Sashe 128
Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Gida ne ya cika makil da al'umma da alama nadin sarauta ake yarda gidan ya cika ba masaka cinke cikin nadin har da yan ketare, yan jarudu sun cika gidan makil ba kowa ake nadawa ba sai Sultan sarkin garin kano da Ammar wazari Sultan da idanuwan shi cike da kwalla haka shima Ammar al'umma sai taya su murna suke, ana gama nadi fadda ta dauka da "gyara kintsi da kyau..! gabaki dayan muta nan dake fadda sukayi sunkeye bazgaye fadawa dake zagaye da Sultan suna cewa, "angaishe ku, an gaishe ku..! algaita sai tashi take ana kirari haka taro ya watse.
Gabaki daya su zaune suke a main parlour suna jiran maimartaba busar dake tashi da algaita zai shedama sarki ya shigo cikin gida alamar an gama nad'i Nihal dake zaune mikewa tayi tsaye sanye take cikin silver alkyaba an mata dinki da gold zare, tana sakin murmushi Sultan ne ya shigo da Ammar cikin shirin su na nad'i gabaki dayan muta nan parlour mikewa sukayi Basmal da mom da Gimbiya jalila wanda yanzu sun tsufa Ammi kuwa na zaune saman wheelchair jikokin sun zagaye ta suna mata kiriniya, har da koyangin dake part din gabaki daya zubewa sukayi har da Nihal sukayi sunkuye bazgaye da kallo Sultan ke bin su shi da Ammar suna smile, har sai da Sultan ya zauna saman doguwar kujera sannan gabaki dayan su suka dago Nihal sai sakin murmushi take shima Sultan yana aika mata, jawabi yayi na yan mintocin sannan suka jeru camera man ya dauke su kowa ne fuskar shi dauke da fara'a Nihal na makale da Sultan Basmal na makale Ammar Nazili na makale da Ahmad Nana na makale da Ashad sun wani saki murmushi lokaci daya camera ta haska su.
Nihal ce sanye cikin alkybar ta black tayi wani irin kyau, ta kara haske da girma bayi mata na take mata baya tana tafiya cikin isa da mulki tana murmushi mai tsada mai kara mata kyau, Habibty da aka ce ne ya sata waigowa dauke da fara'a saurayi ne matashi wanda ba zai wuce 20years ba ya kira ta kamar su daya da Sultan tamkar antsaga kara sai dai wannan yaro ne kan Sultan, murmushi ta saki cikin surprise tana bin shi da kallo shi da kannan shi dake bayan shi guda hudu tana kara fadadan murmushi ta cike da farin ciki ta bud'e masu hannu suka karaso gare ta rungume ta sukayi suna dariya ja ma saurayin kumatu tayi tana cewa, "masha Allah my boy ka kara girma yaushe ka iso baka sanar da ni dawowar ka ba, me yasa kake haka son baka san sanar da mu dawowar ka Nigeria" murmushi yayi yana cewa, "na sanar da Abbi da kanne na ko" ya fada yana jan kumatun yar autar su, dan had'e rai Nihal tayi tace "wato abun yar launin fata ce" Nihal ta ida zancan tana yima d'an nata harara wasa kama kunna shi yayi yana cewa, "sorry habibty next time ke zan fadawawa kin ji" murmushi Nihal ta saki tana cewa, "good boy Allah ya maku albarka ya'ya na bari naje wajan Abbin ku Amir ka kula da su" yar karamar cikin su ciki tsamin muryar ta tace, "Habibty zan biki wajan Abbi please ki je dani," shafa kumatun ta Nihal tayi tace, "Mamana yi hakuri dare yayi gobe akwai school ki je wajan Yasmin ta baki chocolate ki kwanta kiyi dream mai dadi" turo baki tayi tana makale kafada daukar Hafsat Yasmin tayi tana mata wasa tana cewa, "ya hakuri Gimbiya muje na baki labari mai dadi har bacci ya dauke princess," washe baki Hafsat tayi tace, "mu je aunty Yasmin" pack Nihal ta sakar mata tana murmushi Amir ya ja sauran kannan nashi suka wuce part na su yana masu wasa.
