← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 128

Sashe 31

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Arabar gida motocin ammi su ka faka, a hankali ta bud'e murfi Mota ta fito ganin ammar ne ya sata Smile gaisawa sukayi a tsaitsaye ta wuce Fada maimartaba Dan fad'a mashi shawara da ta yanke kan zaman Nihal a cikin su, A hankali Basmal ta k'araso gaban ammar cikin takunta na Jan hankali duk wani d'a namiji me lafiya, far tayi da idanuwan ta tana gyara veil din kan ta a hankali take motsa lips d'in ta tace, "ya ammar ni fa fushi nake da kai amma ka kasa ganewa ko," ta ida zancan tana jefa mashi wani kallo da kwayar idanuwan ta murmushi ammar ya saki yana tataro natsuwar shi yace, "ya za'ayi nayi ma gimbiya laifi kuma na kasa bata hakuri tunda ki kaga haka ban san laifin Dana Aikata ba" yana maganar yana makin funny face, tab'e baki Basmal tayi tace, " Kullun se na kira phone na ka tunda kayi tafiya amma bata Shiga, sannan da ka dawo ko ka fara zuwa ka gani baka zo ba ko? se da kowa ya gama ganin ka yauma Dan dai kawai-kawai" tana maganar tana making face nata kamar za tayi kuka, hannuwa ta Ammar ya rik'e a hankali ya furta "am sorry, ban San ki damu dani haka ba dear shiyasa" kukan shagwaba basmal ta Shiga jerawa Ammar janyo ta yayi jikin shi ya rungume ta tsam yana cewa , "Why those tear,? am sorry am here for you dear, ban kyauta ba nasa princess kuka, ya kamata a bani punishment me tsauri" yana maganar yana shafa bayan ta lumshe idanuwa Basmal tayi tare da yin lamo a chest d'in ammar gabaki d'aya su kawo da abinda yake sak'awa a ran shi, ammar yace, miyasa matsayin da ya aje Basmal ada a yanzu babu shi me yasa yanzu baya tananin ta se na Nihal watsar da zamcan yayi tare da kiss forhead d'in Basmal sun dad'e a haka suna juyo harbawa zuciyoyin juna su sannan Basmal ta zame jikin ta a hankali dariya suka saki su duka Basmal tace, "laa har an gama Sallah magrib muna nan" rufe fuskar ta tayi tana dariya tare da shigewa gida da gudu, murmushi ammar yayi tare da barbaza gashin kan shi sannan ya wuce part d'in maimartaba.

D'an siririn tsaki Sultan ya saki tare da kwaso alulurin dake saman table direct d'akin Nihal ya nufa a hankali ya bud'e kofar d'akin tsaye ya hango ta da alama daga toilet ta fito, a hankali take takawa jin kamar ana Kallan ta yasa ta d'agon idanuwan ta, kauda kai Sultan yayi tare da yin magana can k'asan mak'oshi yace, kin ci abinci, "Zama Nihal tayi saman gado tana cewa, "na kasa ci saboda hannuna ya kunbura" ta ida zancan idanuwan ta taf da kwalla, k'arasowa cikin dakin Sultan yayi tare da zama gefen gado yace, "muga hannun" mik'a mashi hannuwata Nihal tayi ya dad'e yana Kallan santala-santala yatsun hannun ta masu tsaho dasu masu kyau duk da hannun ya kunbura be hana aga kyan su ba, sakin hannu yayi tare da janyo warwer da plate, shinkafa da miya ce taji naman rago da kaji ga coslow ya zuba a plate tare daukar spoon, ran nan nashi a had'e kawai zeyi wannan abune saboda tana patient nashi kuma saboda ammi, a hankali ya d'ebo abincin ya kai bakin Nihal kallan-kallo suka shiga yima juna su sun kusan kawashe Rabin sa'a a haka sannan Nihal tayi k'asa da idanuwan ta a hankali Sultan ya ke feeding nata tana amsa, can ta kware ta fara tari ruwa Sultan ya dauko yana bubuga bayan ta a hankali yana cewa, "sorry ! Aje plate d'in Sultan yayi sannan ya bata ruwa tasha tana sauke numfashi, janyo plate d'in yayi Dan ya cigaba da feeding nata, girgiza kai Nihal tayi cikin kasalaliyar murya tace, "na koshi Allah," tab'e baki Sultan yayi tare da aje plate d'in ya dauko alura ya fara zuk'o magani a Sirinji ware idanuwa Nihal tayi a hankali ta fara zamewa daga saman gado ta yunkura zata ruga Sultan ya dam kota, kuka Nihal ta fara tana cewa, "Wallahi ban San allura ka bani magani Dan Allah" shuru Sultan yayi Nihal se mutsu-mutsu take a jikin shi , hannu ta ya tataro gabaki d'aya ya manna su a chest nashi ya rungume ta sosai a jikin shi kuka Nihal ta fara duk yadda taso ta k'waci kanta daga rukwan da Sultan ya mata ta kasa, cikin sanyi murya Nihal ke cewa, "Dan Allah karka min da zafi" ta ida zancan tare da daura kanta saman fafad'an k'irjin Sultan, tana sauke numfashi a hankali, a hankali Sultan ya tsula mata allura zafin da ya ziyar ce tane kad'an yasa Nihal cikwikwiye Sultan tare da sakin kuka me cike da shagwaba ta k'ankame sultan , lokaci d'aya Nihal ta sakar wa Sultan da kasala abinka da lafiyayan namijin, sun dau lokaci me tsaho a haka Nihal idanuwan ta a rintse tana sauke ajiyar zuciya kamar wadda tayi tsere. A hankali Sultan ya zame jikin shi daga na shi, yana sakin Nihal ta fad'a saman gado tana sauke a jiyar zuciya, Sultan kuma ya ja yan k'afafuwan shi tare da zama saman kujera ya lumshe idanuwan shi.

