← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 128

Sashe 56

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sallama da akeyi ne yasa gwoggo gyara dankwali dake kanta cike da fargaba ta amsa ganin su aunty Aishe ne se da tasha ruwan jinin jikin ta had'e rai tayi tana cewa, "Ku shigo Ku shigo! aunty Aisha se leke take taga ta ina Nihal zata fito ita da baba sani da Ahmad dan baba sani, dake bayan su har suka karasa dakin baki suka zauna debo masu ruwa a randa gwoggo tayi tana mai cewa, "sannu Ku da zuwa ya hanya?
"Alhamdulillah gwoggo" aunty Aisha ta fad'a tana mai cigaba da cewa, "se kika ganmu kwatsam ba sanarwa" gaban gwoggo ne ya kara yankewa ya fad'i tana raraba ido tace, "aiko dai" aunty Aisha ta katse mata tunanin da cewa, "Ina Nihal d'in tun dazu nake ta faman raraba ido ko zan ganta ko tana makaranta ne? aunty Aisha ta ida zancan tana tsare gwoggo da ido, had'e rai gwoggo tayi tare da zayana masu karya da gaskiya ta ida zancan da cewa, "yau kimanin shekara daya kenan raban dana sa Nihal a idanuwa na, ta fitsare kafafuwanta ta shiga duniya," aunty Aisha ce ta mike tsaye dafe da kirjin ta tana cewa, "wallahi karya ne Nihal bazata taba aikata haka ba, se dai ki ce kun musguna mata har ta guda na san d'iyar hansatu baza ta taba aika ta haka ba, wannan shari ne wallahi" mikewa gwoggo tayi tsaye tana kallan aunty Aisha shekeke tace, "A haye Ashe har wata sheda Nihal zaki iyayi, to Alhamdulillah a hannu na ta tashi Nina santa tunda ko uwar tata tun daga wayan Nihal har ta mutu a nad'e take, bale ke uwar gulma da kicifi zaki gayamin kabali da ba'adi , zanyiwa Nihal Shari ne ko mi? Idan baki sani ba yau kin sani watsatsace" dadagewa aunty Aisha tayi ta dauke gwoggo da mari tana huci baba sani ya rike aunty Aisha cike da masifa da bala'i aunty Aisha tace, "ban taba tunanin Sharin naku da muguntar ku ta kai haka ba wallahi ku dai kunji kunya insha Allah se kunga sakaya Allah" gwoggo dake tsaye ce kamar gunki hannu ta dafe da kumatu, Sara ta katse masu tunanin da cewa, "An fad'a Nihal din ba yawan banza tatafi ba" Sara dake bakin kofa ta fad'a tana mai daga hannu ta dauke aunty Aisha da mari tace, "uwa ta ba asarki bace," Ahmad dake tsaye ya dauke Sara da mari har guda uku yace, "banza k'azama har kin isa ki taba min fuskar uwa na tsaya ina kallan ki" Ahmad ya ida zancan tare da yin kukan kura kan Sara tana zunduma ihu saboda taurari da take gani gashi Ahmad ya bita da duka baba sani ne ya dauke shi da mari yana cewa, "Ashe Ahmad baka da hankali se ka biyewa mata suna shashanci idan baza ka bada hakuri ba ai baka hura wutar ba" Ahmad dake fama huci yana aikawa sara mugun kallo baffa da shigowar shi yanzu yace, "to tsoho munafiki ! a gaban ka an tasa min iyalli ana duka sannan saboda tsabar rashin mutunci a cikin gida na" baffa ya ida zancan yana cin kwala baba sani yana huci yace, "Nihal din diyar wani shege ce cikin ku diyar kanina ce, za'a zumin har gida ana tanbaya ta idan ma kwad'a ta nayi na cinye ai ba abinda ze dame Ku bale Ku karankad'a miya danki uwa! ina kuke sanda ita hansatu take ciwo uban wani ya zo cikin ku nemanta? oh wato se yanzu dana gama gina yarinya ta zabin yawo banza saboda gadan gida Ku ne dan mu zuri'armu babu wace tayi yawan daduro shine yanzu zaku zo min gida da zancan banza" aunty Aisha ta bud'e baki zata mulmulawa baffa ashar baba sani ya aika mata wani irin kallo taja baki ta tayi shuru tana maida numfashi gwoggo dake gefe tace, "fada masu dai malam tasha a nono ne" ta ida zancan tana gyara tsayuwar zanin ta tana aikawa aunty Aisha da harara sannan baffa yace, "ku tatara ina ku ina ku ku fice min a gida tun kafi na nuna maku kuni wanene" ya ida zancan yana jera masu takalma su aunty Aisha tace, "wallahi talahi kotuce zata rabu mu daku se kun fito mana da Nihal duk Inda ta shiga" aunty Aisha ta ida zancan tana kuka jan hannun ta baba sani yayi suka fice har suka shiga mota Aunty Aisha na kuka tana cewa, "duk wannan Abu da ya faru har da laifin mu yaya sani mun manta da Nihal har na tsawan shekara daya tunda yayata rasu basu sake dawowa ba, wannan Abu da mi yayi kama wallahi na san Nihal baza ta taba aika ta abinda suke fad'i ba" Ahmad dake driving yace, "Small mom kiyi hakuri ki daina zubar da hawayan ki, insha Allah duk idan take za'a ganta kuma komin daran dadewa zata nememo, su kuma su je Allah na sane da su" Ahmad ya ida zancan yana mai cigaba da driving share hawayan ta Aunty Aisha tayi tana cewa, "dole nayi kuka Ahmad nasan cewa Nihal taga rayuwa tanimu mugun mutum ne Allah seya sakawa Nihal" baba sani yace, " 'yanzu dai mu koma gida a sanarwa hukuma yan'sanda amma karki fada wa khabir halin da ake ciki kin san zafin zuciyar shi Allah dai ya kyauta yasa hannun na gari ta fada gabaki daya suka amsa da amin.

