← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 128

Sashe 88

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sara ko taga SAUYIN RAYUWA Ganin zaman ba abinda ze mata yasa Sara shiryawa zuwa gidan tabawa kawar gwoggo tasan zata samu wani abu wajan ta tunda tana siye da shiyarwa, kaitsaye gidan tabawa ta zame Tabawa dake zaune saman kujera tayani gulma ta turo dankwalli gaba tana kasa alalla saidawa ganin Sara ne ya sata had'e rai tamkar bata taba dariya ba tace, "Allah yasa lafiya idan ma zancan kudi ne ya kawo ki Sara gaskiya ki juya, danni bani da su bani da dalilin su, kuma har da laifin ku duk kadara da kuka tara kuna mi ta kare ko da yake sakaya Allah ce ke bibiya ai dama duk abinda ka shuka shi zaka girba sanda indo ke cikin daula ta manta da kowa se da yanzu iftila'i ya hauku kuke neman mutane to ban da su" kuka Sara ta saki tana cewa, "kiyiwa Allah inna ki taimaka gwoggo na can rai hannun Allah ko motsi batayi bani da ko sisi ko abinda zan daga na saida bani da shi, ki taimaka wallahi gwoggo kad'ai ta rage min,"
"Toh da ran hannuna yake ba hannun Allah ba, kin ga malama fita min daga gida kafin laifin da kukayi ya shafe ni, ai kin saba raba shakira ki se ki je ki kasa ayi a biya ki"
"Haba inna dan Allah ki taimaka ko bashi ne ki bani, ina iya rasa gwoggo a halin yanzu" wata uwar ashar tabawa ta sakarwa Sara tace, "ta mutu mana sai me dama duk mai rai mamaci ne..! kiii Tabawa ta ja Sara ta watso ta waje wani irin kuka Sara ta saki tana cewa, "na shiga uku ni Sara ina zan tsoma rayuwa ta Ashe dama haka sakaya Allah take..! babu abinda ya fado mata a rai se san da Nihal ta zo rokwan gwoggo ta taimaka a kai umma asibiti fir taki kuma wannan dalilin shi yayi sanadiyar mutuwar ta itama yau gashi an mata, duniya kenan idan kai ne yau gobe ba kai bane tabas taga yadda sakaya Allah take haka ta ja kafafuwan ta zuwa kauyan su gwoggo ko Allah ze sa a dace ta sha bakar wahala a hanya ga laulayi da kyar ta karasa aiko cikin sa'a ta sami wan gwoggo ze je gona ta zayana mashi abinda ke faruwa, tasha ciwon baki kamar me sannan ya ciro naira dari biyu ya damka mata wadda ko abin hawa tayi da su sai sun kare haka ta yanko jeji ta dawo gida ta cigaba da yima gwoggo magani wanda da kyar take samo masu na sama bakin sallati har gwoggo ta mike sai dai bakin ta ya karka ce gefe guda.

