← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 121 OF 128

Sashe 121

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da suka fara biyawa shoprite sukayiwa su mama siyaya acewar sultan basa je hannu biyu ba, daga nan suka wuce jan bulo unguwar su Nana basu wani sha wahala gane gidan ba saboda sunyi anfani da location horn sultan yayi mai gadi ya wangale masu geta sultan ya shige da motar shi yayi parking motar a parking space dan murmushi Nihal tayi tana cewa, "yau dai mun zo, kora fi ya kare" su shukura dake wasa a compound suna ganin Nihal suka gane ita ce da gudu suka nufo motar suna cewa, "aunty Nihal oyoyo" bale murfin motar Nihal tayi tana cewa, "love bari na shiga amma ka jira ku gaisa da mama kafin ka wuce" ta ida zancan tana kokarin fita jawota sultan yayi yana nuna mata kumatun shi murmush Nihal ta saki ta sakar mashi pack a cheeks din shi, lips din shi ya nuna mata makale kafada Nihal tayi tana kokarin fita daga motar fisgo ta sultan yayi ta fada saman fafadan kirjin shi ya sakar mata kiss a lips din ta murmushi Nihal ta saki tare da ficewa, su shukara suka karaso suka rungume Nihal sai murna suke sannan ta bud'e back seat ta ciro siyayar da ta masu ta mika masu da gudu suka shige gida suna kwalawa Nana kira.

Nana dake zaune tana kallo a parlour ta jiyo ihu su shukara suna cewa, "aunty Nana ki zo Aunty Nihal ta zo" da sauri Nana ta mike tana cewa, "oyoyo kawas kai amma naji dadi" da sauri Nana ta ruga ta rungume Nihal tana cewa, "kin cika alkawari wallahi da na dauka baza ki zo ba dana ga har four ta wuce"
"na isa na ce zan zo na fasa na hadu da bitar ki, yanzu dai ina mama?
"ai fa ko zama ba kiyi ba na cika ki da surutu"
"mun cika juna dai"
"mama na bedroom yanzu nan ta shiga wanka zauna" kitchen Nana ta shiga ta kwaso wa Nihal kayan motsa baki ta cika tray da su ta dawo parlour ta aje mata sannan ta koma kitchen ta dawo dauke da tray din abinci ta aje tana cewa, "bari na kira mamar nasan yanzu ta fito daga wanka"
"to Nana amma duk wannan kayan da kika jibge min a gaba ni da wa,? harara Nana ta maka mata "bari na dawo sai ki fadi min baki ci kaitsaye kiga yarda zanyi dake" dan murmushi Nihal tayi Nana ta haye sama dan kirawo mama su gaisa.

Aunty Aisha ce tsaye gaban dressing mirror tana murza hoda sanye take ciki tsadadan atamfar ta wanda ta amshi jikin ta Nana ta shigo daki tana cewa, "mama Nihal ta zo tana parlour tunda ta zo take tanbayar ki tana so ku gaisa"
"toh ki ce mata gani nan zuwa naga d'iyar tawa" to Nana tace tare da ficewa ta koma parlour tana cewa, "ina babba yaya tare da shi kuka zo kuwa?
"eh mana tare muka zo"
"shine sai ki bar shi waje? ki ce mashi ya shigo mana"
"dadi na dake sauri ki bari mama ta fito mu gaisa ai, shima sai ya shigo su gaisa"
"haba kawas kin bar shi waje ko ba komai yayan miji nane" dariya Nihal ta sheke da ita tana cewa, "to uwar azarbabi ki bar a daure tukun" duka Nana ta kaiwa Nihal tana dariya gocewa Nihal tayi tana cewa, "sai na fadawa love kin dake ni" ganin Nana ta matsa kan bai kamata ta bar sultan waje ba yasa Nihal mikewa cike da raha ta fice ta sami sultan a waje ya biyewa su shuraka suna ta zuba mashi surutu, murmushi Nihal ta saki mai kara mata kyau tace, "love mu shiga ciki ku gaisa da mama" to sultan yace tare da kama Hannun shukara suka bi bayan Nihal.

Koda mama ta fito Nana ta samu a parlour tace, "ina daughter tawa?
"Taje ta shigo da sultan tare suka zo ta bar shi waje shi ne na ce bai kamata ta bar shi waje ba" murmusawa mama tayi tace "kin kyauta kuwa a bar mutum waje ko parlour baki ai ya zauna"

