← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 128

Sashe 44

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Adda ce zaune a parlour tana kallo Ammar ya shigo jiki a sanyaye ko sallama ya kasa yi saboda nauyin da bakin shi yayi, har ya wuce Adda dan ko ganin ta beyi ba, Adda ce tace, Ammar! shuru Ammar yayi kuma ya kasa juyowa su had'a ido da Adda tasowa tayi tana k'arewa fuskar Ammar kallo wadda ke cike da damuwa cikin sanyin murya Adda tace, "Ammar lafiya...!! Adda bata ida rufe bakin ta ba Ammar ya fad'a jikin ta, tare da sakin kuka yana cewa, "Shikenan Adda yanzu Nihal ba tawa ba ce Adda, Ashe dama ita ce matar da Sultan ya aura, yau ido na ya gane min Nihal a matsayi matar sultan !! Ammar ya ida zancan ciki sakin kuka mara sauti, haka Ammar ya rink'a yima Adda sanbatu, lalashin shi Adda ta shiga yi kamar k'aramin yaro janyo Ammar tayi ta zauna da shi saman kujera suna facing juna, ita kanta d'an nata ya bata tausayi musanman yadda ya kwalafawa ran shi Nihal kama hannuwan shi Adda tayi duk biyu cikin nata, cikin sanyin murya tace, "Ammar! dago jajayan idanuwan shi yayi yana kallan Adda ta cigaba ta cewa, "nasan cewa Ammar kai mutun ne mai hakuri da tawakali ! ina so ka dauka cewa wannna k'adara ka ce Ammar Allah ya nufa Nihal ba matar ka ba ce, bana so ka sawa kanka damuwa ka ji, ka godewa Allah cewa Nihal d'in hannun na gari ta fad'a kuma aure tayi ba yawan banza ba idan haka ka gani se kafi jin zafin abin, Amma yanzu d'an uwan ka take aure kuma aminnin ka, kai kanka kasan Sultan mutumin kirki ne ze kula da Nihal d'in se dai muce Allah ya basu zaman lafiya kai kuma Allah ya baka wadda tafi ta," sauke ajiyar zuciya Ammar kawai yake yana zubawa Adda na mujiya yana tunanin rayuwar da sukayi a baya da Nihal lumshe idanuwan shi yayi wasu hawaye masu zafi suka sulalo mashi, ya san cewa ya rasa Nihal har abada, hannun Adda Ammar ya kama duka biyun tare da kissing na su, sannan ya mike ya wuce part na shi da kallo Adda ta bi shi ita ma duk jikin ta yayi sanyi dole ta san d'an nata ya shiga wani hali ita kanta data ga Nihal da biki ta yaba da kyawun ta da hankali ta, Allah yaba d'an nata wadda tafi ta, Adda ta fad'a a fili tana mai cigaba da yi mashi addu'a Allah ya cire masa San Nihal dan yanzu ta zama matar wani.

Bayan Nihal ta ci kuka ta gaji ganin tunanin be fishe ta yasa ta shige toilet tayi wanka tana mai addu'a Allah ya rufa mata Asirri tana k'ara rokwan Allah maji rokwan bayin shi dan ta san cewa Allah yana sane da ita da irin wannan tunanin Nihal ta gama wanka sanye da towel ta fito, goge jikin tayi ta shafa lotion me kamshi sannan ta shirya cikin white Jean's da black t-shirt tayi kyau sosai tatare gashin kanta tayi ta maida shi gefe d'aya ta feshe jikin ta da turare , maroon Jan baki ta sama lips din ta d'an kad'an , sannan ta zurawa kafarta flat shoe silver me kyalkyali sannan ta fice daga part d'in sultan dan ta gaji da zaman shuru.

