← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 128

Sashe 61

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Nazili ce tsaye gaban dressing mirror tana shiryawa cikin jeans and shirt, black jeans rigar white tasha kyau har ta gaji bakin nan yasha jan bakin tayi parking gashin kanta ya wani nanad'e daga kasa, fost din ta dake saman dressing mirror ta dauka tare da saka takalman ta black boot a hankali tasa Hannu ta bud'e handle din kofar dakin ta, tana tafiya komai na jikin ta na amsawa har ta karaso dining area lokaci sun Ammi har sun fara breakfast, kallan su take da alamar tanbaya sannan ta kalli inda sultan ke zama yana break jan kujera tayi ta zauna tana cewa, "morning grandma" Nazili ta fada tare da sakar wa Ammi pack a cheeks nata
"Morning too Nazili" Basmal dake kusa da Ammi tace, "kin tashi lafiya?
"lafiya lau" Nazili tace tana serving kanta plantain, kallan Ammi tayi tare da cewa, "Ammi ina Sultan? yau beyi break a gida bane? Basmal ce ta amshe zancan da cewa, "Ai yanzu yayana ya daina break da mu tare da wife nashi ya keyi yanzu nasan ya tsufa a office," daga gira Nazili tayi tana kallan Basmal takaici na rufe ta, Basmal ta cigaba da cewa, "Nihal naji da yayana sosai tana bashi kulawa shiyasa kullun soyayya su kara birge ni take Ammi" Basmal ta ida zancan cike da jin dadi, Murmushi Ammi tayi tare da cewa, "shiyasa nake san Nihal akwai natsuwa da biyayya! Wani irin kallan banza Nazili ke bin su Ammi da shi bakin cikin na shigar ta dan siririn tsaki ta saki ta turo plate din gaban ta, Ammi tace, "Nazili ba dai har kin koshi da abincin ba?
"Eh na koshi" Nazili ta ida zancan a gadarance tare da barin dining da sauri cikin zuciyar ta tana cewa, wawaye se naga bayan wannan matsiyaciyar yarinyar nan natsane ki,Nazili ta fad'a da karfi, har Nazili ta isa parking space tana surutai da masifa, tana kokarin bud'e murfin motar ta suka had'e da Ammar, murmushi Ammar ya saki yana cewa, "Nazili ke dawo kuma tun daga nesa na hango ki, kina masifa Allah yasa lafiya" Ammar ya ida zancan yana rike kugu, kallan banza Nazili tayi ma Ammar tana cewa, "dan sa ido kawai mtsww, kaji da rayuwar ka malam mtsww! Ta ida zancan tare da shigewa cikin motar ta da karfi ta fisgi motar kamar zata tashi sama ta fice, girgiza kai Ammar yayi tare da cewa, "ko yaushe Nazili zatayi hankali oho! sannan ya karasa cikin gida a bakin kofar part din Ammi suka had'e da Basmal tana kokarin fita Hannun ta rike da books kasancewar tana da lectures din safe, murmushi Basmal ta saki tana kallan Ammar shima kallan ta yake mai cike da so da kauna, cikin siririyar murya ta tace, "ya Ammar ina kwana," Amsa mata yayi cikin calm tune tare da matsowa kusa da ita kamar me rada yace, "my love kinyi kyau sosai har kin sa na fara kishi, duk wannan kwalliyar school akayi mawa ita" kallan kanta Basmal tayi ba komai bane jikin ta se black after dress se black veil da lipstick da ta shafa ma lips din ta, amma duk da haka tayi kyau, murmushi Basmal ta saki har fararan hakuran ta na bayana tace, "sweetheart ina kwalliya a nan? ni ba kwalliya da nayi Allah" Basmal ta ida zancan cike da shagwaba, ja mata hanci Ammar yayi sannan yace, "toh shikenan amma fa kinyi kyau muje nayi dropping naki tunda naga kamar school zaki" to Basmal tace tare da bin bayan Ammar shi da kanshi ya bud'e mata kofar mota sannan ya koma ma zaunin drive a hankali ya fara jan motar se da sukayi nisa sannan Ammar ya daura hannuwanshi saman na Basmal yana cewa, "my love kin mantar dani ko gaishe da Ammi banyi ba saboda kin rud'a ni da yawa" dariya Basmal tayi mai sauti tana kallan Ammar dake kallan ta a hankali Ammar ya sakar mata light kiss a kumatu shuru Basmal tayi tana tsare Ammar da ido suna kallan juna, horn din da suka fara jine yasasu juyawa lokaci guda a dan razane birki Ammar yaci yana dariya yana cewa, "baby kin gani zaki ja mana hadari a kan titi! nidai gaskiya my love na matsu mu kasance tare da juna, ji nake kamar na jawo satin bikin mu nan kusa" harara wasa Basmal ta sakarwa Ammar tana cewa, "ba ruwana laifin kane na lurama so kake mu mutu kafin bikin" mintsinin ta Ammar yayi a hannu yana harara ta yar kara Basmal ta saki rufe bakin ta yayi dai-dai da parking din motar Ammar a harabar makarantar su Basmal murmushi Basmal tayi tana cewa, "Alhamdulillah mun iso lafiya" ta ida zancan cike da zolaya tace, "thank you sweetheart" dariya Ammar yake yana cewa, "matsoraciya kawai" Ammar ya ida zancan yana kama hannun Basmal fisge hannuwan ta tayi tana cewa, "cizo na zakayi tunda ka mintsineni" dariya Ammar ya saki yana ja mata kumatu yana cewa "no baby ko daya kawai dai" a hankali ya sakar mata light kiss a kumatu yana cewa, "ki kullamin da kanki kin ji my love" daga mashi kai Basmal tayi sannan Basmal ta bud'e murfin motar ta fice, tana kallan Ammar har ya ja mota ya bar harabar makarantar har se da ya kure ma ganin ta sannan ta shige cikin class.

