← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 128

Sashe 60

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Misali karfe 7:00pm Nihal ce ke shiryawa cikin uniform din ta black and White skrt black dai-dai gwiwa da white shirt me dogwan hannu sosai kayan sun amshe ta tayi kyau se White hijab shirya tsab Nihal tayi cikin uniform ita kanta ta yaba kyan da uniform din ya mata, sannan Nihal ta fito daga bedroom zaune a parlour ta sami sultan saman kujera, a hankali sultan ya dago yana kallan ta wani irin kyau Nihal din ta mashi se ya ga ta kara zama to young da ita mikawa Sinbul briefcase din shi sultan yayi tare da cewa, "sinbul ka karasamin da briefcase dina cikin mota kafin na fito" to sinbul yace tare da amsa cikin ladabi ya fice sannan sultan ya kalli Nihal alamar su fita a tare suka fito da sultan gwanin ban sha'awa duk wanda ya kalle su se ya kara a haka har suka karasa main parlour lokacin kowa ya halara a dining area har da maimartaba dauke da sallama suka shigo, gabaki daya kallo ya koma kan su Ammi dake zaune ce ta saki murmushi tana cewa, "masha Allah Nihal uniform din nan ya maki kyau sosai Allah ya bada sa'a ya bada abinda aka je nema" gabaki daya yan' dining suka amsa da, "amin! har da Nihal dake jan kujera ta zauna karasowa sultan yayi tare da yima mom pack da Ammi a kumatu da maimartaba murmushi maimartaba yayi tare da cewa, "fushi nake da kai son! zaro ido Sultan yayi tare da langwabe kai yana jan kujera dake kusa da maimartaba, gimbiya jalila da Ashad kallan juna sukayi tare da tabe bakin suna kallan maimartaba, Sultan ne yake cewa, "am sorry Abba wallahi aiki ne ke boye ni shiyasa, insha Allah for now zan rinka kula da mutane na" kallan shi sarki yayi yana cewa, "Sultan ban san ranar da zaka fara shiga mutane ba, yaushe zaka saba dasu har su san cewa kaine shugaban su nan gaba kad'an, ko dai soyayya ce ta boye ka" maimartaba ya ida zancan ya kallan sultan dake yake, gabaki daya dining area kwashewa sukayi da dariya ban da Nazili dake aika wa Nihal da wani irin kallo, wani tunanine ya fado mata a rai lokaci daya, kayatacan murmushi Nazili ta saki tana fatan nasara furzar da iska mai sanyi tayi tana juya spoon din hannu ta sannan ta dauki wayar ta dake kusa da ita message ta Shiga rubutawa cikin dankakanin lokaci ta gama tare da tura shi tana murmushi, har sultan da Nihal suka gama breakfast suka fice, Nazili na zaune a dining cikin zuciyar ta tana cewa, "yau se na batar dake Nihal se na share tarihin ki a zuciyar Sultan se nasa sultan ya tsane ki" Nazili tana zancan zuci tana sakin murmushi, maimartaba ne dake zaune, kallan Nazili yayi tare da cewa, "daughter yau baki zuwa aiki ne? langwabe kai Nazili tayi tare da cewa, "Abba am not feeling much better am sick! shafa kanta Ammi tayi tare da cewa, " sorry my dear you have to take some rest" mom ce ta amshe zancan da cewa, "kin sha magani? girgiza kai Nazili tayi Gimbiya jalila dake gefe tana cin abinci a yangace tace, "Sorry dear" ita da Ashad mikewa Nazili tayi tare da sakarwa maimartaba pack a kumatu da Ammi sannan ta wuce bedroom.

