← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 115 OF 128

Sashe 115

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Warin da gidan keyi kad'ai ya isa ya hana ka hadiye yawu Nazili sai yan yatsine-yatsine take hancin ta dode haka suma sauran maimartaba da waziri ne da Nihal da sultan kawai suke mazewa amma suma warin na damun su ganin halin da Baffa yake ciki ne yasa Nihal da Dara karasawa da sauri suka hada baki wajan cewa, "me ke damun ka Baffa, me a jikin ka haka Baffa wanna wani irin ciwo ne yaya? Dara ta fada tana sakin kuka haka Nihal cikin shashekar kuka tace, "love ka taimaka mu kai Baffa asibiti a duba lafiyar shi dan Allah" cikin shakakiyar muryar shi Tanimu yana wani irin tari ga kudaje nayi mashi rangadi yace, "murya wa nake ji kamar haule? Baffa ya fadi cikin yanayi na mamaki, Dara dake gefen Baffa tace, "ni ce yaya Tanimu nice na dawo gare ka yaya..! numfasawa Baffa yayi yana cewa, "Haulatu.!! Nihal..! Ashe ina da raban gani ku kafin wa'adina ya cika," kara matsowa su Dara sukayi gaban Baffa suna cewa, "baza ka mutu ba Baffa zaka samu lafiya insha Allah daga kanka an gama irin wannan zalinci Baffa" wani irin nishi Baffa yayi ya cigaba da cewa, "rayuwa kenan shiyasa aka ce duk wanda zai gina ramin mugun ta ya gina shi dai-dai da shi idan ka gina shi da zurfi har da kai za'a fada" wani irin tari Baffa yayi wanda yake jin wata irin azaba idan yayi yace, "Haulatu ki yafe ni bani da bakin da zan iya budewa wajan neman gafara ku, ko kun yafe min ba lallai Allah ya yafe min ba dan ba ku kad'ai nayiwa laifi ba harda ubangiji na" Dara ce ta katse Tanimu da cewa, "yaya wace irin magana ce kakeyi haka mara dadi ji, ko dai zafin ciwo ne ke damun ka," nisawa Tanimu yayi yace, "haule kenan ba ko daya baki san komai ba ne haka kema Nihal abubuwa ne kawai ke faruwa ba tare da sani kowa ba, daga ni sai Allah sai indo muka san abinda muka shuka a karkashin kasa wanda shine ke bibiyar mu a halin yanzu, abinda muka shukane muke girbewa..! gabaki daya mutanan wajan sunyi tsit baka jin komai sai sautin kukan Dara dana Nihal da Sara wani irin tari Baffa yayi yace, "wannan bakin nawa ma dake bude Allah ya bar min shine saboda wannan rana wato ranar tuna siriri kun ga hasada bakin ciki gani kyashi ba karamin annoba bace ni Tanimu ita ta kai ni ta baro a doran duniya, duk abinda nayi dan shi yanzu babu ya kare," numfashi Baffa ya kara ja ga kudaje nata yi mashi rangadi sai kayi dauriyar gaske zaka iya tsayawa ka kalle shi bayan Nihal da Dara babu wanda ya iya karasawa gaban shi, Ashad da Gimbiya jalila da Nazili jikin su yayi mugun sanyi tunda Baffa ya fara zanyanu zance musanman Ashad Baffa ya cigaba da cewa, "haulatu Nihal ku yafe ni ba kamar ke Nihal kunga mutuwar Usaini kunga mutuwar Hassan kunga mutuwar Habu nad'ewar Hansatu sanadiyar barin ki gida Haule" Baffa da kuka yaci karfin shi da kyar ya iya furta cewa, "nine sanadi nina aikata..! kowa na wajan kallan-kallo aka shiga Nihal kuwa zaro ido take tana girgiza kai nan da nan Baffa ya shiga zayano masu duk katobara daya aikata ya ida zancan yana kuka yace, "ku yafe ni...! Dara kuwa wani irin marayan kuka take tana jera ajiyar zuciya tana cewa, "ka cuce mu yaya Tanimu ka tafka babban kuskure mara gyaruwa..! mikewa Nihal tayi dafe da kunne tana ja da baya saboda bakin ta ya mutu mudus bakin ciki ma ya hana ta cigaba da kuka wani abu yayi mata tsaye a zuciya tana tuna irin halacin da Abba yayi wa Baffa amma ya cuce su haka, ya cuci yan uwan shi haka jini Abban shi ganin yadda Nihal keyi kamar sabuwar kamu sultan ya nufe ta da sauri ya jawota ta jikin shi, rungume shi Nihal tayi gam tare da sakin wani irin marayan kuka mai tsuma zuciya mai saurare tana cewa, "ka cuce mu Baffa ka rabani da farin ciki na ka mai dani mara gata ka jefa rayuwar mutane da yawa cikin bakin ciki saboda farin cikin ka, ka cuce mu Baffa ka maida Abba na mahaukaci hakan be ishe ka ba har sai da yayi mutuwar wulakanci, ka nad'e umma ka kashe kawu Hassan Usaini bakin cikin abinda ke faruwa ya kashe kaka da inna saboda farin cikin ka Allah ba ze taba barin ka haka ba sai ka dangwama cikin masifa da bala'i har duniya ta tashi..! insha Allah rahamar ubangiji ta yanke maka daga nan har kiyama, ban taba jin natsani wani mahaluki a duniya ba kamar ka, bana tunanin ko cikin magagin bacci zan iya furta na yafe maka". Baffa dake kwance shame-shame sautin kuka shi kawai ke ta shi sai ihu gwoggo dake daki tana hauka tuburan yana cewa, "na rokeki Nihal" cikin dakewa Nihal tace, "masifa da bala'in duniya sune ajalin ka, na tsane ka na tsani gani ka tir da halin ka" gabaki daya muta nan wajan ras-ras suke jin kalaman Nihal idanuwan su waje suna kallan ta suna kallan Baffa, da gudu Nihal ta fice sultan ya bita a baya Dara ma mikewa tayi tana aikawa Baffa mugun kallo tace, "Allah ya isa tsakani mu da kai Tanimu..! gabaki daya muta nan wajan sun tsume waje daya sunyi cirko-cirko wani irin tausayi da imani ya shige su musanman Gimbiya jalila da Nazili.