part d'in mom ta wuce cikin sallama ta shiga parlour ba kowa se bayi dake hada-hada ko ba'a fad'a mata ba ta san mom na bedroom gaishe ta bayin suka shiga yi Nihal na amsawa rai sake har ta k'araso bedroom d'in mom, a hankali ta kama handle d'in kofar ta d'an leka kanta mom ta hango tsaye gaban drawer tana gyara wasu album's murmushi Nihal ta saki mom da juyawar ta kenan ta sakar wa Nihal da murmushi tace, "daughter shigo mana" shigowa Nihal tayi kai a sunkuye hannu mom ta mik'a mata Nihal ta kama tana washe baki, tace, mom ina wuni"
"Lafiya lau daughter, yau an tuna da mom ko? daga kai Nihal tayi tana gyara gashin kanta murmushi mom tayi tace, " Ammi duk ta kwashe mun ku," ta ida zancan ta smile, washe baki Nihal tayi tana girgiza kai, janyo hannun Nihal mom tayi ta zauna da ita bakin gado suna facing juna aje Album's d'in hannun ta mom tayi tare da sa hannu ta d'ago da fuskar Nihal suna kallan juna Mom ta saki lalausan murmushi tace, "Masha Allah daughter kina da kyau, gaskiya my boy yayi sa'ar mata dan ma baki sakin jiki dani" mom ta ida zancan tana langwabe kai, washe baki Nihal tayi tace," mom na gode," waro idanuwa mom tayi tace, " son be taba fad'i maki kina da kyau ba ne" mom ta ida zancan tana k'arewa kyakyawar fuskar Nihal kallo, shuru Nihal kawai tayi tana yak'e a warwaran dake hannu mom na gold ta shiga cirewa tana cewa, "Nihal bani hannun ki" cikin zak'uwa Nihal ta mikawa mom hannun ta, a hankali mom ta Shiga sa mata a warwarayan a hannu tana cewa, "nima sun min kad'an dama nace duk ranar da son yayi aure matar shi zan ba mawa, duba ki gani yadda suka maki kyau Nihal, masha Allah komai naki mai kyau ne" mom ta ida zancan tana murmushi washe baki Nihal tayi tare da jujuya hannun ta cikin jin dad'i ta rungume mom tace, "na gode mom sun min kyau ina so" ta ida zancan ta zame jikin ta daga na mom, shafa fuskar Nihal mom tayi tace, "Nihal! A hankali Nihal ta d'ago idanuwan ta tana kallan mom wadda fuskar ta, tayi abin tausayi ta cigaba da cewa, "Ni dai fatana daughter ki zauna da Sultan cikin Aminci Nihal ki kulamin da Sultan," shuru Nihal tayi ta kafe mom da idanuwa a zuciyar ta tace, Allah sarki da yake shi d'an gata ne har wani cewa ake na kula shi mutumin da be San daraja ta ba, ni da bani da mai kula dani se dai ya rink'a cusa min bakin ciki ina shanyewa, jin idanuwan ta na kawo ruwa yasa Nihal lumshe idanuwa tana k'akaro murmushi yak'e, album mom ta janyo tana nunawa Nihal album d'in bikin su Wanda tunda akayi pictures d'in ranar biki ko marmarin ganin su batayi ba, mom se murmushi take tana nuna wa Nihal pictures d'in sun ma Nihal kyau sosai kasancewa daga ita har sultan d'in sunyi smile, har suka gama kallan pictures d'in mom bakin ta na dauke da murmushi, wani album d'in mom ta janyo tana cewa bari kiga pictures d'in son yana baby kiyi dariya bud'e pictures mom ta shigayi Nihal na gani tana murmushi duk da bata gane me mom tace da farko ba Amma jikin ta ya bata Sultan take nufi, wani picture suka kai Wanda aka dauki sultan yana kuka ya b'are baki dariya mom da Nihal suka saki, mom ce ta girgiza kai tana cewa, "sultan akwai rigima kin gan shi ko" wuce picture d'in mom tayi ta kai Wanda ita kadai ce da ciki tayi picture murmushi mom ta saki tace, "kalle ni nima san da ina yarinya kamar ki, nan ina da cikin Sultan ne zanyi haihuwa ta farko maimartaba ne yamin picture d'in lokacin munje Dubai, wata rana kema haka zaki haifi jikoki na, nasan Sultan ze ba grandchildren d'ina kulawa of coz shima yana san children" mom ta fad'a tana fadada murmushi ta, kirjin Nihal ne ya bada daram-daram a zuciya Nihal tace, tab d'in jam dawa zata haihun sultan kowa, ko a mafarki bata Fatan hakan ta kasance jiran lokacin take daza tace ya bata takarda sakin ta dan baza ta juri zama da shi ba kwata-kwata bale akai ga wani Abu wai shi ciki, dafatan da mom tayi ne yasa Nihal dawowa daga duniyar tunani, murmushi yak'e Nihal ta saki tana cewa, "mom bari na koma part d'in Ammi tun safe dana bata magani ban k'ara lek'a ta ba," murmushi mom ta saki tana mai kallan agogo tace, "ke dai ki ce min lokacin dawowar sultan yayi zaki gudu" rufe fuska Nihal tayi kamar gaske tare da cewa, "mom na gode da kyauta" pack mom ta mata a kumata sannan Nihal ta fice.
Chapter 44 · 0% Book details