Sashe 126
Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan komai ya lafa Sara ce zaune da yaya mudi har Dara tana labar ta mashi irin mugun halin da su gwoggo suka aikata suka birne har da irin mutuwar wulakancin da Baffa yayi, duk da cewa Dara ba taso labarin ba sai dai ya zatayi da Sara tunda ta fara zuba, jikin mudi sanyi yayi sosai yana mamakin rashin imani irin na iyayan nashi, dama ashe su suka rusa masu family saboda san abin duniya tir da irin wannan hali inji mudi, Dara tace, "kul na kuma jin irin wannan maganar ta fito daga bakin ka, Allah ya ji kan yaya tanimu daya rigamu gidan gaskiya" suka amsa da Amin har auran da zatayi Sara ta fadawa mudi da abin kunyar da ta aikata sam bai ji dadi hakan ba har fada yayi mata kan watsar da tarbiyar ta da tayi, koda yake ta wani fannin bai ga laifin ta ba, sai na gwoggo kalaman da take fadawa Nihal ne suka tabata kan diyar cikin ta, bayan sun gama tattaunawa suka tsaida magana kan cewa gobe zasu wuce Shanono ya duba jiki Gwoggo, har yamma tayi mudi na gidan suna hira da Sara har Nihal ta zo suka dasa da ita cikin farin ciki ya kara mika godiyar shi a kan namijin kokari da tayi na kulla da Sara, duk da abinda su Baffa suka aikata mata murmusawa Nihal tayi ta gwada mashi ba komai ya wuce, kiran sallah magrab ne ya tashe su zuwa yin sallah farin ciki fal a zukatan su.
Washe garin da safe Sara da mudi suka dau hayar shanono a cikin motar da Sunusi ya aiko wa Sara ta hidimar biki, tun a kan hanya datijuwar dake kula da gwoggo ta kira Sara tana kuka ta sheda mata cewa, duk yarda tayi da gwoggo ta kasa haka ta fella a guje tayi kan hanya, tifar dake zuwa kauye dibar icce zuwa birni tayi sama-sama da gwoggo ta take ta ta mutu har lahira, da kuka suka karaso shanono lokacin ana kokari kai gwoggo makwancin ta.
Bayan komai ya nitsa Sara ta kira Dara ta sheda mata rasuwar gwoggo, jikin Dara sanyi yayi tana kara yima Sara gaisuwa, sannan ta katse wayar dama tana part din mom ta labar ta mata rasuwar gwoggo, jikin mom sanyi yayi tayi mata gaisuwa ita da Gimbiya jalila kasancewar itama tana part din suna tattaunawa kan sha'anin bikin dake karatowa.
kasancewar mom keda girki data je turakar maimartaba ta sheda mashi rasuwar gwoggo, washe garin da safe maimartaba suka shirya zuwa gaisuwa kasancewar Nihal tayi nauyi tana zaune gida tare da yakumbo da sauran yara, yakumbo na bata kyakyawar kulawa, sai dai kiran Sara tayi ta mata gaisuwa ta waya tare da mudin, Nana ma ta zo gidan suna ta shan hira har Nazili ta dawo ta daga office itama ta zauna aka dasa sabuwar hira da ita kasancewar bata samu damar zuwa gaisuwar ba sai dai tayi ma Sara gaisuwa ta waya.
Bayan sadakar uku mudi da Sara suka dawo kano ya cigaba da kasuwancin shi, yana samun rufin asirri shi jefi-jefi yana zuwa duba Sara, Sara kuwa tana ta shan gyara kafin lokacin biki, ga kyakyawar kulawa da take samu wajan yaya mudi ya mai data yar lele shi da Nihal har da Dara ta rasa wayafi ji da ita cikin su.
Yau dai kam Nihal wuni tayi wani iri tana jin jikin ta da kyar ta samu tayi sallah azahar tana part din mom duk yinin yau, mom na lura da yanayin ta, da ta tanbaye ta sai tace ba komai can dai wurin 4:00pm ciwo ya kara tsanani Mara da bayan ta suka rike, kuka Nihal ta saki dafe da ciki tana fadin duk addu'ar da ta zo bakin ta tana kiran mom, fitowa mom tayi daga bedroom tana cewa, "daughter lafiya? Ganin yanayin da Nihal take ya sata karasawa a kidime Nihal dake nukurkusu tace, "mom ciki na baya na kugu na"
"Sannu daughter haihuwa ce kin ji daure ki rinka addu'a" kama ta mom tayi da taimakwan Dara suka wuce da Nihal asibitin cikin gidan.
Bangaran sultan kuwa tun daran jiya yake kiran layin hayaty ba a dauka ba, har yau da safe kafin su ida meeting ya fito dan ya rasa natsuwar shi hawo flight yayi zuwa kano.
