nihal nata d'aga masu hannu har suka k'ule sannan Nihal ta soke dubunta a zani.

Bayan Ashad ya tsala wanka ya wuce dining area yayi break yau zuciyar shi fes kamar anzuba mashi k'ankara goge bakin shi yayi da tissue ya wuce part din Sultan hannu shi dauke da kwalbar guba wadda idan yasa ma Sultan a ciwo, ciwo zai cigaba da girma har ya mutu, yana isa bakin kofar parlour Sultan ya watsawa fadawa harara jiki na rawa suka bude mashi kofar ya shige ba abinda parlour keyi se kamshi turare da k'ara AC dake tashi murmushi ya saki na farin ciki ya nufi dakin Sultan, yana bude kofar ya hango Alex zaune saman sofa ida shigowa Ashad yayi tare da watsawa Alex wani irin kallo hannuwan shi na zube a Aljihu yace, "zanyi magana da yayana privacy ya kamata ka bamu guri" tabe baki Alex yayi yace, "bacci yake" harara Ashad ya maka mashi yace, "a hakan nake so ka bani guri, saboda bana zama waje d'aya da matsiya ta" se da Alex ya zo zai wuce Ashad se kuma ya dawo yace, "be carefully kar wani Abu ya biyo baya bayan ka fita," ya ida maganar yana kallan Ashad tsoki Ashad ja tare da nufar bakin bed din Sultan, ya zauna yana kai aika mashi da harara yana shafa gemun shi, Sultan dake kwance idanuwan shi lumshe eye's lashes din shi sunyi Zara-zara a hankali ya bude kwalbar ya dibi maganin ya nufi saman ciwo Sultan da maganin, rike a hannuwa shi akayi kam gaban Ashad ne ya yanke ya fad'i, ware idanuwa shi Sultan yayi suna kallo-kallo da Ashad murmushi Ashad ya k'ak'aro yace, "bros ya jiki" smile Sultan yayi yace, "da sauki"
"Masha Allah" mik'ewa Ashad yayi tare da daukar cup yana had'a coffee, Sultan na binshi da idanuwa Ashad yace, "yaya kwata-kwata banji dad'i wannan Alamari ba" yana fad'a yana jeba sugar me k'waya a tea, Sultan yace, I think shima Wanda yamin haka shima yana can yana jinya, sannu baya hana zuwa se dai a dad'a ba aje ba wata rana da hannu zan kama Wanda ke aiko min su," tabe baki Ashad yayi yace, "aiko dai da se nafi kowa murna da wannan rana," d'an murmushi gefen fuskar Ashad yayi yace, "Na ji kamar waziri na cema maimartaba Azir ya mutu jiya saboda ya ci guba" a zabure Sultan ya mik'e ya ce wani Azir d'in? kake nufi karka ce min doki na" tab'e baki Ashad yayi yace, "waka sani Azir bayan dokin ka" dafe ciki shi Sultan yayi tare da sa sleeping robe din shi ya fice da sauri, dariya Ashad ya saki yana cewa, "huhuhu yanzu muka fara," sannan ya aje cup din coffee a table tare da bin bayan Sultan, sultan yana fitowa parlour Alex dake zaune saman three star ya mike tare da rik'e hannun Sultan yace, "Sultan what wrong" zame hannu Alex Sultan yayi ya fice yana d'ingishi, kallo Alex ya bi Ashad da shi yace, "mika fad'a mashi? Alex ya fad'a cikin d'aga murya tsawa Ashad ya daka mashi yace, heeee!!! ya nuna shi da yatsa yace, " ya kamata Kasan matsayin ka malam, fad'a mashi halin da dokin shi yake ciki nayi saboda ban ga anfanin b'oye mashi ba nonsense mtwss" sannan ya bala ma Alex harara janyo shi Alex yayi ya mak'ure shi a bango fisge hannu Alex yayi ya fita yana gyara kwalla rigar shi,
Chapter 26 · 0% Book details