Sara kuwa ban da kuka ba abinda take bata taba tunanin muguntar su Baffa da rashin imani su ya kai haka ba mikewa Sara tayi da kyar tana cewa, "me yasa kayi haka Baffa me yasa hudubar shedan ta zauna maka kai da gwoggo, kun cuce mu ban taba tunanin muguntar ku da rashin imani ku ya kai haka ba, kunyi sanadiyar rasa rai d'aidaya har bakwai a duni..! abinda ta fara jine ya sata cijewa tana dafe bango tana kuka mai cin rai ba komai bane sai nakuda durkushewa Sara tayi dafe da ciki tana wash ciki na tana wani irin kuka da sauri Ammi da Adda suka rufa ma Sara haka itama Dara nakuda sosai Sara take dan haihuwa ce ta zo mata gadan-gadan ko kafin a kai ta asibiti ta haihu alkyabar jikin su Dara suka cire suka mata runfa dan amsar haihuwar ta.

Nihal na fitowa waje durkushewa tayi cikin dashashiyar muryar ta tace, "ya Allah wannan wace irin cutarwa ce Baffa ka cuce mu ka ci amanar zuminci" ta ida zancan tana wani irin kuka har da marin kanta take ko mafarki take kalaman data ji saboda sunyiwa kunna ta nauyi sai sanbatu take jikin ta sai rawa yake Sultan da Basmal a tare suka danno a guje zuwa wajan Nihal Ammar na biye da su a baya rukota sultan yayi ya juyo da ita suna facing juna cikin muryar shi mai sanyi yace, "hayaty dan Allah ki natsu ki dawo hankali ki dan Allah..! Sultan ya ida zancan yana rungume ta tsam a jikin shi yana mai cigaba da cewa, "dan Allah ki dawo dai-dai ba zan juri ganin ki cikin wannan halin ba, ni kadai nasan yarda nake ji, kina kokarin gefa kanki cikin wani hali ke da abinda ke cikin ki, innalillahi wa'inna ilaihi raju'un zaki rinka furtawa itace makamin mumini kin ji matana" sultan ya ida zancan yana hura mata iskar bakin shi mai sanyi a wuyan ta a hankali ya talabo da fuskar Nihal yasa harshanshi yana goge mata hawayan fuskar ta tas, maida ta kirjin shi yayi ya rungume ta tsam tayi lamo tana sauke ajiyar zuciya jefi-jefe yana shafa bayan ta, zuciyar tace ta fara tashi zamewa tayi daga jiki sultan ta koma gefe tana wani irin amai ruwa Basmal ta mikawa sultan ya wanke mata fuska ta kuskure bakin ta sultan ya talabo ta wani irin jiri Nihal kawai take gani a hankali take lumshe ido tana budewa, murfi mota sultan ya bud'e ya sata cikin mota ya kule murfin motar Ammar ne yace, "dude ya kamata ku wuce gida kafin mu karaso tana bukatar huta"
"Abinda nake kokarin yi kenan Ammar" sultan ya ida zancan a raunane
"Toh shikenan ka kula everything will be okay" daga kai sultan yayi ya zagaya ya shige mota driver ya ja.

Ajiyar zuciya Basmal ta sauke tare da shigewa jikin Ammar tana cewa, "wannan wani irin rashin imani ne aunty Nihal ta bani tausayi" Basmal ta ida zancan tana matsar kwalla Ammar yace, "ko zamu bisu ne dan bana san abinda ze taba min ke da" Ammar ya ida zancan yana shafa cikin Basmal wanda ya fito amma ba sosai ba a hankali Basmal ta daura hannu ta saman na Ammar suna jin motsin baby murmushi Ammar ya saki yana cewa, "baby yana so ya gaisa da daddy" duka Basmal ta kai mashi Ammar ya goce yana dariya ya bud'e mata murfi mota suka shige driver ya ja.

Nihal dake kwance saman fafadan kirjin sultan tana sauke ajiyar zuciya jefi-jefi gidan da taga sun nufo ne ya sata mikewa zaune tana bin gidan da kallo ba abinda ya fado mata a rai sai lokacin da take zuwa da bokitin kokwan ta Ammar na mata juye, tunawa tayi da lokacin da gwoggo tayi mata bugun mutuwa da kyar ta iya karasowa da jan jiki toshe baki Nihal tayi tana sakin marayan kuka tare da fadawa jikin sultan ta kankame shi tana gunjin kuka, lumshe ido sultan yayi siraran hawaye na mashi zarya parking din driver ne yasa sultan goge hawayan shi da sauri dagowar da zeyi ta cikin mirror ya hango bala driver na matsar kwalla saboda duk abinda ya faru yaji a kunna shi tausayi da imani ya shige shi da takaicin hali irin na Baffa daukar Nihal sultan yayi cak suka shige ciki.
Chapter 115 · 0% Book details