← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 128

Sashe 45

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Da fitowar Nihal daga part d'in mom taga motaci na shigowa bin motacin Nihal tayi da kallo tare da kau da kanta, motaci Sultan ne suka faka Alex ne ya budewa Sultan murfin mota kamar ance Nihal ta juyo tana juyowa sukayi ido hud'u da Sultan, da kallo sultan ya bi Nihal wadda itama kallan shi take k'asa tayi da kanta tare shigewa part d'in Ammi, tana shiga parlour taga ba kowa jin motsi a kitchen ne yasa Nihal nufar kitchen d'in tana mamakin mi ake a kitchen yanzu bayan ba'a girki a kitchen d'in kowani part se dai a kawo abinci daga babba kitchen, a hankali Nihal ke takawa maganar da taji anayi k'asa-k'asa ne yasa Nihal lafewa jikin bangwan kitchen d'in yakumbo ce da wata baiwa adama tsaye a kitchen yakumbo na cewa, "ki tabata kin zuba guban nan cikin Abinci Sultan ki san duk yadda zakiyi Dara ta matsa a kan Abincin Sultan se ki barbad'a, idan kika min haka kin gama min komai" murmushi Adama ta saki tana juya ido tace, "karki damu jakadiya ta yadda dani zan maki aiki yadda kike so amma da sharad'i se na ji dubus," murmushi yakumbo ta saki tare da yima Adama rad'a a kunne dariya suka saki tare da toshe baki, yakumbo ta cigaba da cewa, "yanzu na san ya dawo kiyi sauri ki aikata abinda na saki, saboda ke kawai na shigo part d'in nan wallahi," murmushi Adama tayi tace, "karki damu komai ze tafi dai-dai," Nihal dake manne jikin bango kitchen ce ta toshe bakin ta, numfashin ta na sama-sama zuciyar ta na tanbayar ta, to mi Sultan ya masu suke san kashe shi, motsin data jine yasa ta barin wajan da sauri Nazili ce ta bin Nihal da kallo tana aika mata harara tace, "mikikeyi a nan? Nazili ta tanbaya tana tsare Nihal da ido, tab'e baki Nihal tayi tare watsa hannuwa tace, "dan na zagaye gidan su miji na nayi laifi ne" Nihal ta ida Zancan tana hard'e hannuwan ta a kirjin ta, had'e rai Nazili yi tare da tab'e baki tace, "mijin ki? hehehe kiyi sauri ki kuskura bakin ki saboda Sultan yafi k'arfi ki malama, ina mai baki shawara kiyi gagawar fad'a mashi ya baki takarda ki dan se ya fi maki nonsense Almajira kawai," tsaki Nihal ta ja tare da shigewa d'aki ta maida kofa ta rufe, Nazili na huci ta wuce d'akin ta tana maimata kalaman Nihal, zagaye d'aki Nihal ta shiga yi tana cewa, mi sultan yayi ake san kashe shi, shafa gashin kanta Nihal tayi tare furzar da iska me zafi wata zuciyar tace ina ruwan ki, kika sani ko rashin mutunci daya saba yi maki ya masu, ko saboda wannan dalilin suke so su kashe shi su huta da halin shi, Amma idan ta lura ai baya wulakanta ma aikatan shi ita kad'ai ya rai na, wata zuciyar tace amma kuma se su kashe shi, wata zuciyar tace idan Sultan ya mutu ke ma ai kin huta da wannan auran mara anfani zaki samu damar jin dad'in to minene idan ya mutu zama Nihal tayi saman kujera ta dafe goshi.

