← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 128

Sashe 87

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bangaran su aunty Aisha sun isa garin kano lafiya kaitsaye suka wuce offishin yan'sanda aka watsa tanimu bayan kanta aunty Aisha ce tace, "idan yayi magana ku sanar mani, ina so ya dandana kudar shi har se ya fada mana inda ya kai mana yarinyar mu" offisa yace, "baki da matsala hajiya duk yadda kika ce haka za'ayi" sannan aunty Aisha ta kad'a kai ta shige mota suka wuce gida.

A harabar gida driver aunty Aisha ya faka mota ta fito kaitsaye cikin gida ta shige zaune saman two star da sami mijin ta yana karanta newspaper murmushi ya saki yana cewa, "my dear har kun dawo? aje jakar hannu ta Aisha tayi tana cewa, "Eh mun dawo dan ma na tsaya gidan yaya sani na sauke hajiya farida, my love abun dai ba dadi wallahi yanzu haka tanimu yana hannun hukuma har se yayi bayani inda Nihal take za'a sake shi, na rasa wannan wani irin taurin kai tanimu yake, kuma duk ta kare ya san inda take har yanzu naki yadda da cewa be san ina Nihal take ba..! Aunty Aisha ta ida zancan tana matsar kwalla lallashin da mijin ta ya shigayi tare da cewa, "my dear ki bar daga hankalin ki insha Allah Nihal zata bayana, yanzu dai ki je ki watsa ruwa ki fito mun shirya maki abinci mai dadi ni da yaran ki" murmushi Aunty Aisha tayi tana cewa "da gaske mijina shiyasa nake sanka" aunty Aisha ta fada tana sakarwa Abban Nana pack a kumatu, "bari nayi sauri nayi wanka na fito, su Nana har sun tafi islamiyya hala?
"eh sun tafi bama ta dade da fita ba dan duk a tunanin ta tare da Nihal za ku dawo,"
"Allah sarki Nana tana san ganin yar'uwan nan tata" aunty Aisha ta ida zancan tare da wucewa bedroom

Duka dai tanimu yasha haka ya rinka zunduma ihu duk da kafafuwan shi na nad'e hakan be hana su jin azabar da yake sha hannun kuratan yan'sanda ba, yayi laushi sosai ya fita hanyyacin shi fuskar sa ta kunbura saboda tsabar kila, da kyar yake sauke numfashi garba ne dake tsaye rike da gora yace, "tsoho banza zakayi bayanine daga ganin ka mugun tsoho ne," tanimu dake ta sauke numfashi cikin gajiyawa yace, "wallahi ni bani na batar da yarinyar nan ba, nima waya gari nayi ban gan ta ba na rantsema da Allah offisa, bani da masaniyar inda take, ni kai na nemanta nake ido rufe a halin yanzu" tanimu ya ida zancan yana sauke numfashi ai kamar ya zuga garba cigaba yayi da duka kamar Allah ya aiko shi se da tanimu ya sume garba ya watsa mashi ruwan sanyi sannan ya fice yana cewa, "zan dawo na cigaba daga inda na tsaya har se ka fadi inda ka kai yarinyar mutane munafiki" kuka Baffa ya saki ya san cewa ko rabin abinda ya shuka be girbeba yanzu ya fara ganin SAUYIN RAYUWA.

