Sashe 97
Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Nasan cewa duk halin da ake ciki yanzu na san kowa ya kwanta ina so a aiwatar da abinda na uwarce ko dai-dai, bana so a samu matsala"
"Ran ki yadade baza'a samu wata matsala ba, sai ma dinbin sara Gimbiya"
"Da kyau kina iya tafiya, idan kun gama aiki kudin ku na jiran ku" Nazili na gama fadin haka Aziza ta fice, Nazili ta cigaba da zancan zuci, "yau zan nuna maki wacece Nazili ba dai fuskar nan taki yake kallo ba, har baya gani kyan tawa fuskar baya gani na saboda kyanki ya rufe mashi ido, ya kusa daina marmarin ganin ta, Allah sarki *Sultan salim* zaka sha mamaki idan ka dawo ka ga fuskar hayaty se ka razana, daga lokaci ni kuma tawa tutar zata daga zan zama cikakiyar Gimbiya, sultan nawa ne ni kadai..! ya zama dole a kira ni da Gimbiya ma'ana matar sarki ba matar matsiyaci ba dan tallaka" dariya Nazili ta saki ta haye bed tana cewa, "gida ya kusa gwarayewa da ihu da kuka saura kiris zuciya ta ta cika fal da farin ciki"
Nihal dake kwance tayi nisan bacci cikin bacci ta fara jin motsi kamar a bisa kanta kafi tayi wani yunkuri an manna mata handkerchief a hanci sai mutsu-mutsu take ta kasa kwace kanta har se da ta daina motsi, Aziza tayi ma fadawan dake kusa da ita alama da ido daukar Nihal cak sukayi suka fitar da ita daga cikin daki, wani daki suka kaita na cikin gidan, wanda ko ba'a fada maka ba kasan ya dade dakin dan ba komai cikinsa se komutsai da yanar gizo-gizo, a hankali Nihal ta bude ido tana bin dakin da kallo tace, "ina ne nan, mi ya kawo ni nan,? turo kofar da akayi ne yasa Nihal mikewa cikin kidima da rudewa tana kallan bayi mata guda biyu da suka shigo fuskar su rufe cikin wani yaddi idan ka kura masu ido zaka iya gane su nufo Nihal sukayi bakin ta na rawa tace, "Mi nayi maku ku fitar dani daga nan dan Allah, karku matso kusa dani" duk abinda Nihal ta rarumo sai ta jefa masu su kau ce tana ja da baya fisgo mata gashi sukayi daya ta dauke ta da mari ji kake tas, tas, ririke Nihal sukayi tana kokarin kwance kanta suka manna ta a bango suka matse ta jikin bango ta yadda bata iya kwace kanta, Aziza ce ta shigo ta dangwalo wuta a icce fuskar ta a rufe ta nufo Nihal girgiza kai Nihal take tana cewa, "karku cutar dani dan Allah..! Dariya Aziza ta saki tana nufo fuskar Nihal da wuta zafi daya ziyarci Nihal da radadi ne yasa Nihal daga murya tace, Sultan...! Da karfi Gabaki daya gidan sai daya gauraye da ihu da Nihal ta saki, ta fadi sumama da sauri su Aziza suka shige dakin dake kusa da dakin da Nihal take suka kule, kafin kace mi gidan ya gauraye da ihu Nihal mom dake part din maimartaba kwance mikewa zaune tayi tana cewa, "Nihal..! A tare suka mike da maimartaba sleep robe din ta kwai ta daura saman rigar bacci ta suka fito a tare sinbul da tunda ya ji ihun ya nufi inda ya ji ihu kofar dakin bude ya same ta wuta na ci kama baki sinbul yayi yana cewa, "ya sallam..! can yashe ya hango Nihal cikin wuta sume da sauri ya karasa gaban ta ganin fuskar ta kone tayi shawur da ita jikin shi ya dau rawar da kyar ya iya daukar ta ya fito da ita gabaki daya yan gida na compound har da Adda da waziri suna kokarin nufo daki Sinbul ya fito da ita da sauri mom ta karasa ita da Adda suna cewa, "Mi ya same ta? Abinda suka ganine ya sasu ja da baya rike da baki mom tace, "innalillahi wa'inna'ilai raju'un "me nake gani haka me ya sami fuskar ta, waya aikata mata haka Abba sultan? mom ta fada tana sakin kuka Ammi da jiri ya fara dibar ta luuu ta tafi Ammar ya taro ta yana cewa "Ammi..! Ammi..! Daukar ta yayi cak ya shige da ita ciki Basmal ta bi bayan shi da Adda Sinbul shima ciki yayi da Nihal gidan gabaki daya ya rud'e sai kuka dake tashi Nazili na gefe tana murmushi tana zancan zuci ai konewar da fuskar tayi hakan be mata ba tunda ba konewa kurumus tayi ba, doctor Amir maimartaba ya kira ya duba Nihal ko a wuce da ita asibiti Ammar kuma na duba Ammi Gimbiya jalila ko abin dariya yaso bata dan basu ji komai ba saura su ji mutuwar sultan se gidan ya kara cakudewa a cigaba da kuka na tsawan kwana uku, Ashad dake gefe mamaki ne ya lullube shi lallai gidan nan akwai mugaye basu kadai bane akwai wasu kenan shi daya ke tunanin sultan na mutuwa ya lallaba ya aure Nihal din shine se aka samu munafukin daya kona mata fuska, ya san bame aikata haka ze Nazili yariyar nan itama A ce wallahi.