Sultan na shiga part na shi watsa ruwa kawai yayi, ya shirya cikin inner black shirt me uneck, da three quarter brown masha Allah yayi kyau sosai har ya gaji wayar shi ya dauka dake saman bedside drawer sannan ya wuce parlour jakadiya ya gani da Adama suna ta jera abinci a dining murmushi Sultan ya saki yana cewa, "Jakadiya ina wuni" sultan ya ida zancan yana Jan kujera dining, lafiya lau ranka ya dad'e, murmushi Sultan yayi yace, "yau mi aka dafa min" washe baki jakadiya tayi tana cewa, "abinda kafi so shina dafama, Adama a zuciyar tace shi kuma zeyi ajalin ka ba mtsww, wani irin dad'i sultan ya ji tare bud'e warmer miyar, miyar taushe ce tasha naman rago da kaji da yan'ciki se kamshin manshanu take lashe baki Sultan yayi tare da bud'e daya warmer waina ce an mata suya irin me kyanan gyara zama Sultan yayi tare daukar spoon ze d'ibi miyar tun tana warmer a hankali yasa spoon ya d'ebo miyar tare da kai........

```Taku har kullun Salma mas'ud nadabo```
[1/7, 2:27 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
*Story*
*And*
*Writing*✍🏾
*By*
*Salma mas'ud nadabo*👑

🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
(```We are the best among the rest```)

*page: 71_72*

Bayan kowa ya gama breakfast ba yadda Ammi ba tayi da Sultan kar ya je office ba se ya gwada mata cewa wata matsalace ta taso haka ya lalashe ta a kan cewa yana gamawa ze dawo wajan Amaryar shi of coz shima zeyi missing nata haka ya gama tsara Ammi ya fice.

Nihal ta sha kyaututu ka hannu Ammi da mom haka itama Gimbiya jalila haka Nihal ta rik'a zuba masu godiya sannan ta wuce d'akin ta, tana shiga taga Nazili zaune ciki dakin ta, ruwan jinin jikin ta Nihal ta sha tana bin Nazili ta kallo yadda ta daura kafa d'aya kan d'aya saman kujera tana murmushi rai nin wayau mikewa tayi tare da takowa har gaba Nihal shafa fuskar Nihal tayi tare da sakin dariya tace, "oh no! Ashe dama ke Almajira ce hhhhhhh na tausaya ya maki amma" zagaye d'akin Nihal ta shiga yi tana cewa, "ya akayi Sultan ya auri almajira tsintar ciyar make i can't still believe cewa matar Sultan bata da asali bale tushe had'e rai Nazili tayi tare da nad'e hannuwanta a kirji tace, " Asirri kikayi wa Sultan Amma wani bokane me k'ok'ari haka ya maki aiki, kwata-kwata baki dace da rayuwar Sultan ba ina fata kin gane yar talaka Allah yasa ma ba wajan yawan bara ba mama kin tayi cikin ba dan nasan mabarata yadda kuke" ta ida zancan tana d'agawa Nihal gira Kafe ta da idanuwa Nihal tayi tana kallo idanuwan ta taf da kwalla ba kowa ya ja mata rayuwa haka ba se su baffa ya zama dole ta amshi matsayin ta haka, Nazili ce ta d'aga mata haba tana kallan ta tace, "ushhh karkiyi kuka fa gaskiya na fad'a maki baki dace da Sultan ba nayi mamakin yadda Sultan ya iya zama dake ma guri d'aya wallahi, ko baki fad'a min ba na san ciwan yunwa ne ya kashe baba ki da mama ki, kaf dangin ku nasan cewa bame arziki duk taran matsiya ta aka tara, karki damu yanzu kin shigo cikin arziki zaki rabu da tsiya da talauci, Allah yasa kuma baki da bak'ar kafa saboda shi talauci a jinin talaka yake, fad'a min daga naira d'aya har million zan baki ki rabu da Sultan kiyi gagawar cewa ya baki takarda sakikin if not" Nazili ta matsewa Nihal fuska ta cigaba da cewa, "if not se na wulak'an taki gaban jama'a se na tona ko ke wacece," Nazili ta ja tsaki tace, "bitch! kawai" sannan ta fice daga d'aki tare da buga mata kofa, a hankali Nihal take taka d'akin wani jiri na d'ibarta dressing mirror ta dafa hawaye na wanke mata fuska tana maimaita kalaman Nazili tabas ta san bata dace da Sultan ba, me yasa duniya bata san tane miyasa ma aka haife ta a duniyar ne , ko ta wani fani baza ta had'a kanta da Sultan ba shikan shi ya fad'a basu dace ba gashin yau ma ankara nanata mata Kalmar, ce mata akayi san sultan d'in take da zata rink'a jefa mata magana bayan su gwoggo to Sultan ne mak'iyina na biyu inda zan iya yakice shi dana yadda kwalan mangwaro na huta da k'uda, kuka Nihal ta saki tare da duk'ewa tana gunjin kuka babba tashin hankalin ta Allah yasa Nazili karta ta san dalili da yasa ta gudu daga gida kuka Nihal take baji ba gani.

*******************

Akwana a tashi ba wuya wajan Allah satin su Nihal d'aya da aure babu abinda ya canza sultan ya mata Nazili ta mata har k'ara Sultan idan ta gaji tana ramawa gaban Ammi be nuna komai amma da Zara taje part nashi wulak'anci kala-kala.

Shirye-shiryan fara zuwa makaranta Ammi ke tayi ba abinda ba'a siya mata ba Ammi tace surprise za'ayi ma Sultan se dai yaga Sultana ta fara zuwa makaranta kuma ta san haka ze mashi dadi sosai, Nihal ko se murna take komin banza zata samu ilimin boko dama gashin Ammi tace next week malamin islamiyya ze fara zuwa yana koya mata dad'i duk ya ishi Nihal,

Nihal ce kwance saman sofa tayi shirin kwanciya, Sultan na saman bed idanuwan shi na manne da farin glass yana sanye da sleeping robe, dana laptop yake da alama aiki yake can ya d'ago idanuwan shi tare da satar kallan Nihal dake kwance saman sofa ta dunkule dan yau ko blanket yace baze bata ba tausayin tane ya kamashi k'adan, mik'ewa yayi tare da bud'e drawer ya ciro blanket ya k'arasa gaban sofa a hankali yasa blanket ya lulub'e Nihal yana k'arewa kyakyawar fuskar ta kallo, jin dumi ne yasa Nihal bud'e lumsasun idanuwan ta, ta sauke su kan Sultan da Sauri Sultan ya mik'e hannuwan shi na zube cikin Aljihu, juya mashi baya Nihal tayi tare da gyara kwanciyar ta.

*Washe gari*
Chapter 45 · 0% Book details