******

Misalin karfe 7:00am
Sultan ne ke shiryawa cikin wata suit American rose colour da inner blossom red colour tie din shi kala suit nasa ya saka gem stone rose yayi wani irin kyau masha Allah sultan looks breath taking handsome, briefcase din shi ya dauka ya fito parlour Nihal dake jera abinci a dining da bayi na taya ta, tana sanye cikin red gown wuyan rigar a bude yake gashin kanta ya rufe mata kafadar ta tayi wani irin kyau baki ta ya sha red jan baki haka se ya karawa lips din ta kankancewa, waigowar da zatayi karaf suka hada ido da sultan tsare ta da ido sultan yayi yana kallan ta ita ma shi take kallo cikin zuciyar su babu abinda suke yabawa se kyan juna su da sauri Nihal ta janye idanuwan ta bayin dake taya ta jera kaya a dining kai a sunkuye suka shiga zubewa suna gaishe da sultan sannan suka fice, a hankali sultan ya tako yana takowa yana bin Nihal da kallo har ya ja kujera ya zauna serving nashi Nihal tayi chicken and chips wrap sannan ta tura mashi plate din had'e rai sultan yayi yana cewa, "kin manta abinda na fada maki kenan? cikin kosawa da halin sultan Nihal ta shiga feeding din sultan abincin yana ci ko kallan fuskar ta ba yayi saboda yadda ta had'e rai har ta gama feeding nashi sannan yace, "dauki briefcase nawa yau ke zaki rakani bakin mota" had'e rai Nihal tayi tana gunguni sultan yace, "mi kika ce? Dauke kai Nihal tayi tana rike da briefcase din sultan har suka karaso compound bakin motar shi sannan Nihal ta mika mashi briefcase din shi a hankali sultan ya matso har suna jin saukar numfashin juna su ya sakarwa Nihal pack a kumatu sannan yace, "ki shirya anjima idan na dawo zamu fita" can kasan makoshi Nihal tace, "idan bani da lokaci fa" ta ida zancan tana tsare sultan da ido kauda kai sultan yayi tare da shafa sumar shi setin kunne Nihal sultan ya matso tare da cewa, "doka ce daga yau dole ki rinkayi lokaci na ko kina so ko baki so tunda karkashi na kike" tsare Sultan da ido Nihal tayi tana kallo sannan sultan ya bud'e murfi mota ya shige nad'e hannuwa Nihal tayi a kirji tana zancan zuci, "wai shi wannan mutumin me ya dauke ni, bazanyi lokacin na shi ba ko anayi dole" Nazili dake tsaye cikin shirin ta na zuwa office duk abinda ya faru a kan idanuwan ta ya faru wani dunkulan kunci ne ya rufe ta, da takaici yadda take ganin sultan na rawar kafa kan Nihal, takowa tayi gaban Nihal wadda ta Lula duniyar tunanin har motocin sultan sun bar harabar gidan, murya Nazili ce ta doki dodan kunna Nihal, "Ai se a koma cikin gida tunda ya tafi, ko baki gaji da ganin shi ba, oh ko kuma tunani satar da zaki mashi kike, saboda na san mi ya kawo ki kudi..! shi dama matsiya ci baya taba gajiya da abin duniya," maida gashin kanta baya Nihal tayi tana kokarin wuce Nazili damko hannun Nihal Nazili tayi juyowa Nihal tayi a fusace tare da fisge Hannun ta tace, "wai ke wace irin mata ce me yasa baki gajiya da ihu, bani da lokacin ki ba ko da yaushe nake kula karnika ba idan suna haushi ya kamata ki gane haka..! Daga hannu Nazili tayi zata dauke Nihal da mari rike hannu Nazili Nihal tayi idanuwan ta a kankance tana cewa, "fuska ta ba sa'ar wasan ki bace ko a mafarki karki kara wannan gigin bale a zahiri" Nihal ta watsar da hannu Nazili kasa har tayi gaba ta dawo tace, "tunda na malaki sultan ya kamata kin san cewa na malaki komai na gida nan so ba se na tsaya sata zan sami abinda nake so a wajan miji na ba, ina fatan kin gane" Nihal ta ida zancan tare da nuna Nazili da yatsa ta bar wajan, wata wawiyar ajiyar zuciya Nazili ta saki tana waige ko akwai wanda ya gan su cije yatsa Nazili tayi tana cewa, "sai na lallata fuskar nan se na gwada maki cewa ke ba komai ba ce lokaci yayi da zan nuna maki true colour dina, za ki san ni kike gasawa magana se na koya maki hankali Nazili ta ida zancan tare da shigewa motar.

Koda Nihal ta shige cikin gida ta manta da wata Nazili ta cigaba da sha'anin ta ita da su nawwara dan har yau basu koma school ba, after sun gama lunch suka dunguma zuwa shopping saboda shirye-shiryan komawar su nawwara school kuma yau ake birthday din wata kawar su shiyasa zasu je shopping mom ta basu kudi masu yawa driver ya kai.

Nihal ba karamin dadi ta ji ba a harabar shop right motar driver ta faka Nihal ta sha mamaki ganin garin kano Ashe dama haka waje yake sun shiga shop right sun judo kaya kala-kala har Nihal ta dauwa mom da Ammi da Dara nasu sannan suka dawo gida a gajiye likis part din Ammi suka wuce nan Nihal ta ba Ammi nata tsaraba da Dara sannan ta wuce part din mom ta bar su nawwara suna shirin zuwa birthday.

Mom dake zaune a bedroom badiya na jera mata kaya a wardrobe a hankali aka turo kofar dakin ta Nihal ce ta shigo fuskar ta dauke da fara'a hannu ta na rike da leda turaren data siyawa mom a shop right murmushi mom ta saki tana cewa, "diyar albarka shigo" cikin ladabi Nihal ta shigo tare da gaishe da mom ta amsa tana cewa, "har an dawo kenan" daga kai Nihal tayi tana cewa, "mom kema ga naki tsaraba" washe baki mom tayi tana cewa, "har dani cikin siyaya to na gode, gashi turaran mai kamshi daughter kema kina san kamshi kamar ni" murmushi Nihal tayi tana sinne kai badiya dake jera kaya zubewa tayi tana gaishe da Nihal amsawa tayi tare da amshe kayan da badiya ke jerawa tace, "bari na jera kina iya tafiya," mom tace" "baza ayi haka ba daughter ki barta ta cigaba ke da kika dawo daga kasuwa ya kamata ki huta" shagwabe fuska Nihal tayi tana cewa, "mom ki bari nayi na saba a gida ni nakewa umma na komai bana jin dadi zama bana yin komai, kuma ban gaji ba" Nihal ta ida zancan tana gyarawa mom wardrobe ba yadda mom ta iya haka ta barma Nihal tanayi suna fira har ta gama sannan ta kule wardrobe din tace, "saura me mom?
"ba komai daughter" zama Nihal tayi saman sofa rukwo hannuwan Nihal mom tayi tana cewa, "Allah ya maki albarka Nihal" murmushi Nihal ta saki tana cewa, "amin mom" kiran sallah la'asar ne ya tashi su Nihal alwala Nihal dauro tare da mom suka gabatar da sallah bayan sun idar mom tace ma Nihal bari ta je fada maimartaba ta dawo.

*********
Chapter 87 · 0% Book details