← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 128

Sashe 15

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da kyar Nihal ke takawa saboda wani irin jiri dake d'ibar ta ga wani irin nauyi da farantin talla ya mata a haka ta samu ta k'araso har inda suke haduwa da yaya, ko da ta zo wajan ba kowa se baba mai gadi data hango yana zaune saman kujera shi kamar kullun, da kyar ta iya takowa har wurin shi tunda baba mai gadi ya hango ta yake ta washe baki saboda da ya hango Nihal yasan yau gidan shi ba kwanan yunwa, ganin ta k'araso wajan shi ya sashi tashi a kid'ime saboda yanayin da ya ganta a ciki gefen bakin ta a fashe jini na zuba fuskar nan tayi jawur ta kunbura, tausayin tane ya lulub'e shi tare da tanbayar ta cikin nuna tausayi yace, " Nihal mi ya sameki ? maganar da yayi ma Nihal ce tasa ta sakin kuka a hankali ya Shiga bata hakuri duk da bai San dalilin yin kukan nata ba amma dai koma minene yasan irin bak'ar wahala da Nihal ke sha a hannu marik'in nata, janyo hannu yayi tare da zaunar da ita saman tabirin da yake zaman sannan ya aje farantin ta gefe dan ya lura tsayuwar gagarata take nemanyi, har Nihal ta zauna bata ce ufan ba se ajiyar zuciya da take faman saukewa, baba mai gadi ne yace, "sannu kinji Nihal bari na kira maki yayan naki ai yana ciki" daga mashi kai Nihal kawai tayi da Sauri shi ya k'arasa yana ayana yadda aka maida fuskar Nihal kamar lauje dan duka a dai-dai bakin kofar parlour yaci karo da yaya Wanda ke k'ok'arin fitowa sanye yake da shada light brown tasha aiki da dark brown zare haka hula dake kanshi light brown colour ne da ratsin dark brown ba k'aramin kyau ya zaubaba se kamshi yake zubawa ganin baba mai gadi ne ya sasa tsayawa yana sakin k'ayatacan murmushi Wanda fararan hak'oran shi suka bayana, ko da baba mai gadi ya k'araso jiki shi a sanyaye kamar an zare mashi laka ganin haka yasa yaya tambayar shi lafiya tun kafi yayi magana yace, "baba Allah yasa lafiya dai," "Eh to lafiya ba lafiya ba yarinyar nan ce Nihal ta zo kamar wadda tayi hadari," ko ida ji zancan yaya beyi ba ya wuce baba mai gadi da Sauri ya fita, ida baba mai gadi ya bar Nihal har yanzu nan take sai dai wannan karan kanta na bisa cinyoyin ta, ta dunk'ule waje d'aya tana faman sauke ajiyar zuciya, da sauri yaya ya k'araso tare dayin kneel down dai-dai setin Nihal a hankali yasa hannu yana dago da fuskar Nihal wadda a lokaci ta k'ara kunbura rintse idanuwa yaya yayi tare da ware su kan fauskar Nihal cikin rudewa yana cewa, "k'anwata waya makin haka? duk wadda ya maki haka be kyauta ba wannan wani irin laifi kika aikata da za'a maki irin wannan horan" kuka kawai Nihal ke shek'awa musanman taga yayan nata wanda take mashi shagwaba yadda take so kukan da Nihal take shi ya k'ara rikita yaya sai fama lalashin ta yake, cikin sanyi murya yace, "ya isa mana kukan kiyi hakuri kijin k'anwata bari na fito da mota na kai ki asibiti kijin" daga mashi kai Nihal tayi ciki gida yaya ya koma ya ya janyo hadadiyar motar shi luxus me tsada gaske baba mai gadi ne ya wangale mashi gate ya fita sai da ya zo dai-dai saitin Nihal yayi parking tare da zagayowa ya bude mata murfin mota, zaro idanuwa Nihal tayi tana kallan motar duk da zafin ciwo da take ji qin tasowa tayi sai idanuwa da dake ta faman rabawa ganin irin yadda take yasa yaya k'arasawa tare da kamo hannuwata sai fama titila idanuwa take cikin rawar murya tace, "yaya na warke wallahi," dariya abin ya so bama yaya amma sai ya hade rai yace, "shiga muje asibiti zan kai ki kijin" make kafa ta kumayi tana San zame hannuwan yaya daga rukwan da ya mata, ita Allah na gani bata iya Shiga wannan motar ace Mota duk bak'i har da window's ai bama zeyu ba ta bishi duk Nihal na wannan zancan azuciyar tane, kamar yaya yasan tunanin da Nihal take yace, "tsoran Shiga motar kike ko? Saboda bakin tinted" kallan shi Nihal tayi dan ita bama tasan me tinted din ba, cike da kauyanci Nihal tace, "me kuma hakan yaya" dariyar da yaya yake ta boyewa ce ta kubuce masa sakin baki Nihal tayi tana kallan shi ganin be daina dariyar bane yasa Nihal sakin kuka shuru yayi yana kallan Nihal murmushi ya saki tare da ja mata hanci yace, " ke ko wallahi kin iya rigima wannan mijin ki ya bani da rigima Shiga muje a duba min lafiyar ki haka nan za'a lalatawa yar k'anwata kyakyawar fuskar ta da duka," murmushi Nihal tayi