Murmushi Nihal ta saki idanuwan ta cike da kwalla a hankali take takawa tana zancan zuci tana cewa, nice Nihal din nan yar talla nasha yawo k'afa ba takalmi a kauyan mu na sha wahala rayuwa nayi kwana yunwa, lokaci daya Allah ya kawo min SAUYIN RAYUWA mai daurewa har karshan rayuwa ta insha Allah, Allah ya kawo min farin ciki mai daurewa ban taba mafarkin zan zama Gimbiya ba, sai gashi yau na zama matar Sultan yar gata a wajan mijina abin kauna ta farin ciki rayuwa ta ina san ka Sultan..! ka zamo haskyan rayuwa ta farin cikin ruhi na yar lele a cikin zuri'ar ka, ka bani ilimi wanda nake tunkaho da shi yanzu tunda na cika burina na zama shugaban likitocin Nigeria rayuwa kenan, Allah na gode maka daka bani Sultan a matsayin miji uban ya'ya na..! Nice Nihal mahaifiyar Amir da Akram da jamal da Khadija da Hafsat, nice NIHAL...! hawayan dake makale a idanuwan ta ne ke kokari zubuwa lokacin yayi dai-dai da isowar ta bakin kofar turakar Sultan wage mata kofar akayi, ajiyar zuciya ta sauke tana bin turakar da kallo a hankali ta zura kafafuwan ta, alama tayiwa bayin dake bayan ta su tsaya waje, sannan ta karasa ciki tsaye ta hango sultan hannu shi nad'e ta baya yana kallan tangameman hotan Abba dake manne a bangwan dakin sanye yake cikin milk shada shi babba riga an mata aiki da dark brown zare da alkyaba light brown tasha aiki da dark brown zare kafar shi na sanye cikin takalmin sarauta kanshi na dauke da rawani, sanyayan murmushi Nihal ta saki tana kallan shi ta baya a hankali tace, "Love..! waigowa Sultan yayi idanu shi manne da farin glass ya kara girma da kamala ya manyanta, murmushi ya saki yace, "hayaty..! tare da bud'ewa Nihal hannu da gudu-gudu sauri-sauri ta karasa gaban Sultan ta fada jikin shi ya rungume ta tsam yana shafa bayan ta yana murmushi a hankali ya furta, "I love you hayaty"
"I love you more love..! Um love shine baka sanar dani Amir zai dawo yau ba ko, kun kyau daga kai har d'an naka" murmushi Sultan ya saki yana cewa, "ban so ki wahala min da kanki wajan yi mashi something special kuma kin san halin Amir da tsurfa" um Nihal tace tare da kara shigewa jikin Sultan, kissing forehead nata yayi a hankali ya lallubu lips din ta yana kissing nata ya dauke ta cak tana dariya tana cewa, "love sai yaushe zaka girma ne? mun tsufa fa, muna da saurayin d'a fa" dariya Sultan yayi ya ja ma Nihal hanci yana cewa, "ni ban girma da soyayya, so ba ruwa da girma na," ya ida zancan yana zame mata alkyabar dake jikin ta daga nan wasa ya fara canza zani ganin haka yasa na sulale na fice.
*_ALHMDULILLAH A NAN NA KAWO KARSHAN WANNAN LABARI NAWA MAI SUNA (SAUYIN RAYUWA) INA NAN TARE DA KU MAKARANTA NA, MASOYA LITTAFI NA ALLAH YA BAR KAUNA_*
*_ABUBUWAN DANA FADA DAI-DAI DA WANDA BA DAI-DAI BA ALLAH YA YAFE MANA KURAKURAN MU_*
```TAKU HAR KULLUN SALMA MAS'UD NADABO```
*_GAMAI BUKATAR LITTAFI NA GA NUMBER TA 07063683025_*