← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 127 OF 128

Sashe 127

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau Nihal ta cika 40days tsaye take gaban dressing mirror da daddare Yasmin da bariri na bayan ta da Dara a hankali ta saki towel din dake jikin ta, ta mika hannu wata fitinana riga Dara ta saka mata white mai zare-zare daga kasa a tsatsage take gaban boobs din ta kamar zasu fasa kirjin ta su fito, ta murje tamkar bata taba haihuwa ba zama tayi aka tsantsara mata make up, gashin ta ya nanad'e kamar taliya ya baje a gadan bayan ta kanta na dauke da wasu flowers a sama, Alkyaba blue aka saka mata wadda ta sha aiki da gold zare kungun ta na sanye da jigidar gold, da hula alkyabar ta rufe fuskar ta Bariri na rike da baby cikin towel din sarauta na baby's ya sha kyau ya gaji sai kamshi suke zubawa haka suka fito daga bedroom, fresh milk mom ta bawa Nihal ta kafa kai ta shanye tas sannan suka fice daga part din zuwa nasu.

Bangaran Sultan ma Sinbul da Barma ne ke shirya shi cikin sleeping robe din shi White yayi kyau har ya gaji, sajan shi ya kwanta luf-luf da shi sai smile yake saki yana fitar da sanyayan kamshi, dakin ya sha gyara da red flowers yana fitar da kamshi da sanyi AC, gefe ga bed din baby pink shima ya sha gyara karma ace bed nasu dake baje da red flowers haka suka gama shirya shi suka fice kai sunkuye, tsaye yake yana facing tangameman mirror yanayin yana kallan agogo.

Murda kofar da akayi ne ya sasa lumshe ido yana juyo jigidar dake kugun Nihal yarda take amsawa, wani yar yaji lokaci daya a hankali juyo yana sakin smile Nihal na rike da baby kanta sunkuye tana smile mai tsada ga wani kamshi ta daya cika dakin, a hankali sultan ya tako gabanta a hankali ya dago da fuskar ta "masha Allah..! ya furta a hankali yana bin fuskar ta da kallo tamkar ya cinye ta, da shu'umin kallan shi mai kashe mata jiki yake bin ta, kukan da baby ya saki ne yasa gabaki dayan su daura idanu su kan Amir dake hannu Nihal yana shuru kafa yana kuka ganin suna kallan shi ya sashi yin shuru yana raba ido, dariya Nihal da Sultan suka saki suna ja mashi kumatu a tare suka sakar mashi pack a kumatu amsar Amir Sultan yayi yana mashi wasa har ya kwantar da shi saman bed din shi suna Lila shi yana dariya yana wasa a haka bacci ya dauke shi.

Ajiyar zuciya Sultan ya saki tare da juyo da Nihal suna facing juna matso da ita yayi jikin shi sosai yana kissing nata yana cewa, "I miss you hayaty" ya dauke ta cak kamar baby bai dire ta ko ina ba sai saman bed yana romance din ta daga nan suka lula duniyar ma'aurata.

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya hada-hada biki ake ba kama hannu yaro yau dinner zaune suke gabaki dayan su a parlour Ammi ana masu kunshi mai kyan gaske Basmal tace, "masha Allah kunshin nan yayi kyau aunty Nihal" murmusawa Nihal tayi tana cewa "na gode" Minal ce ta shigo tana cewa, "gaskiya anyi mana san kai kunshin ku yafi kyau kar ma ace na aunty Nihal yafi na kowa kyau" dariya Nihal ta saki tana mata gwalo tace, "je ki goge naki a maki wani" murmusawa Minal tayi tace "aike mai kyau ce aunty komai kikayi yana maki kyau shi yasa kunshi ya hau hannu yayi das" smile Nihal tayi tace, "thank you"
"Ni ko ina Amir?
Murmushi Nihal tayi tace, "yana hannu love tun dazu ya amshe shi yanzu haka na san duk inda suke ya fara rigima raban shi da abinci tun safe" har aka gama masu kunshi suna hira,

part nasu Nihal ta wuce a bedroom ta sami Sultan dauke da Amir yana ta kuka yana lallashin shi dafe goshi Nihal tayi tana cewa, "oh Amir dama na san by now kanan kana rigima, am sorry prince umma ta tafi ta bar ka da yunwa umma bata kyauta ba" hannu ta kai ta amshe shi tana cewa, "shhh ya isa mana love ya hana ka zama ko sorry" d'an murmushi Sultan yayi ya zauna kusa da Nihal yace, "hayaty nayi missing naki sosai" ya ida zancan tare da jawo Nihal jikin shi dake ba Amir nono cikin muryar rad'a Nihal tace, "Nima haka love nayi missing naka ai yanzu muna tare har zuwa time din da zamu je dinner ko love" daga mata kai Sultan yayi yana kallan lallan dake hannun ta yace, "hayaty wannan lallan yayi kyau sosai waya maki shi? murmushi Nihal tayi tana juya hannu ta tace, "na gode" hannu Sultan ya kama yana kissing na shi ringing din wayar shine ya katse mashi hanzari ganin Ahmad manne a screen din wayar ya sashi cewa, "aifa baza su barni na huta ba, hayaty bari nayi sauri nayi fresh up kafin Ahmad ya biyo ni dan tun da nace zan maido Prince na dawo yake kira na" dan turo baki Nihal tayi cike da shagwaba tana cewa, um, um za tayi magana Sultan ya sakar mata light kiss a lips nata, ya shiga toilet ya watsa ruwa ya fito ya shirya cikin milk yadi yayi kyau sosai ya daura hula, da ido Nihal ta bishi saboda kyan da yayi mata murmushi Sultan ya saki ganin yarda Nihal ke kallan shi yasan ya mata kyau hura mata iskar bakin shi mai sanyi yayi yace, "kallan fa?
"kayi kyau love" murmusawa Sultan yayi yace, "thank you hayaty" ya cigaba da cewa, "bari naje na dawo" ya ida zancan tare da sakar ma Nihal pack da baby.

