Sashe 37
Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
A parlour ya ci karo da Nihal tana kallo tana ganin Sultan ta mik'e da Sauri zata shige d'aki, fisgo ta Sultan yayi har kan ta ya daki fafad'an kirjin shi gashin kanta ya gogi fuskar shi har yana k'ok'arin shige mashi baki matsar da gashi sultan yayi ga wani kamshi ta daya mamaye mashi hanci lokaci daya, ture ta Sultan yayi daga k'irjin shi, tafiya Nihal tayi taga-taga zata fad'i Sultan ya k'ara matse lalausan hannun ta kamar audiga, wata yar k'ara Nihal ta saki tare da rintse idanuwan ta, kafe ta Sultan yayi da idanuwa yana kallan ta be ma San yana yi ba of coz he can't resist to stop looking at her natural beauty face, jin shuru yasa Nihal ware manyan idanuwan ta tare da sauke su kan kyakyawar fuskar Sultan ture ta Sultan yayi da k'arfi, tare da gyara suit d'in shi, fad'awa saman kujera Nihal tayi idanuwan ta taf da kwalla tana sauke ajiyar zuciya, juya mata baya Sultan yayi tare da zuba hannuwashi cikin aljihu yace cikin honey voice d'in shi , "ina me baki shawara tun wuri ki cewa Ammi baki so na, baki yadda da wannan auran ba, ko kuma ki fad'a min nawa aka biya ki ! kika shigo rayuwar Sultan tun daga naira d'aya har zuwa billion ki fad'a min ni kuma na maki alk'awari zan baki, kwata-kwata baki dace da Sultan ba ya kamata ki San da haka, ga cheak nan zan baki na naira million 10k idan be maki ba ki fad'a min na k'ara maki, na baki nan da yamma ina so ki had'a ina ki ina ki kisan inda dare ya maki" sannan Sultan ya watsa mata cheak d'in kud'in ya fice, kuka Nihal ta saki tare yayaga cheak d'in da Sultan ya bata, ta shige daki da gudu jikin jakadiya ta fad'a dake jera mata kaya a drawer, juyo da ita Dara tayi suna facing juna a hankali ta zauna da Nihal saman gado, jin kukan Nihal take har cikin zuciyar ta a hankali Nihal ta daura kanta saman kafad'ar Dara tana cigaba da kuka ita kanta Nihal bata San me yasa take jin Dara kamar umma ta ba shafa bayan ta Dara take. A hankali tana sauke ajiyar zuciya tana jan majina kamar me mura, Dara ce tace, " ki k'ara hakuri da Sultan kin ji, nasan bame b'ata maki rai a wannan lokacin se Sultan tunda shi kad'ai ya shigo part d'in nan, duk wannan abun da Sultan ke maki na d'an lokaci ne Nihal, jiki na na bani auran nan Alheri ne kuma ki duba ki gani Sultan be da wata makusa yana da halaya masu kyau kowace uwa ta gari zata so ce yarta ta Sultan ze aura, shiyasa nafi kowa yi maki sha'awar na ga kin zama matar Sultan ina nan dake wata rana se kin bani labarin kulawa da Sultan ke baki, na san cewa yanzu ba lalai ki fahimci abinda nake fad'a maki ba Amma nan gaba zaki gane" kawai saurara Dara Nihal take Dan zuciyar ta ta fara raya mata ta gudu kamar yadda Sultan d'in ya buk'ata Amma ta gudu ina zata shine tunanin da take, lumshe idanuwa tayi, ta cigaba da tunani shin ta gudu ta kyautawa Ammi kuwa, murmushi Dara tayi tare da shafa kan Nihal tace, "Nihal karkiyi tunani Mara kyau saboda abin Sultan ya maki kin ji Sultana, kada kiyi k'ok'arin barin gidan nan ko dan ni, saboda inajin wani Abu game dake Nihal wadda har yau kasa gane me dalilin hakan, na rasa mi ya sami kwakwalwata bata tuna baya" hawayan dake mak'ale a idanuwan ta Dara ta goge tare da saurin tashi ta bar dakin, Nihal ko bin ta tayi da idanuwa tare da cewa, ya akayi ta gane tunanin da nakeyi kenan, gyara zama Nihal tayi tare da ware idanuwan ta yaya ne ya fad'u mata a rai Allah sarki shi ka d'ai ne ke gwada mata soyayya a duniya bayan umma da Abba se yaya se Ammi da Dara Wayan da suka shigo rayuwar ta yanzu, wai yaushe ne zata samu *SAUYIN RAYUWA* ne lumshe idanuwan Nihal tayi tare da kwaciya ta watsar da tunani dake damun ta.
