← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 128

Sashe 22

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin shirin shi Sultan ya fito na Jean's n t-shirt, t-shirt din black me d'an k'aramin hannu jean's blue, ba k'aramin kyau ya zubaba kafar shi na sanye da Booth black, se shek'i yake, direct garden ya wuce, ihu bayi maza ke tashi, iya kar haduwa garden din ya hadu ko ina malale yake da grass carpet, gefe guda kuma swimming pool ne da kujerin shan iska, gefe d'aya kuma kujeri ne na Alfarma, ihu da aka kuma sawane ya janyo hankalin Sultan wajan ya nufa inda fadawa da bayi ke shewa da alamar abinda ake na masu dadi, murmushi Sultan ya saki ganin Ashad ne ke wasa da wuk'a tare da fadawa majiya karfi duk Wanda ya bige se ya fadi ya cinye shi se bayi da fadawa ke shewa, saboda haka aladar wasan yake, suna ganin Sultan suka fara zubewa suna kwasar gaisuwa, hakan ne ya Ankara da Ashad kallo d'aya Ashad yayi ma Sultan ya watsar, gabaki d'aya bayin gurin suka dauka da cewa Sultan ya shigo suyi da Ashad daga masu hannu Sultan yayi yace, to murmushi Ashad ya saki Wanda iyakar shi laban shi, zaro wuka Sultan yayi ya Nufo Ashad yana smile, fara wasan wukar suke cikin k'warewa Wanda Ashad da gaske yake binshi da wuk'ar ganin abin Ashad da gaske ne yasa Sultan wani irin juyi tare da dukan habar Ashad hakoran shi da lips din shi suka hade ya tafi taga-taga Sultan ya kaima k'irjin shi duka da wuka ya fadi k'asa warwas, sultan ya bishi da wuk'a a wuya suna kallan juna ido cikin ido kowana su na maida numfashi murmushi Sultan ya saki irin na rainin wayau yace,"aushh" ya taba gefen bakin Ashad Wanda jini ya fara zuba, ihu fadawa ne ya dawo da su Sultan murmushi Sultan ya saki tare da mik'awa Ashad hannu ya mik'e, bubuga bayan Ashad yayi ya matso dai-dai satin kunnan shi kamar me rad'a yace, "har yanzu da sauran ka, tsakanin ka da *SULTAN SALIM* akwai tazara mai tsaho" sannan Sultan ya biki kafad'ar Ashad yana shu'umin murmushi ya k'ara gaba ya bar Ashad yana binshi da mugun kallo me cike da tsana .

