← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 128

Sashe 65

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Nihal ce zaune saman sofa tana sanye da pink sleeping dress din ta wando da riga mai dogwan hannu tana duba books din ta murda kofar da akayi ne yasa Nihal dago da idanuwan ta sultan ne sanye cikin night dress dark blue wando da riga kallo daya Nihal ta mashi ta kauda Kai saboda haushin sultan yake bata, saboda ta san a kan shi Nazili ke gasa mata magana akan mutumin dako damuwa bayi da ita ba, d'an siriri tsaki Nihal ta saki a zuciyar ta bata San ya fito fili ba sultan dake tsaye gaban dressing mirror can kasan makoshi sultan yace, "dawa kike? Galala Nihal tayi tana kallan sultan tana mamakin da yaushe ya jita shuru Nihal tayi tare da daukar books din ta tana ajewa a drawer dagowar da zatayi taga mutum tsaye a kanta had'e rai Nihal tayi tana kallan sultan shima sultan ranshi a had'e babu alamar wasa yace, "dawa kike? shuru Nihal tayi a karo na biyu takowa sultan yayi daf da ita matsawa Nihal tayi Sultan ya kara biyo ta har se da ya manna ta a bango had'e rai Nihal tayi cike da tsiwa tace, "wai me haka Sultan? ka matsamin na wuce," Nihal ta ida zancan a tsawace tsare ta da ido sultan yayi yana kallan lips din ta kamar me neman wani Abu, raraba hannuwan shi sultan yayi jiki bango yayi ma Nihal runfa har suna jin saukar numfashin juna su sultan yace, "idan naki fa what can you do hum? Are you going to beat me up or what! Nihal ce ta kara tsinkewa da lamarin sultan, tsare Nihal da ido Sultan yayi ba alamar wasa a face na shi, duk da zuciyar Nihal na dukan uku-uku saboda kwarjinin da Sultan ya ke mata hakan be hana Nihal had'e rai ba tana kokarin ture hannuwan sultan ta wuce ba, janyo ta sultan yayi ya Kara manna ta bango wata yar kara Nihal ta saki saboda matse mata hannu da Sultan yayi da hannun shi ya kara matsowa kamar ya shige cikin jikin ta rintse idanuwa Nihal tayi jikin ta na rawa tare da cewa, "Dan Allah kayi hakuri bada kai nake ba fa, wallahi ban masan tsakin ya fito ba dan Allah ka bani guri na wuce, bacci nake ji" had'e rai sultan yayi yace, "yau nan zamu kwana! zaro ido Nihal tayi tare da kallan sultan idanuwan ta waje tana kallan sultan dake kallan ta tsaki sultan ya saki tare da barin Nihal tsaye kamar gunki sauke ajiyar zuciya Nihal tayi tare da cewa mugu a zuciyar ta, saman bed sultan ya haye tare da kashe light din dakin gabaki daya zancan zuci Nihal ta shigayi tana cewa, "dan mugun Abu har da kashe min haske ban gama shiryawa ba to bazan ce ka kunna min ba, dana ce ka kunna min Kara na mutu, bin bango Nihal ta shiga yi tana neman haskyan dakin a hankali gashi dakin yayi duhu sosai tuntube Nihal tayi kanta ya daki center table Kara Nihal ta saki tare da fashewa da kuka saboda zafin da ya ziyarci goshin ta, a hankali sultan ya bud'e lumsasun idanuwan shi yana jin kukan Nihal har cikin ran shi duk yadda ya so yayi banza da ita ya kasa can kasan makoshi Sultan yace, "what's this Nihal you know I hate distraction! bayan kin ce kina jin bacci me na damuna kuma yanzu" Banza da shi Nihal tayi ta cigaba da sakin kuka kamar ma zuga ta Sultan yayi lumshe ido sultan yayi jin ba zai iya jurewa kukan da Nihal take ba ya tashi zaune tare da zame blanket din dake jikin shi ya kunna haskyan daki, duke a kasa ya hango Nihal tafe da goshi tana kuka zuba mata ido yayi yana kallo kana yace cikin calm tune, "what's wrong with you? dago da jajayan idanuwan ta Nihal tayi tare da fashewa da kuka, a hankali sultan ya sako daga saman bed cikin natsuwa ya karaso gaban Nihal tare da dukawa ya zame Hannun ta dake saman goshi ta ganin yadda goshin ta lokaci daya ya kunbura yayi ja yasa sultan rintse ido, bedside drawer ya bude ya ciro magani a dan tufu ya matso kusa da Nihal ya matsa maganin a Hannu shi bismillah sultan yayi yana kokarin daura Hannun shi saman goshin Nihal, ja baya Nihal tayi tare da cewa, "lafiya! karka tabani na fada ma" Nihal ta ida zancan tare da dunkulewa waje daya tana kuka tana jan majina, Kauda Kai Sultan yayi tare da kara matsowa kusa da Nihal dan bashi da lokacin musayar yawu da ita dan ya lura ta fara rai na shi, a hankali ya daura hannun shi saman goshin Nihal yana murza mata wata yar kara Nihal ta saki sakwamakwan wani irin zafi ne daya karu a goshin ta bata san lokaci data shige jikin sultan ba ta kara rushewa da kuka cikin shashekar kuka take cewa, "da zafi ka kyale ni please! hura Mata iskar bakin shi sultan ya shigayi me sanyi tare da cewa kamar me rada dai-dai setin kunnan Nihal yace, "ki bari na murza maki kin ji idan ya kai gobe kunbura zeyi sosai" dakyar Nihal ta iya daga mashi kai ta zame taga jikin shi murza mata goshin yayi karo na biyu kara Nihal ta kuma saki tare da shigewa jikin sultan ta cikwikwiye mashi night dress din shi hura mata iskar bakin shi sultan yake yana murza mata a hankali, cikin dankankanin lokaci baccin wahala yayi awan gaba da Nihal, tsare ta da ido sultan yayi yana kallo yadda ta lafe a chest din shi, a hankali ya dauke ta kamar baby ya shifid'e ta saman bed tare da gyara mata kwanciya ya ja mata blanket, tsare ta sultan yayi da ido yana kallo a hankali ya daura hannun shi saman kanta tare da matsar da gashin kanta daya rufe mata fuska a hankali ya furta "Nihal! cikin calm tune sannan ya mike a warwaran Hannun Nihal ne ya Kama rigar sultan juyowa Sultan yayi tare da dukowa yana cire awarawaran gyara kwanciya Nihal tayi tana facing Sultan tare da kama hannu shi tayi pillow da shi ta kankame hannu sosai sultan ya dau kusan 30 minutes duke yana kallan yadda Nihal ke bacci ga hannun shi da Nihal ta kankame kamar za'a kwace mata shi juyawar da tayi ne yasa Sultan zame hannun shi ya koma sama sofa ya kwanta ya dade yana juyi ya rasa meke damun shi kwana nan wani abu na tokare mashi zuciya da kyar ya samu bacci barawo ya sace shi.

*WASHE GARI*
Chapter 65 · 0% Book details