Sultan ne zaune cikin office ya lumashe idanuwan shi yana juya kujera a hankali, a zuciyar kuwa fata yake kafin ya koma gida Nihal ta tafi, dan shi kwata-kwata by know love doesn't exist in his dictionary, knocking d'in kofar da akayi ne yasa Sultan cewa, "come in" cikin calm tune har a lokacin idanuwan shi a lumashe, Ammar ne ya shigo hannu shi dauke da file kallan Sultan yayi Wanda har a lokacin idanuwan shi na lumshe suke, zama Ammar yayi tare da gyaran murya yace, "Sultan! Cikin calm tune d'in shi ya cigaba da cewa, "haba Sultan mun riga da munyi maganar nan jiya be kamata yau na gan ka cikin damuwa ba ya kamata ka rage to much of thinking nasan Ammi baza ta tab'a ma zab'in mara kyau ba, jiki na na bani cewa zab'in nan Alheri ne ya kamata ka daina maido hannun agogo baya abinda ya wuce ya wuce Sultan nasan kana jin tsora kar a kuma yin na Asiya I don't think wannan haka take please ka daina haka mana" A hankali Sultan ya ware lumsasun idanuwan shi ya zubawa Ammar su kamar TV yana kallan sa yace, " Ni fa kwata-kwata yarinyar nan bana san ta, ban san mi ya rufe wa Ammi ido ba, ko ra'ayi na bata tanbaya ba kan yarinyar nan, ina tunanin ko 17 year bata kai ba mtsww,"
"Kayi hakuri Sultan kowa na duniyar nan hakuri yake ni kai na hakuri nake dan ji nake kamar duniyar ta min nauyi" galala Sultan ke kallan shi yace, "Dama kana da wata damuwa ka kasa fad'a min!
" ya za'ayi na fad'a ma bayan ga taka damuwar please ka daina tunani, yanzu dai ka tashi muje muyi lunch dan har na fara jin yunwa"
"Bana ci na koshi, saboda bani da matsayi a wajan ka har Abu na damun ka kakasa fad'a min"
"Ya hakaru Sultan ban San tadama hankali ne kuma nayi promise da mun gama lunch zan fad'a ma"
Harara Sultan ya watsawa Ammar tare da cewa, " sarkin ci" a tare suka fice da Sultan yana kunbure-kunbure kamar ka ce kule yace cas.
"Gimbiya Nifa k'inshin-k'inshin nake ji Sultan ze yi aure," date k'arjin ta Gimbiya jalila tayi tare da cewa, "au mi? Anya kunnan ki dai-dai ya ji kuwa yakumbo?
" Wallahi Gimbiya jiya da kunne na naji se dai ban tabatar ba kamar ma basan auran yake ba Ammi ce zata lik'a mashi wata ya aura"
"Kinga wannan jarababa tsohuwar ni ina k'ok'arin kawar da shi ita kuma tana k'ok'arin yi mashi aure ya Tara zuri'a kenan! Bari naje part d'in Ammin na gani da idanuwa.
Alkyabba kawai Gimbiya jalila ta zura tare wuce wa part d'in umman Sultan dan tasan wajan ta kad'ai zata ji yadda zancan yake, dauke da sallama a bakin ta ta shigo, Gimbiya Nadiya na zaune saman kujera ana mata massage, murmushi mom ta saki ganin Gimbiya jalili tare da yi mata nunu da mazauni, tsayawa Gimbiya jalila tayi har se da yakumbo ta kakab'e mata wajan sannan ta zauna girgiza kai mom tayi tana mamakin rashin yadda na jalila, maganar Gimbiya jalila ce ta katse mata tunani da cewa, "Haba umma Sultan ban tab'a tunani haka ba," karkato hankalin ta mom tayi kan Gimbiya jalila tare da yima bayin d'akin Alamar su fita, yakumbo ko ji tayi kamar ta kifawa mom mari dan ta so ayi komai a gaban idanuwan ta, Gimbiya jalila ta cigaba da cewa, "Ashe dama irin zaman da muke kenan a ce abin Arziki ya sami Sultan se dai naji labari a wajan bayi na, ace me jiran gado zeyi aure bani da labari, ko da yake aini ban kai matsayin uwa a gare shi ba" Gimbiya jalila ta ida zancan tana matsar kwalla, duk mom se ta ji ba dad'i kuma haka ba laifin ta bane laifin Ammi ne tayi tunani tun ranar da aka kawo mata Nihal ranar an kai ta wajan momi, mom ce tace, "kiyi hakuri Gimbiya nayi tunanin an kai maki ita tunda nima Ammi ce ta aiko min da ita saboda zab'in Ammi ce, kuma yarinyar mai hankali se dai muce Allah ya tabatar da Alheri dan Sultan yayi sa'a" wata uwar harara Gimbiya jalila ta makawa mom bata lura ba sannan ta mik'e tana cewa, "bari na je na ga suruka tawa to" tana maganar tana washe hakoran munafirci, mom tace, da kinyi zaman ki se a kira maki ita "
"Ba komai bari na k'arasa d'in" sannan Gimbiya jalila ta fita tana maimaita maganar da mom tayi tare da Jan d'an siririn tsaki.