Amir dressing yayi ma Nihal ya rufe mata fuska gabaki daya idanuwan tane kawai bud'e ya daura mata drip shi kan shi abinda ya gani ya girgiza shi, ya sultan ze ji idan ya dawo ko ya ji labari wai shi me yasa komai nashi se an bata mashi Allah ya kare shi ya tsare yana fitowa daga daki maimartaba da mom suka ce, "ya jikin nata?
"da sauki amma zatayi kwana biyu da dressing a fuskar ta ranar Monday zan zo na cire mata dan abin ya zo da sauki turirin wutar ne ya taba ta, inda wutar tataba ta bashi da wani yawa a fuskar se dai turirin wutar yayi mata ila, idan har magani dana shafa mata beyi ba se an fidda ta waje kuyi fatan Allah yasa kunar bata taba cikin fatar ta ba," kuka mom ta saki tana cewa, "wannan wace irin rayuwa ce dubi yadda yariyar mutane ta koma saboda sultan, wai yaushe ne d'a na ze samu natsuwa? na gaji da wannan cutarwar da ake mashi daga shi har matar shi ba'a kyale ba har yau ba'a taba kama ko mutun daya ba dake da sahannu a cikin abubuwan dake farwa ba daya baya daya, na gaji da wannan rayuwar dan inayin shuru shiyasa har yau aka kasa gano masu laifi Abba sultan, tun yana karamin yaro yake shan wahala kana tunanin hakan namin dadi ne kowa ce uwa zata so ace d'an ta na da natsuwa da kwanciyar hankali amma ban da nawa d'an toh hakan ya fara isa ta kar asa na fara zargi cikin gidan nan ake so a ga baya d'a na da matar sa, to wannan karan bazan dauka ba" kokarin janyo ta jikin shi maimartaba yake mom ta kwace tana cewa, "bazan kara saurara ka ba sai ka ganu min wayanda ke kokarin rabani da dana da suruka ta, ida ba haka ba zaka fara ganin dayan hukunci dan allura zata tonu galma" Mom ta ida zancan tana kallan Gimbiya jalila tare da ficewa fuuu, ruwan jini jikin ta Gimbiya jalila tasha me wannan matar take nufi kar ace fa ta san makircin su, amma hakan be hana ta sakin malallacin murmushi ba sannan ta juyo kan maimartaba dake kokarin bin mom ta tari numfashin shi da kar ya bita ta burbusa mashi wani labari musanman da ran ta ke bace tace, "karka bi ta tashin hankali ne ya mata yawwa, nasan bata bukatar kowa kusa da ita, tana bukatar samun space zuwan ka ba abinda ze haifar se wani zafin" Gimbiya jalila ta ida zancan tana rungume maimartaba ta cigaba da cewa, "wannan abu dake faruwa ba ita kadai ya shafa ba har muma ya shafa muna jin zafin shi" Gimbiya jalila ta ida zancan cike da munafirci har da kwalla maimartaba na lallashin ta fitowar Ammar daga dakin Ammi ne ya sasu dunguma suka shiga dan duba ta Adda da waziri kuwa sai tausaya Masu suke musanman Adda da Nihal tayi mata tsaye a zuciya wannan wani irin mugun abu ne, wannan dalilin ne ya hana kowa na gidan rintsewa Nazili da Aziza ne kawai sukayi bacci se Gimbiya jalila, Ashad kuwa ya kasa rintsawa saboda tunanin wani hali su frank ke ciki bunu-bunu ya duba wayar shi.
*****
A hankali sultan ya bude ido yana bin dakin da kallo yana ganin biji-biji maida ido yayi ya lumshe Nihal ce ta fado mashi a rai da sauri ya bud'e ido herry dake zaune yana jinyar sultan ne ya mike cike da farin cikin ganin sultan ya bud'e ido yana yunkurin ta shi da sauri ya fita dan kira doctor ya zo duba shi, sultan kuwa yana tashi zaune kokarin cire drip din Hannun shi yake dan Nigeria yake so ya koma dan gabaki daya zuciyar shi na tunani wani hali Nihal zata shiga, har ya cire drip din ze taka wata yar kara ya saki saboda fama kafar shi dayayi dan kwata-kwata ya manta da Harbin da yasha a kafa komawa yayi ya zauna yana maida numfashin lokaci yayi dai-dai da shigowar doctor da sauri ya karaso yana cewa, "sultan what are you doing like that" maida shi herry da doctor sukayi saman gado suka maida mashi drip din cikin sanyi murya sultan yace, "I can't stay here anymore..! I have to leave, please let me leave i need to go back Nigeria let me be doctor, am fine just leave me alone" sultan ya ida zancan yana kokarin kara banbare drip doctor yace, "sultan you are not feeling much better you have to stay here" a haka ya lallaba yayi ma sultan allura bacci a hankali bacci ya fara dauke sultan yana surutai furzar da isa me zafi doctor yayi yana kallan herry yace, "mr President must no abut this issue, you have to call him before sultan wake up,"
"I will doctor" sannan doctor ya fita be zame ko ina ba se dakin Alex wanda har yanzu a Como yake injinane kawai ke aiki a jikin shi babu abinda ke motsi a jikin shi sai kayan aiki da suke nuna alamar yana da rai, Haka doctor ya gama dube-dube shi sannan yayi mashi allura a jijiya.