*****

A hankali sultan ke bud'e lumsasun idanuwan shi juyawar da dakin ke mashi ne ya sasa kara lumshe idanuwan shi yana maida numfashi shi da kyar, linke dadumar hannu ta Nihal tayi ta aje tare leka fuskar Sultan a zuciyar ta tana cewa wannan mutumin Allah ya zuba mashi kyau kamar shi yayi kan shi, amma a haka se ka rantse be da masifa, ganin hannu Sultan na motsawa a hankali yasa Nihal saki murmushi tana me kara kallan fuskar shi tana addu'ar Allah yasa ya bud'e idanuwan shi, a hankali sultan ya bud'e idanuwan shi ya sauke su kan Nihal tsare ta yayi da ido yana kallo itama kallan shi take tana dariya mai kuka da sauri ta fita domin kira doctor ko 5 minutes Nihal ba tayi ba se gata ta dawo da doctor duduba sultan yayi tare da cire mashi a Karin jinin da ake mashi shi da oxygen din hanci shi, sultan bin su kawai yake da ido yana lumshe su, se da doctor ya gama komai sannan ya juyo yana kallan Nihal yace, "ki had'a mashi tea me kauri yasha banda bread"

"Toh" Nihal tace sannan doctor ya fita a hankali Nihal ta karaso bakin bed d'in tare da yin kokarin jigina da Sultan lumshe ido sultan yayi yana shakar kamshi turaran Nihal dake mamaye mashi hanci veil din kanta ne ya zame gashin kanta ya zubo mashi a fuska ajiyar zuciya sultan ya saki tare da ware idanuwan shi ya sauke su kan Nihal dake juyowa suna facing juna dauke kai Nihal tayi zata mike veil din kanta ya tad'iye ta fadawa tayi luuu sama fadadan kirji sultan rintse ido Nihal tayi tare da cije hakora tayi loma a kirji Sultan sun dau lokaci me tsawo a haka, lumshe ido sultan yayi yana shakar kamshin Nihal tare da jin saukar numfashi Nihal a chest din shi a hankali Nihal ta dago kamar Mara gaskiya tana gyara gashin kanta cije hakora Nihal tayi tare da mikewa zunbur ta dauki veil din ta jikin ta se rawa yake ciki sarkewar harshe tace, "kayi hakuri dan Allah ba da gangan na fado...!!! Nihal tayi shuru saboda tsare ta da ido da Sultan yayi ciki rawar jiki Nihal ta fara had'a mashi tea hannun ta se kyarma yake Sultan ko bin ta kawai da ido yake har ta gama hada tea din ta mika mashi wajan amsa ya had'a da hannun ta me laushi yana mai kara tsare ta da ido ita d'inma kallan shi take, tiririn tea din ne ya fara kona Nihal yar kara ta saki tana cewa, "aushh hannu na ! rike hannun ta Sultan yayi yana hura mata da iskar bakin shi me sanyi tsare Sultan da ido tayi tana kallan red lips din shi ritse ido Nihal tayi tana cewa a zuciyar ta, ya Allah jin an murda kofa yasa Nihal fisge hannun tan kokarin tashi Basmal ce da Ammar suka shigo Basmal tace, "aunty na da sauri Nihal ta shige toilet Basmal ta kyalkyale da dariya tana kallan Ammar tana dariya kasa-kasa saboda yadda Sultan ya had'e rai ta aje basket din hannu ta

```Taku har kullun salma mas'ud nadabo```
[1/7, 2:29 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🕊 *SAUYIN RAYUWAN*🕊
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
*Story*
*And*
*Writing*✍🏾
*By*
*Salma mas'ud nadabo*👑

🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
(```We are the among the rest```)

*Page: 83_84*

Kwana uku sultan ya kwashe a asibiti yana jinya duk wata kulawa Nihal ke bashi ita, har mamaki irin dawainiyar da take mashi yake hakan se yasa ya dan saki jiki da Nihal har ta dan fara bashi tausayi, bayan an sallamo su hukuma ta wanke sultan daga zargin da ake mashi sannan har yanzu tana kan bincikyan ta, Gimbiya jalila da Ashad ko kamar suyi hauka dan baki ciki dan sun so ace sultan ya mutu a asibiti. DPO Bilal haka ya rinka ba Sultan hakuri a kan abinda ya faru sultan gwada mashi yayi kwata-kwata be damu ba saboda ko so daya be kawo shi a rai ba, dan yafi zargi na kusa da shi ne ke mashi zagwan kasa wanda har yau ya kasa tabatar da zargin shi wannan kenan.
Chapter 56 · 0% Book details