Sultan ne zaune saman kujera yayi relaxing a cikin office na shi yana juya kujera da yake zaune idanuwan shi a lumshe, ba abinda yake tunawa se Nihal murmushi Sultan ya saki yana tuna yadda Nihal ke zakalkalewa tana mashi masifa, murmushi ya saki Wanda shi kan shi be sani ba, har dimple din shi na lomawa hakan se ya kara mashi kyau, a hankali Sultan ya furta, "oh goshh why do I always have to think about her even since I set my eye's on her, I hate this! lumshe idanuwan shi Sultan ya kuma yi knocking din kofar da akeyi ne yasa Sultan cewa, "come in" cikin honey voice din shi Ammar ne ya shigo hannu shi dauke da file's aje su yayi saman table sannan shima ya samu waje ya zauna yana facing din Sultan ya zuba mashi idanuwa gyara zama Ammar ya kumayi yana kallan Sultan dake ta zuba smile, Ammar yace, "Sultan yau ka duba patient kuwa" ya fad'a yana tsare Sultan da ido zaro ido Sultan yayi yana cewa, "oh my god na manta" Sultan ya ida zancan yana kokarin daukar aluran dake saman table, kallan shi Ammar yayi tare da cewa, "yana ji voice kana with full of joy" murmushi Sultan yayi tare da cewa, "mi ka gani? dariya Ammar yayi yana kallan face din Sultan yadda ya canza yana tanbayar Ammar, Ammar yace, "am sure you having a good time with Nihal" Ammar ya ida zancan yana tsare sultan da ido shima din kallan shi yake zuciyar Sultan na dukan uku-uku me ke faruwa da shine duk yana wannan zancan ne a cikin zuciyar shi rintsi idanuwan shi Sultan yayi ba abinda yake gani se Nihal, a hankali ya sauke su saman fuskar Ammar da ya tsira mashi ido had'e rai Sultan yayi yana cewa, "Allah ya sauwake nayi good time da wannan yarinyar kawai ina cikin good mood ne", dariya Ammar yayi tare da cewa zakayi bayanine Allah ya nunamin ranar da Nihal za tayi wining heart naka Sultan,! had'e rai Sultan yayi tare da cewa, "enough! Ammar bana san irin wannan kidding din let change da subject please" Sultan ya ida zancan yana tatare file's din dake saman table jikin shi yayi sanyi yana fatan Allah karya nuna mashi ranar, taba shi da Ammar yayi ne yasa Sultan juyowa suna facing juna yace, "Na batama rai ko am sorry dude, to min ya hanaka duba patients da wuri wani abu na damun ka ne" murmushi yake Sultan yayi yana kallan Ammar yace, "Uhm wasu abubuwa na tsaya dubawa" Sultan ya fada yana kallan Ammar dake kallan shi da alamar tuhuma, kad'a kai Ammar yayi sannan suka fice tare daga office din.
Chapter 61 · 0% Book details