← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 128

Sashe 85

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Aunty Aisha ce zaune gaban yaya sani tana matsar kwalla tace, "haba yaya sani yanzu haka zamu zuba ido kan yarinyar nan, yau kimani wata biyu kenan ina maka magana kan yarinyar nan Nihal, ya kamata tanimu ya d'andana kudar shi amma ka rintse ido ka ce a'a" aunty Aisha ta ida zancan tana rushewa da kuka ta cigaba da cewa, "da ace yaya hansatu na raye baza ta tab'a yafe mana ba, abinda muke aikatawa be dace ba, tun tana raye ba ruwan mu da ya ta kwana ya ta tashi gashi yanzu ma diyar tata mun watsar da lamarin ta, bayan muna da rufin asirri da zamu iya ja da tanimu ni dai ba zan cigaba da zuba ido ba wallahi," yaya sani ya katse mata hanzari da cewa, "Aisha wai mi yasa baza ki gane abinda nake nufi ba shima fa tanimu waya gari sukayi ba yarinyar nan, ban ga dacewar a kai tanimu ga hukuma ba, saboda shima tamkar mahaifin ta yake bana tunanin zeyi abinda ze cutar da diyar d'an uwan shi, idan ma da sa hannun su Allah na gani, kuma zanyi iya bakin kokarin yan'sanda su gani inda Nihal take nima abun na damuwa, amma maganar mika tanimu Hannun hukuma ban laminci da ita ba"
"toh shikenan yaya tunda bazaka dau mataki ba ni zan dauki mataki duk inda Nihal ta shiga a duniyar nan dole tanimu ya fada mana, dan ba tsoran shi muke ji ba idan ma mutuwa tayi sai ya fadama, ni dai kam se inda karfi na ya kara akan maganar nan kaga tafiya ta..! Aisha ta dau jakarta tana kuka hajiya farida matar yaya sani tana cewa, "ban ga laifin ki ba wallahi ai bazeyu ba shima alhaji ban san kafewar nan ta micece ba, ya wuce asasu bayan kanta su ci duka ai zasu fadi inda suka kaita ina anfani mutane mugaye ina goyan bayan ki dari bisa dari" hajiya farida ta ida zancan tana rako aunty Aisha compound har ta shige motar ta, ta bar harabar gidan tana ciwan baki sannan Hajiya farida ta shigo cikin gida tana kokarin wuce alhaji sani yace, "farida..! tsayawa tayi cak sannan tace, "idan ba maganar yarinyar nan zaka min ba da irin matakin da zaka dauka ba ni da kai ba wata sauran magana, duk sanda ka janye wannan bakar al'adar taka zamuyi magana, koma haihuwar ta tanimu yayi aka neme ta aka rasa ai ma ji dalilin bale kuma a matsayin sa na wan uban ta sannan gobe idan Allah ya kai mu zamu wuce shanono da yan'sanda" sannan hajiya farida ta haye sama ta bar yaya sani.