Ammi nashiga fada maimartaba bayan sun gaisa da ammi, take sheda mashi ra'ayin ta kan Nihal tare da fad'a mashi rayuwar Nihal kamar yadda Nihal ta zayana mata, sosai maimartaba ya jinjina maganar Inda yaba ammi goyan baya d'ari bisa d'ari, shiyasa a kullun yake alfahari da mahaifiyar tashi musanman yadda take kyautatawa marayu da marasa karfi, shiyasa wani lokacin yake ganin kamar tare da ammi suke mulkin kuma hakan na mashi dad'i sosai, ammi taji dad'in amincewar d'an nata zuciyar ta fal da farin cikin tabar fada tana sak'e-sake a zuciyar ta.

*****

Bangaran su gwoggo ko da safiya tayi gwggo taji shuru ba motsin Nihal a fusace ta debo ruwa mai sanyi a randa tayi d'akin Nihal tana huci, ganin mudi a d'akin yasa gwoggo zunduma ihu tare da sakin bokitin hannun ta tana k'walawa baffa kira, da gudu baffa ya fito daga d'aki shi da Sara, daukar mudi yayi se asibiti gwoggo se kuka take tana antayawa Nihal zagi tana kuka, baffa ko yara ya tara yan'daba yace su nemo mashi Nihal duk Inda take a kauyan ko a Raye ko a mace.

```Taku had kullun Salma mas'ud nadabo```[1/7, 2:27 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
*Story*
*And*
*Writing*✍🏾
*By*
*Salma mas'ud nadabo*👑

🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER FORUM*🐄
(```We are the best among the rest```)

*Page: 59_60*

Jijiga Sultan ammar yake yana cewa, "Sultan.!! Sultan.!! gabaki d'aya ya rud'e cikin d'aga murya yace, "guards !! security d'in sultan suka k'araso, daukar Sultan ammar yayi jikin shi na rawa har yayi gaba ya tsaya cak yana cewa cikin murya me rawa, "ina so ku bi samarin da suka kawo ma Sultan hari a raye ko a mace Ku kawo min su," yana ida zancan ya wuce da Sultan cikin part nashi, jikin ammar se rawa kawai yake yana tsoran Allah yasa Sultan be samu wata matsala ba yana shiga part d'in sultan fadawan shi sukayi ca suna tanbayar mi ya faru ko saurara su Ammar beyi ba se daya shiga da Sultan d'akin shi ya shin fid'e shi har a lokaci jini na zuba a kanshi duk yawan gashin shi se da jini ya jika shi, a hankali ya tako bakin kofar yace, "bana so ku sanar da kowa cewa ga halin da Sultan ke ciki" d'aga kai su Sinbul su kayi suna zubar da kwalla rufe d'akin Ammar yayi tare da daukar wayar shi ya kira Dr amir saboda baya iya kula da sultan shi kad'ai Amir na daukar wayar ammar yasa kuka kamar k'ara min yaro yana cewa, "Amir ana so a kashe min dude" kuka ammar yake sosai tare zamewa k'asan wajan yana korawa Dr amir bayani Alex dake gaban Dr amir yana mashi dressing ne ya mashi wayar hannu amir Wanda yayi kasake, kuka Alex ya saki yana cewa, "no ! nasan ba abinda ze sami Sultan" Ya mik'e da sauri duk da alokacin k'arin ruwa ake mashi rik'e hannu shi Dr amir yayi yace, "you have to rest Alex," cikin sanyin murya Alex yace, "bana iya jurewa dole na bika" a tare suka bar Asibitin tare da daukar kayan aikin da za'ayi anfani da su bama komai suka kwasa ba saboda A cikin masauratar akwai asibiti,

Gimbiya Nadiya ce ta fito hannu ta dauke da cup d'in coffee subucewa yayi a hannu ta ya fad'i gaban tane ya yanke ya fad'i tana bin cup d'in da kallo, guri ta samu ta zauna tana sauke ajiyar zuciya, Sultan ne ya fadu mata a rai addu'a ta shiga jera mashi duk da bata San halin da yake ciki ba, jin a dafa ta ne ya sata sakin murmushi tunanin ta Sultan ne ganin maimartaba ne yasa ta mikewa tsaye tare da k'ara sakin wani murmushi bayin dake part nata tuni sun fice, jikin maimartaba ta fad'a ta rungume shi tsam ita kanta bata San dalilin canjin nata ba,

A hankali Nihal ta zauna saman kujera bugun zuciyar ta na k'aruwa ta rasa dalilin hakan, lumshe idanuwan tayi a hankali Dara ta mik'e kafafun Nihal tana mata pedicure, su Yasmin suna mata tausa bayan Dara ta gama ta shafa mata wasu mayi ka na musanman a k'afar ta saboda fasan k'afar ta yayi saurin bacewa, mamaki ko hana Nihal magana yayi saboda yadda take gani ana mata cikin zuciyar ta kuwa hamdala take Allah ya kawo mata *SAUYIN RAYUWA* daga ta inda bata tab'a tsanmani ba,
Chapter 31 · 0% Book details