Yau dai Nihal tasha wanki sosai dan kusan se yama likis ta gama tana shanya aka fara kiraye-kirayen sallah magrib, ruwan dauraya ta juye a maguji sannan ta shige dakin su, dakin in ban da wari ba abinda yake da sauri ta k'araso kusa da umma, tausayin umma ne ya kama Nihal da kyar Nihal ta janyo umma waje sannan taja ruwa a rijiya ta juye abokiti tayi ma umma wanka, sannan ta shige dakin su ta gyara shi fes, gurin umma ta dawo ta dafa jikin umma, zafi jikin umma yayi rau sakwamakwan ruwan da gwoggo ta shek'a masu ya haifar wa umma da zazzabi, hakan ne yasa Nihal rudewa tana, cewa umma na zazzabi ke damun ki sannu kin ji da kyar ta ja umma ta maida ta daki, sannan ta debo ruwa tare da b'alo panadol taba umma tare da k'ara tab'a goshin ta tace, "sannu umma na"
sannan Nihal ta fita waje dan dauro alwala.

```Taku har kullun salma mas'ud nadabo```🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
*Story*
*And*
*Writing*✍🏾
*By*
*Salma mas'ud nadabo*👑

🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
(```We are the best among the rest```)

*Page: 43_44*

Daran yau daga umma har Nihal ba Wanda ya rintsa saboda zazzabi dake damun umma a hankali Nihal ta daura kan umma a saman cinyar ta, tana shafa kanta Wanda jikin yayi rau kamar garwashi, wasu hawaye ne ke sulalowa Nihal tana sa bayan hannun ta tana gogewa kwantar da umma tayi ta fita ta debo ruwa ta dawo ta dau zani ta nufo umma tare da maida ta bisa cinyoyin ta tana danna mata ruwan a hankali tana cewa, "umma sannu kin ji Allah ya baki lafiya" se dai umma ta daga kai ita ka d'ai tasan abinda take ji.

Sultan nashiga part nashi wanka ya sake ya fito sanye da bathrobe da dan k'aramin towel yana tsane jikin shi knocking din kofar da a keyi ne yasa shi tsayawa da goge gashi kanshi yana kallan kofar, cikin honey voice din shi Sultan yace, koma waye ya jira ni a parlour na gama shiryawa jin hakan yasa, khalifa tsayawa a parlour tare da zama saman kujera ya b'oye wuk'ar dake hannu shi cikin riga, janyo lotion Sultan yayi ya shafa sannan ya bude wardrobe ya curo fara jalabiya me kyau ya saka masha Allah tuni kyan Sultan ya fito, yayi kyau kamar balarabe sannan ya feshe jikin shi da turare a hankali ya bude handle din kofar daki tun da ya hango khalifa yake sakin murmushi tare da k'arasowa cikin takun shi na mulki hannu wanshi na hard'e a baya, da sauri khalifa ya mik'e kan shi a k'asa yace, "Ranka yadade barka da wannan dare dama na zo na taya ka hira ne,"
Murmushi Sultan ya saki yana bin khalifa da kallo yace, "amma fa ka kyauta khalifa, se dai kuma kash main parlour zani dinner yau sweetheart tasa an dafa min favorite food dina, ko zamu je tare muyi dinner tare? Murmushi khalifa ya saki yace, " ranka yadade ban dade da cin abinci ba na gode da tayin ka, Allah ya k'ara maka tsawan cin rai," gajeran murmushi Sultan ya saki yana kallan khalifa yace, "mu tafi ko" Sultan na gaba Khalifa na baya zaro wuk'ar yayi har ya d'aga ze cakawa Sultan wuk'ar ya ga alamar ze juyo se ya maida wuk'ar yana maida dawa Sultan ya juyo yana murmushi ya matso kusa da khalifa kamar me rad'a ya rungume shi tsam a jikin shi yace, "a duk inda kake ka iya takun ka, saboda mak'iya na zagaye da kai , so dayawo ana kashe mutum ta hanyar Wanda ya yadda da shi, amma ka sani mutane da yawa nayi ma kallan biri kai kuma kanayi masu na ayaba shiyasa nake san ka, kasancewar ka jarumi, " Sultan ya shafa k'ungu shi yace yana sakin murmushi, "saboda kullun kana yawo da makamin saboda mak'iya idan nine kai da mindiga zanyi yawo" wani irin miyau khalifa ya had'iya me d'aci, take a nan jikin shi ya fara rawa, amma se yayi ta maza ya daure yana murmushi yak'e, Sultan ya katse shi da cewa, "idan mak'iyin ka ya shigo gidan ka idan kai ne mi zaka mashi,? baki khalifa na rawa yace, "kashe shi zanyi" dariya Sultan yayi yace, "Ni bana kashe mak'iyi a ranar farko se a rana ta biyu" sannan Sultan ya kakab'e rigar khalifa yana shu'umin murmushi yace, "muna iya tafiya" jiki a sab'ule khalifa ya fito duk se ya ji ya tsani kanshi.

Direct main parlour Sultan ya wuce lokaci kowa ya halara a dining area shi kad'ai ake jira, dauke da sallama a bakin shi ya shigo Gimbiya jalila dake zaune sai da tasha jinin jiki ta, tana bin Sultan da kallo Jan kujera yayi tare da zama kusa da ammi yana murmushi yace, "ya dai matar na ga duk kin wani bi kin tsure ko tsoran kar na ce ki sha maganine," yana maganar yana kallan Gimbiya jalila ko ba'a fad'a mata ba tasan wannan magana da biyu akayi ta an jefi akuyar kishiya, murmushi maimartaba yayi yace, "Ku dai baku gajiya kai da ammi," murmushi ammi tayi tana jawa Sultan kumatu tace, "wannan bokan turan wallahi ya ishe ni," basmal tace, "mu dai bamu shiga tsakanin Ku, ka shiga kasha kunya" tana maganar tana saving din Sultan waina da biyar taushe wadda taji yan'ciki da kaji da naman rago ga man shanu ya ji, tun kafin ta ajewa Sultan ya fara lashe baki yana cewa, "sweetheart wannan shagalin duk ni ka d'ai gaskiya zan baki tokwici," murmushi basmal ta saki tana aje mashi plate din, Nazili da mom suka hada baki wajan cewa wannan abun har da San kai shine kika wareshi shi kad'ai kika mashi wannan shagalin ko," Nasim yace, "nima yaya zanci" minal tace, "nima" ita da shukura suka had'a baki wajan fad'i dariya Basmal tayi tana cewa, "ai shi yayana be san cin abinci shiyasa na yi mashi favorite nashi ko ya samu ya ci," Ashad dake gefe sai aika masu da harara yake da ya sannan da wannan abinci da guba ze sa mashi ko shinkafar b'era yaci ya mutu, a haka suka gama dinner din wasu na farin ciki wasu zuciya cike da mugunta.

Bayan sun gama dinner Sultan ya ruk'o hannu ammi suna tafiya suna tab'a hira har suka k'araso dakin ta ta zauna saman sofa tana cewa, "Sultan wai yaushe ne zaka kayi aure ka ga mun zuba maka idanuwa amma har yanzu shuru, naga alamar ma maimartaba be damu da zancan kayi aure ba ya zuba maka na mujiya, hade rai Sultan yayi tare da daura kan shi saman cinyar ammi yana cewa, " shi fa aure lokaci ne ni har yanzu ban samu wadda ta kwanta min a rai ba," ture shi ammi ta shiga daga cinyar ta tana cewa, "kai kullun aka yima maganar aure se ka hau wa mutane wasu jawabi, ko dai baka da lafiya ne? dariya Sultan ya saki yana Jan bedside drawer yana cewa, "lafiya ta lau ammi garas nake lokaci dai nake jira" yana maganar yana balo mata magani, duka ammi da kai mashi ya goce tana cewa, "ja'iri indai da gaske kake mu gani a k'asa," to Sultan yace yana mik'a mata glass cup ta amshi glass cup din ta kora magani, Sultan yayi kissing goshin ta yace, "matar Allah ya baki lafiya" tace, "ameen," sannan ya fito. direct part nashi ya wuce yana shiga bedroom ya iske night dress din shi saman bed zurawa kawai yayi ya fad'a bed yana tunanin maganar da ammi ta mashi, shi kan shi be samu peace of mind ba yama za'ayi yayi aure, shi kwata-kwata aure baya gaban shi ma yanzu hasali ma mata haushi suke bashi tunda Asiya taci amanar shi, aka had'a baki da ita wajan kashe shi, watsar da zancan yayi bacci me dadi yayi awangaba da shi.
Chapter 22 · 0% Book details