Zagaye daki Nazili keyi tana sakin murmushi murda kofar dakin da akayi ne ya sa Nazili hayewa bed da sauri ta lulube, Aziza ce ta shigo dauke da tray da ruwa se magani mekewa Nazili tayi tare da zabga tsaki tana cewa, "mi ya kawo ki daki na yanzu, bana bukatar ganin kowa idan ina san ganin ki zan nemeki" Nazili ta ida zancan tana amshe tray din hannun Aziza, cikin rawa jiki Aziza tace, "Ammi ce tace a kawo maki magani" harara Nazili ta watsa mata tare da cewa, "naji..! naji..! kina iya fita" jiki a sabule ta bud'e kofa zata fice Nazili tace, "Aziza! juyowa Aziza tayi kai a sunkuye Nazili tace, "ina so ki samin ido a kan abinda ke faruwa main parlour" daga kai Aziza tayi tare da ficewa tana fita Nazili ta janyo wayar ta dake saman bedside drawer kiran wata number ta shigayi bugu daya aka dauka daga dayan bangaran akayi sallamah murmushi Nazili tayi tare da cewa, "Tjee ina fatan ka ga sako na" murmushi Tjee yayi daga dayan bangaran yana cewa, "Gimbiya naga komai amma baki rubuto da suna makarantar ba? Wani malalacin murmushi Nazili ta saki tare da furta, " prime college! Shine suna makarantar TJee ina so kayi min aiki kamar yadda na saka ka! zan baka ko nawa kake bukata tun daga 1 million har 10 million TJee"
"Baki da wata matsala Gimbiya zanyi duk abinda kike bukata amma ki aje min kudi na cas"
"Kai ma kasan kudi ba matsalata bace ni dai fata na kayi min aiki da kyau TJee!
"toh shikenan Gimbiya baki da wata problem a kaina" murmushi Nazili ta saki tare da kashe wayar Hannun ta, tana zagaye daki tana cewa, "yau Nihal na lahira se ya fiki jin dadi se kin dandana bacin ran da kika dade kina dasa min! murmushi Nazili ta kuma saki tana tunanin bakar wahala da Nihal zata sha hannun TJee ta kara tintsirewa da dariyar keta..

```Taku har kullun salma mas'ud nadabo```
[1/7, 2:29 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
*Story*
*And*
*Writing*✍🏾
*By*
*Salma mas'ud nadabo*👑

🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITERS FORUM*🐄
(```We are the best among the rest```)

*Page: 87_88*

Bayan Nihal da Sultan sun gama breakfast books din ta Nihal ta dauka tare da daura white veil din ta, Sultan se kallan ta yake briefcase din shi ya dauka suka fito a tare kasancewar da safe lesson teacher Nihal ke zuwa har suka fito compound idanuwan Sultan na kan Nihal, cikin natsuwa Nihal ta wuce lesson room, Alex dake tsaye kusa da Sultan ya dau 5 minutes yana mashi magana amma kwata-kwata hankali shi na kan Nihal ya tsare ta da ido yana kallan wani saban yanayi game da ita yana shigar shi wanda shi kan shi be san dalilin hakan ba, me yasa ya tsinci kanshi da tana birge shi kadan bada yawa ba, taba shi da Alex yayi ne yasasa dawowa dai-dai shafa sumar kanshi Sultan yayi yana sakin smile tare da mikawa Alex briefcase din shi da sauri ya shige mota ya zauna gidan baya tare da lumshe ido yana tuna moment din shi na jiya da Nihal, a haka motocin shi suka fara barin harabar gidan Alex dake front seat mazauni banza, juyowa yayi yana kallan Sultan yana smile daga mashi gira sultan yayi yace, "what? Dariya Alex yayi tare da cewa, "boss yau na lura kamar kana cikin good mood" murmushi Sultan yayi tare da lumshe ido yana cewa, "wani abu ka gani? aini kullun haka nake, ko kaga wani canji ne? sultan ya ida zancan yana tabe baki girgiza kai Alex yayi yana cewa, "uhm amma kad'an bada yawa ba! dafa goshin shi Sultan yayi yana cewa cikin zuciyar shi what wrong with me maida kanshi Sultan yayi bakin window yana sauke ajiyar zuciya.

Maida hankali Nihal take sosai suna lesson ita da aunty abiola tana kara wayar mata da kai kan karatun ta tare da sheda mata cewa, next week za'a fara JSCE tayi magana da Sultan yace makaranta ze kai ta tayi exam ya kamata ta dage da karatun, to Nihal tace mata sannan suka cigaba da gudanar da lesson din su.
Chapter 60 · 0% Book details