← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 128

Sashe 43

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bayan sun koma d'aki Dara da Nihal Dara tace, "hmmm yaran yanzu ba'a iya masu, ko jin kiri babu yanzu shi duk wannan kulunbotsan da ya gama maki ai na dauka se kinyi wata kafin ya neme ki se gashi har da kyauta da ya dace Abawa kowace cikakiyar mace ya baki hakan na nuna lafiya lau kika zo gaskiya Ammi zata ji dad'in labarin nan sosai," Dara na maganar tana yima Nihal gashi ita ko tayi fuska dan bata gane me jakadiya ke nufi ba aiko da suka fito lokacin har k'afar ta, ta saki ta fara tafiya Normal Dara se cewa take "gashi nan magani har yayi aiki sannu kin ji ai kin durzu wallahi" Nihal ko se d'aga kai take tana cewa, "baki ji d'a zu ba jikin se ciwo yake Amma yanzu ya saki"
" ai dole tafiyar kima sauyawa tayi" Dara na maganar tana shirya Nihal cikin wata gwon dark blue me bud'adan kafad'a saman ta anjera stone's masu kyalkyal daga baya kuma tana da igiya shepa d'in ta ya fito sosai zubo mata tayi da gashin ta har gadan baya, tayi wani irin kyau Dara tace, "bari na kira Ranka yadad'e ku wuce dining area" tabe baki Nihal tayi tare da zama bakin gado.

Aziza ce ta shigo d'akin Nazili tace, "Aunty Nazili Ammi tace kiyi hakuri ki zo kiyi breakfasat" tsaki Nazila ta saki tana cewa, "idan bazan yi ba fa," rufu kofa Aziza tayi cike da gulma tace, "Sultan da Amaryar shi yanzu zasu fito, tab'e baki Nazili tayi tare da cewa, "ganin zuwa," mikewa tayi ta shirya cikin wata orange riga mara hannu sannan tasa black skirt ya kama jikin ta sosai shepa ya fito se skirt d'in yayi kamar gwon tasa parking gashin tayi tare shafa red Jan baki a lips d'in ta direct dining area ta wuce.

