← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 128

Sashe 33

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sanye yake da inner white shirt me uneck da three quarter black ya kama jikin shi sosai yayi kyau kwarjinin shi ya k'ara fitowa a hankali yake takawa kamar me tausayin k'asa a haka har ya k'arasa part d'in mom zaune ya hango ta saman kujera murmushi ya saki har dimple d'in shi na lomawa a hankali ya k'arasa ya rungume ta baya murmushi Gimbiya tayi tana cewa, "my son" kissing forhead d'in ta yayi tare da zagayowa ya zauna tare da daura kanshi saman cinyar mom shafa kanshi take tana cewa, "my son kana cin abinci kuwa"
"Eh mana"
"Se naga kamar ka rame son" d'an murmushi Sultan yayi yana cewa, "kawai dai kinyi kwana 2 baki ganni bane shiyasa" ya fad'a yana mikewa "bari na je wajan ammi nasan yau zamu sha drama" dariya Gimbiya tayi tace, "kai dai baka ji" dariya Sultan yayi.

direct part d'in ammi ya wuce ammi da fitowar ta daga dakin Nihal kenan taga Sultan saman kujera zaune ya lumshe idanuwa kamar me bacci, harara ammi ta maka mashi tace, "kai miya kawo ka nan? A hankali ya bud'e lumsasun idanuwa shi, har a lokacin ammi na harara shi yace, "zuwa nayi na gaishe ki ," oh na dauka b'atan kai kayi ai" a zuciyar ta kuwa wani irin dad'i ammi taji ta dauka Sultan na fushi da ita ne, amma yanzu ta yadda ba fushi yake da ita ba, Sultan yace, "kina shan maganin ki kuwa matar" had'e rai ammi tayi Dan raban da tasha maganin ta har ta manta, harara ammi ta maka mashi tace, "ai yanzu se ka zo ka cigaba da duramin kwayoyin tunda ka zo" murmushi Sultan yayi tare zauna da ammi yace, "maganin fa is good for you ammi yanzu Abu kad'an na iya faruwa ki samu Matsala saboda baki shan maganin ki please ki rink'a sha ko bana nan kin ji matar, ni fa lafiyar ki nake so ba komai ba," murmushi ammi tayi tace, "toh zan rink'a sha ta ida maganar tana shafa gefen fuskar Sultan smile yayi yana cewa, "ammi zan sha fura" ja mashi ceeks tayi tace, "dama shi ya kawo ka.

```Taku har kullun Salma mas'ud nadabo```
[1/7, 2:27 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
*Story*
*And*
*Writing*✍🏾
*By*
*Salma mas'ud nadabo*👑

🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
(```We are the best among the rest```)

*Page: 57_58*

A kwana a tashi ba wuya wajan Allah yau dai aka sallamo Nihal daga Asibiti masha Allah ta murmure ta d'an k'ara kyau saboda natsuwar da ta samu na kwana biyu, Ammi da Basmal se nan suke da ita a harabar gida motocin suka faka. Nihal ko tunda suka nufo bakin gate gidan bakin ta ke hangame, bata k'ara rud'ewa ba sai da aka bude masu murfin mota, baki a sake take bin gidan sarauta da kallo wadda zata iya cewa raban da taga mulki da sarauta mai tsarin irin na gidan har ta manta, Basmal ce ta janyo hannu ta ganin ta tsaya tak'i gaba tak'i baya, binta Nihal tayi kamar rakuma, duk inda suka wuce se bayi sunyi k'asa da kai tare da zubewa suna kwasar gaisuwa, wani miyau Nihal ta hadiya tana cewa a cikin zuciyar ta Ashe dama da manyan mutane irin haka nake tara, lalakam kirkin su ammi ya kai tunda har suka iya bata lokacin su a kai na, Ashe dama duniya akwai masu kirki bayan yaya, ba abinda zata iya cewa ammi se dai Allah ya k'ara bud'i, shigowar su part d'in Ammi ne yasa Basmal sakin hannun Nihal ta zauna saman kujera tana murmushi tana bin Nihal da kallo wadda ta tsaya cak a parlour kamar wadda ruwan jikin ta ya tsotse, Jakadiya Dara dake goge-goge ce tabi Nihal da kallo, kallan Nihal take sosai tana so ta tuna ina ta san fuskar ko ba yau ba tasan wata me fuskar jin k'anta ya mata nauyi yasa Dara watsar da tunanin ta na murmushi Dan Nihal ta mata, murmushi ammi ta saki tana cewa Dara, "ya kika gani" tace ma Dara murmushi Dara tayi suna magana da ammi cikin mulki da sarauta Wanda se Wanda ya taso a cikin su ze gane manifar su, Dara ce tayi murmushi tace, "yadda kike so haka za'ayi ranki yadad'e komai ze tafi dai-dai" dariya Basmal tayi ita da ammi, janyo Nihal ammi tayi ta zauna da ita saman kujera kusa da ita ammi tace, "ki saki jikin ki Nihal nan ma kamar gida ne, duk abinda kike buk'ata kimin magana" sannan ammi ta nuna Dara tace, "wannan da kike gani jakadiya ce ita ce shugabar bayin gidan nan duk abinda kike so ki mata magana" kai Nihal ta d'aga ta cigaba