Da daddare yan'mata sunyi shiri ciki ashoben suna dinner can na hango Nihal sanye da fitted gown light purple ta kama jikin ta tayi kyau shape din ta ya fito das da shi, sai ka rantse budurwa ce bata taba aure ba saboda kyan da ta zuba masha Allah, kan ta na dauke da head dark purple tayi kyau sosai, Sultan na sanye cikin shada shi Ash tasha aiki irin na sarautar nan a haka suka shige mota zuwa dinner.

```Taku har kullun salma mas'ud nadabo```
[3/11, 5:56 PM] salma😝: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🕊 *SAUYIN RAYUWA* 🕊
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
*Story*
*And*
*Writing*✍🏾
*By*
*Salma mas'ud nadabo*👑

🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
(```We are the best among the rest```)

*Page:145_146*

Fadin tsaruwar wajan dinner bata lokaci ne amare sunyi kyau har sun gaji, kallo daya zaka masu kasan suna cikin tsantsar farin ciki, karasawa gaban Nana Nihal tayi tana smile dukawa tayi tana mata magana a kunne tana smile daga nan aka fara gudanar da shagulgulan bikin, an cashe anyi ciye-ciye da lashe-lashe naira tayi kuka haka taro ya watse cikin farin ciki.

Washe garin aka daura auran angwaye da amare a babba masallacin maimartaba sarkin kano inda manya-manyan yan kasuwa da k'ososhin gwabnatin sun halari daurin auran Ashad da Nana Nazili da Ahmad Sara da Sunusi kan sadaki lakadan naira dubu hamsim, angwaye baki ya kasa rufuwa karma ace Ashad dake ta zuba rawar kai cikin su, gabaki daya su cikin fara shada babba riga da Alkyaba angwayan suka shirya gwanin ban sha'awa duk idan suka gilma sai an tanka saboda yarda suka bada, kan sun had'e Sultan Ammar Ashad Ahmad sai Sunusi, maroka sai bin su suke suna busa, algaita sai tashi take.

Cikin gidan ma amare sunyi kyau har sun gaji gidan ya kacame da busa, a daran rana flight din amare da agwayan ya tashi zuwa US honeymoon Ahmad da Nazili kuma Dubai suka wuce, bayan kwana biyu su dawo US da zama.

*_Bayan shekara biyar_*

Yara ne maza guda biyu suna ta gudu a company da alamar bama Nigeria bace saboda yanayin tsarin wajan da yarda yaran ke sanye cikin kayan sanyi suna wasa da ball a cikin garden, Amir da khalifa ne suke ta wasa gefe guda kuma yara ne mata guda uku da namiji daya cikin su suna wasa da Teddy's, dan namijin cikin sune ya amshe baby dake hannu d'aya daga cikin matan ya bale mata kai kuka ta saki har da birgima ta ruga tana cewa, "Habibty..! Ciki muryar ta mai tsamin da yarin ta ganin yarda take kuka yasa, Akram bin Duha yana lallashin ta yana gyara mata baby ya mika mata washe baki tayi ta sakar mashi pack a kumatu ta ruga tana cewa, "ya Amir ya Khalifa zo ku ga baby na da ya Akram ya gyara min" murmushi suka saki gabaki dayan su sauran matan dake gefe suna wasa rugowa sukayi da gudu suka nufo su Amir suna bin su suna gudu suna zagaye compound suna dariya suna jefa masu snow din dake kasa, lallacewa iyayan sukayi suna kallan yaran nasu yarda kan su ke hade.

Nihal dake zaune saman resting chair ta daura kanta saman chest din Sultan yana shafa kanta sai zuba rashin kunya suke, Ammar da Basmal dake zaune gefe Basmal ta daura kanta saman cinyar shi pillow ya dauka ya wurgawa Sultan yana cewa, "na lura baka jin kunyar mu wallahi, bari dai yaran nan su zagayo su gan ku haka, idan baka ji kunyar mu ba ka ji kunyar ya'yan ka" dariya Sultan yayi ya kashe mashi ido Ahmad da Nazili dake tsaye gaban abun gasa nama da tulelan cikin ta wanda haihuwa ta biyu ce sai zuba mashi shagwaba take yana lallashin ta yana feeding nata nama, gefe Ashad da Nana suna sunuka wani iri ihu ta saki ganin ta cinye shi tana dariya rugawa tayi da gudu ganin ya biyo ta tana dariya tana mashi dariya, ta shige cikin yaran suna gudu tana mashi gwalo.

After sun gama duk abinda suke suka hada kan ya'ya su zuwa cikin gida bayan sunyi sallah isha suka had'e a dining area nan ma sabuwar hira suka bud'e sai pictures suke da video's cikin jin dadi da SAUYIN RAYUWA mai cike da annuri da farin cikin mai daurewa.

*_Bayan wasu yan shekaru_*
Chapter 127 · 0% Book details