Murd'a kofar da akayine yasa Nihal d'agowa ta kalli bakin kofa Sultan ne tsaye shirya ciki wata armani royal blue suit da white inner tie d'insa kala suit d'in ta kama jikin sa hata wandon pencil ne ya saka cufflinks masu diamond royal blue stones yayi kyau har ya gaji he look masha Allah can kasan makoshi Sultan yace, " se ki ta so muje ko" a hankali Nihal ta tashi tasa flat shoe black sannan ta taso, har sunyi gama Sultan yace, "kada ki kuskura ki gwada ma wani cewa muna da matsala nama fad'a maki duk abinda zanyi inayi ne dan lafiyar Ammi to ki guji bacin ranta" ya ida zancan yana had'e rai, kallan shi Nihal kawai tayi tare da kauda kanta, a hankali suke tafiya a tare jigidar da Nihal tasa na amsawa duk wanda ya ji k'ara se ya gane cewa jiya sun kasance a tare, hakan ba k'aramin dad'i yayi ma ammi ba data ji k'ara, a haka har suka iso dining area kallo ya koma kasan su, Basmal tace, "masha Allah matar yayana kinyi kyau" murmushi yak'e Nihal ta saki tace, "Na gode" Nazili dake zaune ji tayi wani kulutun bakin ciki ya mata tsaye da kyar take had'iye miyau, Sultan jama Nihal kujera yayi ta zauna tana raraba ido sannan ya zauna kusa da ita a tare suka gaishe su Ammi da mom, amsawa sukayi cike da fara'a Gimbiya jalila da Ashad ko ji suke kamar su shak'e Sultan har se ya daina numfashi, haka itama Nazili ji take kamar ta kashe Nihal dan haushi musanman data ganta kyakyawa da kusan haske kawai Nazili zata nunawa Nihal nesa ba kusa ba, serving nasu plantain porridge Wanda yasha yan'ciki fara cin abinci sukayi cikin natsuwa, Nazili ce ta katse shurun da cewa, "Sultan Ashe kayi aure?
"Uhmm" sultan yace yana mai cigaba da cin abinci" kallan mutanan dining Nazili tayi tare da kallan Nihal tace, "Amma naga saurin yin auran nan yaushe kuka had'u da Sultan ne dama kun dad'e tare ? Nazili ta jefawa Nihal tanbaya tare da tsare ta da idanuwa Shuru Nihal tayi tana kallan Nazili wadda ta kafe ta da idanuwa, sultan ne yace, "Nazili kin fiye tanbaya da yawa" Sultan ya ida zancan yana tsare Nazili da ido, maganar da Sultan yayi ma Nazili tayi ma Ammi dad'i saboda dama ba Wanda yasan wacece Nihal daga maimartaba se Basmal su kad'ai ne suka sani, aje spoon d'in hannu ta Nazili tayi tare da cewa, "daga tanbaya se ace na fiye surutu," murmushi Nazili ta saki ta k'ara cewa, "wanenen mahaifin kin a Nigeria wani aiki yake? Kema doctor ce oh what" Nazili ta ida zancan tana tsare Nihal da idanuwa, Gimbiya jalila uwar gulma tuni ta dago Nazili kishin Sultan take wani murmushi ta saki tana tunanin ga wata dama ta samu tana wani huhura hanci tana kallan Ashad Wanda shima ya d'ago Nazili, kwarewa Nihal tayi ta fara tari da sauri Sultan ya mik'a mata ruwa yana aikawa Nazili mugun kallo yace, "bakin San idan ana cin abinci ba'a magana ba," murmushi Nazili ta saki tare da cewa, "kamar na so nasan wata me kama da ita ne shiyasa nake tanbayar ai" gaban Nihal ne ya k'ara yankewa ya fad'i, a je spoon d'in hannu ta Nazili tayi, ta watsawa Nihal mugun kallo ta zo dai-dai setin Nihal tana cewa, "sorry dear nasa kin kware hala baki basa cin irin shi a gida ba ne" nata maganar tana kallan Nihal gabaki d'aya Nihal ta ji ba dad'i saboda ta gane cewa gasa mata magana Nazili take sannan ta dafa kafad'ar ta tare da bari dining area ta shige daki tana cewa, "Uhmm yanzu na gane saboda mi yasa Sultan ya aure ta saboda kyan fuskar ta ko to se na kona fuskar , se naga yan da za'ayi, se na had'a mata makircin da Sultan ze tsane ta har abada, am gonna make this house a living hell to you Nihal, se naga bayan ki, talaka kawai," ta ida zancan tana smile tare da janyo wayar ta dake bedside drawer.....

```Taku har kullun salma mas'ud nadabo```[1/7, 2:27 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
*Story*
*And*
*Writing*✍🏾
*By*
*Salma mas'ud nadabo*👑

🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
(```We are the best among rest```)

*Page: 73_74*

Bud'e murfin mota Sultan yayi ya shige jingine jikin seat d'in mota yaga Ammar idanuwan shi a lumshe tsare shi da idanuwa sultan yayi yana kallo ko bai fad'a ba fuskar shi ta nuna damuwa k'arara saboda fuskar shi ta canzan lokaci d'aya, cikin calm tune sultan yace, "Ammar ! A hankali ya bud'e lumsasun idanuwan shi Wayan da lokacin sun rine da ja, ya zubawa Sultan na mujiya, hankalin Sultan ne ya tashi ya cigaba ta cewa, "Ammar what wrong with you? Nazili ta b'ata ma rai ne? Mi ya same ka, shiyasa bana san yariyar nan bata da kunya" k'ak'aro murmushi Ammar yayi Wanda iya karshi lab'an shi yace, "Ba abinda Nazili ta min, kira na akayi a waya yanzu ake ce min friend d'ina ya rasu," langwabe kai Sultan yayi yace, "Eyya Ammar Allah ya ji kanshi, take heart, amma ya akayi ban san shi ba? Sultan ya ida zancan yana tsare Ammar da ido kasancewa duk friend d'in su d'aya, d'an daburcewa Ammar yayi tare da cewa, "San da naje kauye ba tare da kai ba shi ne lokacin muka zama friend sosai har muka saba" tab'e baki Sultan yayi yace, "OK Allah ya gafarta mashi"
"Amin" ganin Ammar d'in duk yayi suku-suku yasa Sultan cewa, "bari nayi driver d'in na lura kamar baka cikin natsuwa" d'aga kai Ammar yayi tare bud'e mazaunin driver ya barma Sultan ya koma inda sultan ya bari har sultan ya ja mota Ammar ya kalli sultan tare da cewa, "please ka sauke ni gida bana jin zan iya komawa aiki yanzu," kallan Ammar Sultan yayi yace, "ba dai shanono zaka tafi yanzu ba? Girgiza kai Ammar yayi yace, " Se gobe zani"
Da ace bani da theater gobe da munje tare,"
"Ku ma fa " Ammar yace tare da maida idanuwan shi ya lumshe, kofar gida sultan ya aje Ammar ya wuce dan tsakanin gidan waziri da gidan maimartaba ba wani tazara dan duk kusan cikin gida d'aya ne.
Chapter 43 · 0% Book details