da bin parlour da kallo kamar k'war idanuwan ta zata fito, hannun ta Ammi ta rik'e su ka Shiga wani d'aki fad'in tsaruwar dak'in b'ata lokaci ne komai na d'akin pink and white ne se royal bed yana sanye da bedsheet White se royal chair guda biyu pink da table a tsakiyar su se tangameman mirror tsaye, gefe kuma dressing mirror ne da drawer k'asan d'akin carpet ne me laushi pink and white, wasu hawaye ne su ke k'ok'arin sulalo wa Nihal ta had'iya Ashe tana da raban shiga rahamar uban giji, Ashe zata samu SAUYIN RAYUWA goge hawayan tayi dake gangaro mata tayi tana k'ara bin d'akin da kallo kamar a film, ammi ce ta katse mata tunani da cewa, "Wannan d'akin ki ne Nihal idan be maki ba ko baki San colour d'in dakin kimin magana" ware manyan idanuwan ta Nihal tayi tana cewa, "Bani da abinda zance se dai nace na gode Allah ya k'aro bud'i" girgiza mata kai ammi tayi tace, "bana san wannan godiyar taki kin ji kamar Basmal kike a guri na" kwalawa wasu bayi mata guda biyu Ammi kira tayi, cikin rawar jikin suka k'araso kan su a k'asa kowace cikin su gashin kanta ya sha two baby's cikin ladabi Yasmin da Barira suka ce, "Barka da zuwa Sultana, Allah ya k'ara nisan kwana Gimbiya" kallan-kallo ammi da Nihal suka shigayi watsar da abinda kunnan ta ya ji mata Nihal tayi tare da sakin murmushi, Ammi tace, "daga yau Ku zaku rink'a kulawa da Sultana kamar yadda zaku kula da Basmal" d'aga kai su kayi a tare sannan Ammi ta basu izinin fita.

Bakin mirror Dara ta janyo Nihal tana k'are mata kallo daga sama har k'asa, ita dai Nihal bin su take dana mujiya Dara ce tace, "Yasmin ki had'awa Nihal ruwan wanka" da Sauri Yasmin da Barira suka shige toilet Dan hadu ruwan wankan Nihal, ruwan wanka suka had'a na sosai a cikin kwamin wanka sannan suka fito da wani zani sharara d'an k'ararami, Dara ce tasa hannu tana k'ok'arin cirewa Nihal kayan ta ware idanuwa Nihal tayi tana kallan ammi idanuwan ta taf da kwalla tana kallan ammi, girgiza mata kai ammi tayi tace, "karki damu duk abinda za'a maki haka tsarin yake kin ji" tana maganar tana murmushi sannan Ammi da Basmal suka bar d'akin suna smile, haka dara ta cirewa Nihal kayan ta duk da kunyar da Nihal ke ji tana nok'e-nok'e zanin da su Yasmin suka dauko shi suka nad'awa Nihal sannan suka nad'e mata gashin ta suka so ke shi da wata yar kibiya, jakadiya Dara na rike da ita suka shige toilet su Yasmin na bayan ta rik'e da bathrobe da towel haka Nihal ta bi su kamar gunki, suna shiga toilet d'in tayi mutuwar tsaye saboda haduwar toilet d'in da tsaruwar shi, cikin kwamin wanka Dara tayi ma Nihal nuni da ta shiga a hankali ta zura santala-santalan kafafuwan ta janye zanin jikin ta Yasmin tayi, yar k'ara Nihal ta saki tare da yin zaman yan buri a cikin kwamin wankan, Barira da Yasmin dariya suka saki lokaci d'aya jakadiya ta watsa masu harara simi-simi suka fice daga toilet d'in suna dariya k'asa-k'asa, in tak'aice maku Dara ce tayi ma Nihal wanka ciki da bai sannan ta mata wanka da ruwan turare daga nan tasa ta cikin hayaki na turare ta lulube ta zani se da hayakin ya ratsata turaran ya kamata sannan ta yaye zanin tare da bata bathrobe tasa sannan ta nad'e mata jik'akyan gashin ta da towel duk kunya ta lulub'e Nihal.

Gudu suke a doki suna dariya Sultan ya mik'e saman dokin yana yima Ammar gwalo yana dariya saboda yayi ma Ammar nisa, Jan lizamin dokin shi Ammar yayi yana cewa, "Sultan zan kama Kane, wallahi wannan lamarin akwai San kai kayi ban yadda da wannan tseran ba ka dawo a sake," dariya Sultan saki har dimple d'in shi na lomawa ya k'ara ma dokin shi gudu yana magana da karfi saboda yayima ammar nisa sosai yace, "ba wani San...!! Be ida magana ba aka duke mashi kai da wani k'atan icce wutar Sultan ce ta dauke ya tafi taga-taga tare da sasatau ruk'wan da yayi ma linzamin dokin shi kafin yayi wani yunk'uri an k'ara maka mashi ta gaba k'okarin rik'e na gaban yake aka k'ara maka mashi iccan a keya rike keyar shi Sultan yayi yana fida numfashi sama-sama yana ganin biji-biji, haniniya dokin Sultan ya fara da karfi, ammar gudu ya k'arawa dokin shi jin haniniyar dake tashi isowar shi wajan yayi dai-dai da guduwar samarin da suka kawowa Sultan hari da sauri ammar ya sauko daga doki yana isa gaban Sultan yana fadowa daga duki sumame.
Chapter 33 · 0% Book details