bata ce ufan ba ta shige motar tana dari-dari rufe murfin motar yayi tare da zagayowa ya shige motar ya ja su, a hankali yake tukin duk bayan mintina yana kallan Nihal Wanda sanyi AC motar ke San sata bacci, isowar su harabar asibitin yasa yaya gyara parking sannan ya b'ale murfin motar ya zagayo ya budewa Nihal, ko da suka shiga asibiti office din Dr suka Shiga dressing aka mata sannan aka mata alura wadda sai da aka sha fama dan da kyar ta tsaya, sannan Dr ya basu magunguna tunda Nihal tasha alura take aikawa yaya harara da murguda mashi baki sai faman kumbure-kumbure take a dole fushi take da shi, abinma dariya yake bashi Hakan ma da take ba k'aramin k'ara mata kyau yake ba, har suka zo Shiga mota ba Wanda yace k'ala bude mata murfin motar yayi ta Shiga sannan shima ya shige be zame da so ko ina ba sai wurin shitu me tsire a nan ya siyi tsire sannan ya shiga shagwan kusa da shi ya siyo lemo masu sanyi, ya dawo bude back seat yayi ya aje ledojin sannan ya dawo ya zauna mazaunin driver har lokacin Nihal fushi take da shi, a hankali ya daura hannuwa shi saman na Nihal dago idanuwa tayi suna kallan juna shagwabe fuska yaya yayi ya zama abin tausayi yace, "please ayima yaya hakuri a daina fushi da shi haka mana please" ya ida zancan yana shagwabe fuska dariya Nihal ta saki tana cewa, "dama manya na shagwaba yaya? " Eh mana manya na shagwaba musanman idan yaya yayi ma k'anwa laifi ya ida zancan yana Jan cheeks din Nihal, dariya Nihal ta kuma tintserewa da ita tana cewa, "amma gaskiya yan birni ke haka gaskiya mu nan kauye ba namijin dake shagwaba" murmushi yaya ya saki yace, "Dan Allah? "Allah kuwa" "tab muko birni kowa na shagwaba yayi maganar cikin sigar wasa kamar yaro washe baki Nihal tayi tace, "Kasan wani Abu yaya? " a'a sai kin fada" "gaskiya yaya ni dan birni zan aura," dariya yaya ya saki yana mai cigaba da tukin da yake yace, "alalai k'anwata ta fara zama yan'mata rufe fuska Nihal tayi ala dole tana jin kunyar yaya dariya sosai yaya yake yace, "karki damu indai dan birni ne kin samu ni da kaina zan zaba maki miji ko ki fada min irin Wanda kike so na samo maki me hankali da natsuwa wadda zai kulamin dake," murmushi kawai Nihal tayi, janta fira sosai yaya yayi har suka k'araso gida tunkafin ya Shiga da mota cikin gida Nihal ta sauka shi kuma ya k'arasa da motar ciki, bayan yayi parking ya dawo Inda suka saba zama dauke da ledoji a hannun shi sai da suka k'ara gaisawa da baba mai gadi ya k'ara tanbayar shi me jiki sannan shima ya mik'a mashi ledar dake hannu shi guda daya sannan ya k'arasa wajan Nihal wadda ke zaune tana wasa da yar tsutsuwa isowar yaya ne yasa yar tsuntsuwar tashi sama, murmushi ta saki ganin yaya zama yayi sannan ya bude Leda d'aya yace, "oya matso ki sama cikin ki wani Abu nasan kina jin yunwa washe baki Nihal yi tare da janyo ledar lafiyayan tsirene yaji albasa da tumatur da k'uli gefe guda kuma ga mango juice , wani miyau Nihal ta hadiya tare da gyara zama ta faraci hannu baka hannu k'warya yaya na kallan ta wani irin tausayin tane ya lulube shi insha Allah sai ya fida ta daga cikin wannan kuncin wannan promise yayi ma kanshi, daina cin da tayine yasa yaya tanbayar ta yace, " kanwata kar dai ki ce min har kin koshi so kike na maki dure ko," idanuwan Nihal ne suka kawo ruwa tace, "yaya inata cin dadi na manta da umma na gaskiya ban kyauta ba ko yaya,? Murmushi yaya yayi yace, " to yar umma ai umma ba taki bace ke ka d'ai nima na aje mata karki damu ki cinye wannan nakine," murmushi Nihal ta saki ta mai godiya a gaskiya bata da abinda zata ce ma yaya shiyasa ta aje shi waje na musanman ita ko tayi ma kanta alk'awari duk randa yaya ya nemi wani Abu a wajanta zata mashi sai dai inya sabawa shari'a musulinci ne ba zatayi ba.

Wayar yaya ce ta fara ringing da Sauri ya miqe tare da matsawa gefe yana wayar Abu daya na karshe Wanda yace shine insha Allah 1 week na cika zan dawo zan zo maka da labari me dadi , duk da ba'a jin abinda na wayar ke cewa amma da ka lura da yanayin wayar zaka Kasan aminan junane wayar su ke cike da kauna sai da yaya ya gama wayar tsaf ya dawo yana kallan Nihal wadda har ta gama cin abinci sai kunsan yama likis sannan yaya ya rako ta kamar yadda suka saba ya bata Kudin ta cif da qari sannan ya bata ledar magunguna ta yana kallan ta har ta shige gida.
Chapter 15 · 0% Book details