*********

Da yamma likis sultan ya dawo gida ko da ya dawo part na su ya wuce kaitsaye bathroom ya wuce yayi wanka ya fito sanye da towel yana goge jikin shi d'aya, ya shafe jikin shi da lotion sannan ya shirya cikin jeans and black t-shirt me dan karamin hannu ta kama jikin shi yayi kyau sosai sannan ya feshe jikin shi da turare, part din mom ya wuce kaitsaye kafin yaje na Ammi dauke da sallama sultan ya shiga part din mom ganin ba kowa parlour se bayi dake hada-hada, hakan yasa sultan wucewa bedroom din mom a hankali ya murda kofar kwance saman gado ya hango Nihal ta kudindine cikin blanket bayan mom ta fita bacci ya dauke ta, a hankali sultan ya tako bakin gadan ya tsare Nihal da ido yana kallan yadda dake bacci kneel down sultan yayi bakin gadan a hankali sultan ya kai hannun ze shafa saman cheeks din Nihal gyara kwanciya Nihal tayi tare da janyo hannu sultan tayi pillow da shi tana bacci, murmushi sultan yayi yana kallan ta dan ba karamin kyau Nihal ta mashi ba a hankali ya sakar mata kiss a goshi dan motsawa Nihal tayi a hankali ta bud'e idanuwan ta tare da maida su ta lumshe se kuma ta dan bud'e saboda kamshi turaran sultan daya doki hanci ta, a zabure Nihal ta mike tana kallan sultan shima se daya dan zabura saboda yadda Nihal tayi tamkar taga abin tsoro waige-waige Nihal ta shigayi ganin ba mom a dakin cike da masifa tace, "Mi ya kawo ka nan" Nihal ta ida zancan tana tsare sultan da ido shafa sumar kan shi sultan yayi yana wani kill smile nashi yace, "tanbaya ta kike mi ya kawo ni dakin mom? to zan fada maki na zo ganin matata ne..! tunda bata iya tarbar mijin ta ba idan ya dawo daga wajan aiki" galala Nihal ta tsaya tana kallan sultan tare da watsa mashi harara tace, miji..! Na wucin gadi ko, idan mafarki kake ya kamata ka farka, ni fa ka ishe ni da wannan bibini na gaji" sultan yace, "ni kuma yanzu na fara..! ya ida zancan yana hayowa saman gadan ja da baya Nihal tayi tana cewa, "karka kuskura ka matso na fada maka sultan na mana iya ka" har Nihal ta kai karsha gadan ta tafi luuu zata fadi kasa sultan ya taro ta a nanauyar ajiyar zuciya Nihal ta sauke idanuwan ta a ritse tare da kankame rigar sultan daukar ta yayi cak kamar yar baby har lokacin idanuwan ta na rintse murda kofar da akayi ne yasa Nihal ware idanuwan ta mom ce ta shigo zaro ido Nihal tayi da sauri ta duro daga rukwan da sultan ya mata cike da kunyar mom ta fita da gudu daga dakin, gogan na ka kuwa ko a jikin shi girgiza kai mom tayi tare da ja mashi kunne tana cewa, "baka ji kasa min daughter guduwa" yar kara sultan ya saki yana sosa kunne shi zama mom tayi sultan ya daura kan shi saman ciyar mom tana shafa kan shi tana cewa, "ka tada min daughter daga bacci ko, kuma ka zauna min tashi ka bi matar ka" lumshe ido sultan yayi yana cewa, "mom korata kike? yau nan zan zauna" yayi maganar cikin sigar shagwaba lakace mashi hanci mom tayi tana cewa, "Allah ya shirya min kai, shagwaba da kake min ko nawwara bata zaunawa tana min" rungume mom sultan yayi yana cewa, "tabar min shiyasa" murmushi mom ta saki tare da cewa "tashi ka bi matar ka" mikewa sultan yayi yana cewa, "mom ko baki ce ba bin Abita zanyi" pillow mom ta janyo ta bi sultan da shi tana cewa, "duk wata sauran kunyar ka ta fice" da gudu sultan fita yana dariya...

```Taku har kullun salma mas'ud nadabo```
[1/15, 6:58 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
*Story*
*And*
*Writing*✍🏾
*By*
*Salma mas'ud nadabo*👑

🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
(```We are the best among the rest```)

*Page: 107_108*

A kwana a tashi ba wuya wajan Allah yau su nawwara ke hada kaya dan komawa school Nihal kuwa duk jikin ta yayi sanyi ta san za tayi missing nasu ba d'an kadan ba, dama suke debe mata kewa nawwara ce ta shafa kumatu Nihal tana cewa, "Aunty Nihal ko zaki bi mu ne? murmushi Nihal ta saki tana cewa, "ina jin kamar haka zanyi missing na ku sosai" ta ida zancan idanuwan ta cike da kwalla, nawwara ta minal rungume ta sukayi a tare suna cewa, "ki daina damuwa aunty zaki rinka zuwa mana visiting mun san yaya ze kawo mana ke ko Aunty Nihal" daga kai Nihal tayi gabaki daya murmushi suka sakarwa juna su Dara ce ta shigo dakin tana cewa, "Ku fito an gama hada kaya suna compound driver na jiran Ku" a tare suka fito compound har da Ammi, Ammi tace, "iyallan rigima yau za'a tafi Allah ya kiyaye hanya" mom tace "ma huta kwana biyu kafin hutun ya kare" hugging din su mom sukayi suna dariya, minal na kokarin shigewa mota Gimbiya jalila ta jawa minal kunne tana cewa, "bana ce ku biya ta part nawa ba kafin ku wuce" yar kara minal ta saki tana cewa, "sorry Momi na manta ne"
"Hmm ai ke kullun cikin manta uwar kike shashasha" warmer abinci Gimbiya jalila ta mikawa minal tare da yima minal da nawwara pack a kumatu sannan suka shige mota Nihal na masu bye-bye har motar su, ta bar compound sannan ta juyo cikin gida.

*BAYAN KWANA BIYU*

Nihal ce ke shiryawa cikin jeans white and black shirt tayi wani irin kyau gashin kanta ya wani nanad'e ya zubo har gadan bayan ta, murda kofar da akayi ne ya sata juyowa Dara ce ta shigo hannun ta rike da tray na fruit, murmushi Nihal saki tare da karasawa ta amshi tray din hannu Dara, murmushi Dara tayi tana cewa, "nayi tunanin kina part naku Ammi ke ce min kina nan shine nace bari na kawo maki kayan motsa baki,"
"Umma kina ji dani, na gode umma, yanzu na fito daga wanka dama niya ta dana gama shiryawa na je kitchen na taya ki aiki,"
"aiki da wannan kwalliyar wannan gayun na ganin mai gida ne, kuma se a shiga kitchen da shi" murmushi Nihal saki tana cewa, "kin ji ki umma wai kwalliyar gani mai gida, ina so na shiga na daurawa sultan wani abu bana su bayi na mashi girki kamar yadda kike so ke da mom" murmushi Dara tayi tana cewa, "hakan na da kyau akwai dalilin da yasa haka amma nan gaba zaki gane" daukar apple Nihal tayi tana ci tace "yauwa umma bari na nuna maki hotan umma da Abba dama na dade ina so na nuna maki,"
"haka fa dauko na gani, nima ina san gani su tun ba yau ba," da sauri Nihal ta nufi drewar kwalla mata kira da Basmal keyi ne yasa Nihal washe baki tana cewa, "Basmal sun dawo yau kenan" maida drewar Nihal tayi ta kule da sauri tayi waje Dara ta girgiza kai tace "af ta manta ta fice bata dako hotan ba, bari na fita nima wani jukwan na gani"
Chapter 88 · 0% Book details