Yana zuwa gida aka fada mashi Nihal na asibitin cikin gida, Kaitsaye can ya nufa isar sa tayi dai-dai da shigar da Nihal labour room yana juyo yarda take kwalla mashi kira, duk addu'ar da tazo bakin shi kawai yake fadi duk ya kidime ya rude, da sauri mom ta tare shi yana kokari kunna kai labour room din a kidime, idanuwan shi jawur zame hannu mom yayi tana kokari magana, Gimbiya jalila ta mata alama ta kyale shi Ammi kuwa ban da zarya ba abinda take Nihal dake labour room da karfi take furta, "innalillah wa'inna ilaihi raju'un, ya sallam ya Allah...! Sultan.. Sultan ku kira min Sultan..! da sauri Sultan ya shige labour room din Nihal dake kwance tana nakuda gadan-gadan zuba na karyo mata tana kara kiran suna shi tana cewa, "Sultan..! da sauri ya karasa ya kama hannu ta yana goge mata zuba yana cewa, "ina tare da ke hayaty Allah ya sauke ki lafiya yi nishi hayaty kin ji kara" da karfi Nihal ta saki nishi can tayi lakwas tana cewa, "bazan iya ba mutuwa zanyi ya sallam ya Allah" tana maganar tana kara kankame hannu Sultan tana kuka, Sultan kuwa kuka yake kamar karamin yaro, saboda Nihal na cewa zata mutu a hankali yake mata addu'a a cikin kunna ta a hankali yana cewa, "zaki haihuwa lafiya mata na insha Allah" Nihal na rike da hannu shi gam wani irin nishi Nihal ta saki tare da furta *SULTAN SALIM* da karfin ta inda yayi dai-dai da fadowar baby boy tare da sakin kuka wata ajiyar zuciya Nihal ta saki hawaye na bin kuncin ta wani murmushi Sultan ya saki, yana shafa kan Nihal a hankali ya sakar mata pack a goshi yana kara godewa Allah daya sauki Nihal lafiya da abinda ke cikin ta, bayan nurse ta yankewa baby cibi jiki na rawa Sultan ya amshi baby yana kallo yana smile, yana kallan Nihal dake murmur da ido ganin ta sauka lafiya ya fita ya sheda wasu mom cike da murna suka rungume shi musanman Ammi sai pack take mashi a kumatu tana cewa masha Allah, Alhamdulillah.
Ana cikin haka aka turo Nihal saman goda nurse na rike da baby da sauri Basmal ta karasa ta amshe baby tana smile, amsa baby mom tayi bakin washe tare da mikawa Ammi, Sultan kuwa ya kasa rufe baki saboda murna Ammar da Ashad rungume Sultan sukayi suna taya shi murna harda Ahmad bakin shi ya kasa rufuwa dimple din shi sai lomawa yake haka aka wuce da Nihal waiting room.
Sai wajan isha Nihal ta tashi daga wahalalan baccin daya dauke ta, a hankali ta bud'e lumsasun idanuwan ta, ta sauke su kan Sultan dakewa baby huduba su Ammi duk suna dakin har da maimartaba, aje baby Sultan yayi a hankali ya jinginar da Nihal wadda duk kunya ta rufe ta saboda rawar kafar da Sultan yake mata tamkar ba gaban su maimartaba ba, baby ya dauka ya mikawa Nihal yana cewa, "bashi ya sha na san yana jin yunwa" Sultan ya ida zancan yana smile kallan baby Nihal take tana smile kamar shi daya da baban shi tamkar Sultan yana baby dagowa Nihal tayi karaf suka hada ido da sultan kashe mata ido yayi yana cewa, "bashi mana" Ammi dake gefe tace "to dasa kunya beran tanka sai ka ba manya ka waje, ko kunya baka ji gaban uban ka kana cewa ta ba yaro nono Allah ya kowa mu ni kuluwa, sai ka tashi ko, yar tahali kan nan ko abinci bata ci ba ka tasata da yaro kana cewa ta bashi nono ka bari ko tea ta kurba, matsa ka ban guri" sosa yake Sultan yayi ya mike Nawwara da Minal dake zaune dariya suke kasa-kasa kallan da Sultan ya watsa masu ne ya sasu hadiye dariyar, mom kuwa girgiza kai tayi tana maka mashi harara maimartaba kuwa murmushi yayi ya kama hannu shi suka fice tare da waziri, Adda dake zaune mikewa tayi tana murmusawa ta karasa gaban gadan da Nihal ke zaune tana ba baby nono.
Kwana Nihal daya a cikin asibitin gida ta dawo cikin gida part din mom ta sauka kasancewar a nan zatayi wanka, Sultan kuwa kullun yana makale da hayaty da rigima da komai mom ke tasa keyar shi waje dan ta lura fama zatayi da shi, dan sam bai yarda da zaman ta part din mom ba, kullun sai yayi bitar mai ya sami part nasu har zaunawa yake yana tsara mom ai shi likita ne zaifi kowa bata kyakyawar kulawa, yana kai aya mom zata rarumo mabigi idan Gimbiya jalila na kusa ta tare tana dariya shi kuma ya fice da sauri, wata irin kula yake nunawa baby dan ko gajiya ba yayi da daukar shi, su Ammar su rinka mashi tsiya suna cewa sai ka ce kan shi aka fara haihuwa, Ahmad kuwa cewa yake a kyale shi yayi suma lokaci suke jira ya zo.
Ranar suna yaro yaci suna maimartaba ana kiran shi da Amir, maimartaba kuwa farin ciki lullube shi yayi ganin ya samu takwara, har filli yabawa takwara da gona da doki da god'iya saboda tsabar murna yaba Sultan ya aje mashi idan ya girma ya bashi nashine halak malak, Sultan kuwa ban da godiya ba abinda yake ita kanta Nihal din ta sha kyauta hannun maimartaba mom kuwa sarkar diamond ta bata, Gimbiya jalila kuwa jigidar gold ta bata kit guda, Ammi kuwa trolley din alkyaba ta bata da kayan baby, Nihal ta amshi kayan sosai har na ban mamaki su Aunty Aisha ma ba'a barsu a baya ba taga gata anyi ciye-ciye da lashe-lashe kudi sunyi kuka anyi bidiri sosai.
Haka Nihal ta cigaba da wankan ta sosai baby Amir ke samun kula ya kara wayau, gyara mom takewa Nihal sosai ta kara fresh da kyau kasancewar ta kusa cika 40days ta kuma part nata.