Abinda ta ganine yasa Nihal daskarewa tsaye, tana bin Aunty Aisha da kallo idanu ta cike da kwalla, anya da gaske aunty Aisha ta gani ba mafarki take ba kuwa, Aunty Aisha ma ganin Nihal ne ya katse mata zance a zabure ta mike zuciyar ta na lugude tana kallan fuskar Nihal duk da Nihal ta goge tayi fresh hakan be sa ta mance kamanin ta ba, tsayawa cak Nihal tayi ta kasa gaba ta kasa baya sai idanu ta dake waje cike da kwalla tana kallan Aunty Aisha, sultan dake bayan ta ganin yarda ta tsaya cak yanayin ta ya sauya alamar ba lafiya juyo da ita sultan yayi har a lokacin idanu ta waje jijiga ta sultan yayi yana tanbayar ta lafiya, bakin ta na rawa tace, "Da gaske aunty Aisha nake gani kanwar umma love da gaske ita nake gani ba mafarki nake ba," kallan Aunty Aisha sultan yake itama ta daskare waje daya hawaye na wanke mata fuska tace, "ba mafarki kike ba daughter da gaske ni ce kika gani" ragowar hawayan dake makale a idanu Nihal ne suka gangaro tana cewa, "ita ce aunty Aisha da nake fada ma saboda ita na zo birni" murmushi ne ya subucewa sultan yana gogewa Nihal hawayan ta yana cewa, "ba kuka ya kamata kiyi ba godewa Allah zakiyi da ya hada ku" murmushi take wasu hawayan na kara biyu kumatun ta, aunty Aisha da hawaye ke mata anbaliya tace, "Ashe ina da raban sake ganin ki a idanuwa na Nihal ashe labarin diya ta Nihal na dade ina ji" Nana dake gefe mamaki ya lullube ta ta kalli Nihal ta kalli mama, da sauri Nihal ta nufo aunty Aisha haka aunty Aisha rungume juna sukayi tare da saki kuka a tare dago da fuskar ta mama tayi tana kissing kumatun ta tana kallan Nihal tace, "Ashe kina raye Nihal babu irin neman da bamuyi maki ba dan ganin cewa kin dawo gare mu" mama tana maganar siraran hawaye na mata zarya a hankali Nihal ta daura hannu ta saman na aunty Aisha tana cewa, "ba mafarki nake ba ashe na dade ina tare da yar uwa ta ban sani ba ashe akwai ranar da zan saku a idanuwa na" share mata hawaye Aunty Aisha tayi ta zaunar da ita suna facing juna murmushi ne ya subuce masu lokaci daya aunty Aisha na makale da hannu Nihal tace, "Allah mai iko Allah na gode maka daka amshi addu'a ta," kallan sultan mama tayi dake tsaye tana murmushi tace "zo ka zauna d'a na" kasa da kai sultan yayi yana sosa keya ya duka har kasa cikin ladabi ya gaishe da mama, mama da bakin ta ya kasa rufuwa ta amsa da wani shauki tace, "ina zuwa ya kamata Abban Nana ya ji wannan dadadan labarin da su yaya sani" mama ta ida zancan tana ciro wayar ta. Nana kuwa mamaki ya hana ta magana da kyar ta iya furta, "dama ke ce yar uwar tawa da su mama suke nema ido rufe" wani irin murmushi Nihal ta saki tana daga mata kai da sauri Nana ta karasa gaban ta ta rungume ta cike da murna.

Dawowa aunty Aisha tayi ta zauna tana smile tace, "yaya sani na kan hanyar zuwa ya zo yaga wannan albishir Nihal ta dawo gare mu, saki jikin ki daughter haka kai ma son ko ruwa baku sha ba" murmushi kawai su Nihal ke zubawa musanman Nihal da farin ciki ya mamaye zuciyar ta.

Koda su yaya sani suka zo sukayi tozali da Nihal zo ku ga murna Nihal kuwa taga gata wajan su baba sani har da baba khabir wanda duk abinda ya faru baya kasar dan jiya ya dawo kasar, dama sunyi maganar Nihal da aunty Aisha kan zasu cigaba da bincike har Allah yasa a gano ta koda gawar ta ce, sai gashi yau Allah ya bayana ta gare su, bayan komai ya nitsa Nihal ta kwashe duk abinda ya faru da ita ta shedawa su mama sai dai ba tayi gigin fada masu auran dole akayi mata da sultan ba, sun tausaya mata sosai tare da ganin namijin kokarin sultan daya aure ta da su kan su iyayan nashi, Nihal taga soyayya da gata kowa nan yake da ita hatta sultan yaga so sai zuba mashi godiya suke kan rike masu daughter da yayi amana ya bata kyakyawar kulawa kunya kuwa ta hana sultan cewa komai, sallah magrib ne ya tashe su zuwa masallaci su Aunty Aisha suka wuce bedroom dan dauro alwala.

Bayan sun idar da sallah mama na kokarin cire hijab din dake jiki ta tace, "amma dai tanimu ba shi da imani ko kadan shiyasa san da yaya sani ke so a saurara mashi naki yarda saboda kwata-kwata hankali na be kwanta da shi ba Allah dai ya sauwake" Amin Hajiya farida tace da Nana mama ta cigaba da cewa, "shi kuma wannan yaro ya matukar kyautawa bamu da abinda zamu iya cewa family din shi sai Allah ya saka masu da alkairi" gabaki daya suka amsa da Amin sannan suka baje suna ta fira har aka kira isha suka gabatar da sallah.

Nihal kuwa taga tatali da gata dan kuwa sun rasa ina zasu tsoma ta saboda tsabar murna, aunty Aisha kuwa cewa tayi sultan ya bari su kwana gobe da safe sai su tafi gabaki dayan su gidan dan su kara mika godiyar su wajan maimartaba da Ammi dan ba karamin halaci suka masu ba, hakan yasa sultan cewa to sannan ya kira su mom da maimartaba ya shide masu sosai sun taya Nihal murna.

Daran yau kuwa hira kawai suka sha da aunty Aisha tana kara jinjina kokarin irin na su maimartaba da halaci da sukayiwa diyar tata, Nihal kuwa dakin mama ta kwana su uku sultan kuma da Abban Nana ya kwana cike da kewar Nihal din shi, haka itama Nihal din duk hira da ake cikin nishadi hakan be hanata kewar sultan ba musanman yarda ta sama kwana saman fafadan kirjin shi.
Chapter 121 · 0% Book details