*******

Abubuwa sun rincabe sun tsakude a gidan tanimu dan abinda zasu ci yanzu gagara su yake saboda duk wata kadara daya mallaka ta kare wasu sun kone kanikancin ma yaran sun gane cutar su yake tuni sun bar aikin, komai ya rushe komai ya tabarbare yau kimani wata guda kenan yana kwance yana ciwo ko tashi be iyawa danasani da nadama sun rufe shi wulakanci babu wanda be sha a hannu gwoggo, turo kofar da gwoggo tayi ne yasa tanimu dago ido yana kallan ta cike da masifa tace, "ni dai wallahi na gaji da wannan masifa tanimu idan ma zaka mike ka mike, ko kuma kasan nayi ina dalilin kullun cikin fidda kayan gida nake ina saidawa saboda mu samu nasawa a bakin sallati na gaji wallahi kama san nayi wallahi dubi yadda na rame na lallace kamar bani ba indo, nan gaba kad'an sai mun koma almajiranci na sani, toh wallahi ka sani mindin na gaji gida zan koma cikin dangi da yan'uwa tunda ina dasu kuma nasan zasu amshe ni hannu bibiyu" hawayan wahala ne ke sulalowa tanimu dajin dacin maganganun da gwoggo take watso mashi masu kama da harshan damo, kwata-kwata gwoggo bata damu ba se cigaba da cewa tayi, "kai kuma da an fara magana se hawaye kai ga makwarara sarki tsiyaya kai ka sani shawaraki kawai" jin kakarin amai ne yasa gwoggo fita waje a guje Sara ce keta amayar da garin rogwan da suka sasak'a tunda safiyar Allah, se amai take kamar zata amaye yan'hanjin ta sallati gwoggo ta rafka tana tafa hannuwa tace, "Mi nake gani Sara karki ce min cikin shege kika dauko min nabani ni indo, tashi dan ubanki kimin bayani" Sara da ta galabai ta da kyar ta iya debo ruwa ta wanke bakin ta tare da share wajan gwoggo na tsaye tana kokarin wucewa gwoggo ta fisgo ta tace, "zaki fada min wani tsinanene ya maki ko saina kashe ki" gwoggo ta ida zancan tana kirbar Sara kamar Allah ya aikota kuka Sara take tana ihu da kyar ta samu gwoggo ta saurara mata tana haki tace, "zaki fada min koko? cikin kuka Sara tace, "wallahi gwoggo ban san waya min ciki ba" dokewa Sara baki gwoggo tayi tana cewa, "a ruwa kika sha cikin ko min dan ubanki" muciya gwoggo ta dauko zata makawa Sara ta zunduma ihu tana cewa, "zan fada..! cikin shashekar kuka tace, "wallahi gwoggo ban sani ba saboda ba mutum daya nake bi ba"
"laaaha'ilaa gwoggo ta ida zancan tana cewa, "na bani ni indo yaushe raban ki da al'ada dan ubanki wanene na karshe wanda daga shi baki sake al'ada ba," sauke numfashin Sara tayi tana cewa, "Audu giya..! sallati gwoggo ta saki tana cewa, "wannan matsiya cin dan shaye-shayan wanda daya wuce se gori ya dauka, wanda nayi daduro da shi san da ina yan'matanci ki rasa wa zaki bi se shi tsoho sa'an uban ki wannan ma ai yama girmi uban naki, tallaka fitik fakara'u alalrurati na shiga uku ni indo..! zama gwoggo tayi tana matar kwalla tana cewa, "kin cuce ni Sara da ilimin ki da komai, ko cutar (S) aka ce Audu giya nada ita ban gardama a halin yanzu dai, nayi asara kudin tara dana baki da kika je boko dan ki waye ashe tukunya kike shiga" tanimu dake daki duk abinda gwoggo ke fadi yana ji yau ya tabatar da mi ya aura dai-dai da halin shi ya samu yayi kuka kamar zuciyar shi ta tarwatse yayi danasanin abinda yayima yan'uwan shi babu abinda yake gani sai su a idanuwan shi suna firgitashi tabas yasan karshan shine ya zo yana mai rukwan Allah ya taimake shi Nihal ta dawo ya nemi gafara ta kafin Allah ya dauki ran shi, Allah sarki kanwata haulatu ko tana ina yasan tana raye amma ya mata kurciya ko ina take a duniya yasan baza ta taba dawowa kauyan nan ba, sai dai idan asirrin daya mata ya kare kuma abinda be taba yuyuwa ne saboda boka yadade da mutuwa tun bayan rasuwar Habu kuka ne ya kubuce mashi.

*****

misalin karfe 4:30pm jirgin su ammar ya isa US kaitsaye masaukin su suka wuce iyakar haduwa wajan ya had'u fadin tsaruwar shi bata lokaci ne bayan sun ci abinci sun dan huta Basmal ta wuce toilet dan watsa ruwa haka shima Ammar.

Basmal ce tsaye gaban dressing mirror daga ita se towel ta nad'e gashin kanta da wani tana shafe jikin ta da lotion mai kamshi, turo kofar da akayi ne ya sata dagowa Ammar ne ya shigo gabaki daya rudewa Basmal tayi tana neman abinda zata rufe jikin ta da shi abin ma dariya ya bashi yace, "duk ke kad'ai" rintse ido Basmal tayi tare da rufe fuskar ta da tafin hannun ta Ammar kuwa gabaki daya ya rikice a hankali Ammar ya tako gaban ta ya rungume ta ya saukar da nannauyar ajiyar zuciya yana shinshina kamshi ta, cikin murya rada yace, "my love ki je ki dauro alwala ki zo muyi sallah mu godewa Allah daya nuna mana wannan rana" Basmal ko bakin ta ya mutu da kyar ta iya jan kafafuwan ta ta shige toilet ta dauro alwala ta fito a zaune saman daduma ta sami Ammar after dress kawai Basmal tasa tare da sa hijab sallah raka'a biyu suka gabatar tare da godewa Allah, bayan sun idar Ammar ya juyo ya kama kanta ya mata addu'a sannan ya saki murmushi yana kallan Basmal mikewa yayi ya bud'e fridge ya ciro fresh milk ya tsiyaya a glass cup tare da janyo Basmal jikin shi kunya duk ta rufe ta yana bata tana amsa har ta shaye shima ya sha sannan Basmal ta shirya cikin night dress din ta doguwar riga dai-dai gwiwa me d'an siririn hannu sannan ta haye bed ta kwanta kashe haskyan dakin Ammar yayi shima ya kwanta tare da janyo Basmal jikin shi wasa ya shiga yi da ita daga nan ya hada bakin su waja daya yana yi mata rikitantan kiss gabaki dayan su sun fita hayyacin su (ganin haka yasa na sulale na fice ba dani ba salalan kaza)
Chapter 85 · 0% Book details