← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 128

Sashe 96

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*_fan's ina mai baku hakurin jina kwana biyu shuru hidimomi ne sukayi min yawwa, masu kira na da masu yimin text duk na gode wannan page naku ne kyau ta, kuyi yadda kuke so, ina ganin comment yadda ya kamata hakan na karamin gwarin gwiwa_*

*Page: 113_114*

Dago sultan Frank yayi daniyar ya kara luma mashi wuka jiniyar motar yan'sanda ce ta katsewa frank hanzari zaro ido yayi yana kallan yaran shi da sauri ya saki sultan ya fadi kasa, da sauri suka shiga guduwa ko da yan sanda suka shigo sun sha mamaki irin ta'adancin da aka aikata kafin su iso, kafin ka ce mi ambulance ta zo wasu cikin su sun mutu wasu da sauran su sultan da har a lokacin yana jin motsin mutane sama-sama aka sa shi cikin ambulance.

Kaitsaye asibiti aka wuce da su dan basu taimakwan gagawa shugaban kasar Moscow yasha mamakin irin wannan ta'adaci da aka tafka abin takaicin ma ko mutun daya ba a kama ba, kuma duk yawan security's basu tabuka komai ba, ko dayake daga gani ba kananan makisa aka samu ba amma yace a tsana ta bincike har se an gano su tunda yan kasar ne babu idan zasu, sannan ya hana shige ta fice har ma da masu yunkurin barin kwasar yace karsu barta, har sai an gano makisan.

Likitoci suna iya bakin kokarin su a kan Alex dan ganin cewa sun ceto rayuwar shi dan ba karamar galabai ta yayi ba, dan ba suyi tunanin yana da rai ba da farko, dan har an sashi cikin matatun hannun shi ya fara motsawa, cikin ikwan Allah an cire mashi bullet's din dake jikin shi amma har a lokacin yana como, bangaran sultan ma an cire mashi bullet daya na kafar shi ayi mashi dressing an kai shi waiting room har a lokacin be tashi ba.

*******
Yau dai kam Nihal suku-suku ta tashi gaban ta ban da faduwa ba abinda yake haka dai tayi wanka ta shirya cikin uniform din ta, wayar ta ta janyo ganin bata ga miss call din sultan ko daya ba, wata zuciyar tace ta kira shi toh ko ta kira shi yanzu a can dare ne kilama yana bacci hakan ya hana Nihal kiran sultan sannan ta wuce main parlour dan yin break, lokacin su Ammi suna zaune suna break gaishe da su tayi a takaice ta zauna Ammi ce ta kalle ta tace, "Nihal yana ganki suku-suku ko tun yau kin fara missing mijin naki? Cike da kunya Nihal tace, "a'a Ammi bana jin dadi ne shiyasa"
"sannu kin ji, kuma shine kikayi shirin zuwa makaranta? ki zauna gida ki huta, idan kin samu sauki se ki je,"
"zan iya zuwa makaranta tunda ciwan ba wani rufe ni yayi ba, kuma kin ga jiya ban je ba, be kamata na rinka fashi ba daga fara zuwa na"
"haka kuma toh kafin ki fita ki tabata kin sha magani" daga kai Nihal tayi tana break haka nan dai ta tsakuri abincin sannan ta wuce parking space lokacin driver na zaman jiran ta.

Koda Nihal taje makaranta bata daina jin faduwar gaba ba, Nana ce ta ta lura da yanayin da Nihal ke ciki ne tace, "Nihal mike damun ki ne baki daya yau kinyi sanyi kamar wani abu na damun kin, ko dazu da uncle ya shigo hankalin ki baya kan karatun kwata-kwata" numfasawa Nihal tayi tace, "Nima Nana ban san me ke damuna ba bana jin dadi jiki na gabaki daya"
"Allah ya sauwake ki yawai ta addu'a ita ce makamin mumini, idan an tashi break se muje ki sha magani,"
'bana jin zan iya shan magani na san dana koma gida komai ze zama normal"
"Allah yasa"
"Amin" shigowar Malami ne ya katse Masu zance suka cigaba da daukar darasi a haka har lokacin tashi yayi Nihal ta dawo gida.

Koda ta dawo part nasu ta wuce tayi wanka ta shirya cikin wata blue doguwar riga, rigar ta mata kyau ta kama jikin ta sosai, sai dai fuskar nan tata ba walwala tayi fayau da ita kamar ta kwana biyu tana ciwo, wayar ta dake ciki drewar ta ciro har yanzu ba kiran sultan ba alama da kanta ta shiga kiran layin amma wayar kashe dan kwata-kwata bata shiga lamarin har ya fara daure mata kai amma se ta share ta wuce part din Basmal dauke da sallama a bakin ta ta shiga Basmal dake zaune a parlour tana kallo ta amsa cikin fara'a tace, "Aunty Nihal yanzu nake cewa zan shigo cikin gida na tanbaye ki gabaki daya yinin yau wayar yayana bata shiga, hankali na duk ya tashi," zaunawa Nihal tayi tana cewa, "Nima na kira amma wayar bata shiga, ina tunanin aiki ne ya mashi yawa,"
"kuma fa tana iya yuyuwa saboda na san yayana baze kashe wayar shi haka nan ba, ko dan ke ze barta kune, amma kuma yayana be saba kashe waya ba idan yayi tafiya kina ganni lafiya kuwa? Shigowar Ammar ne ya katsewa Basmal zance da sauri Basmal ta karasa tayi hugging nashi tare da sakar mashi pack a kumatu ta amshi briefcase din hannun shi cikin sigar shagwaba tace, "my love sannu da zuwa"
"yauwa abar kauna ta, yana ga fuskar ki na dauke da tsantsar damuwa waya taba min ke?
"Ban wanda ya taba ni lamarin yaya ne ya fara bani tsoro,"
"Me ya faru da shi abar kauna ta?
"babu komai, kunyi waya da yayana duk yinin yau?
"a'a bamuyi ba na kira wayar bata shiga amma nasan aiki ne ze rike shi, ki daina damun kanki abar kauna ta, har kin sa hankali na ya tashi"
"Kayi hakuri my love, Aunty Nihal ma duk ta damu da jin yayana shuru, tana kewar yayana da baya kusa da ita, dama tare suka tafi se sunfi samun sakewa"
"uhm kuma kinyi gaskiya musanman yadda suke love bird" Ammar ya ida zancan cikin sigar tsokana Nihal dake zaune dan darawa tayi tare da gaishe da Ammar ya amsa cikin fara'a yana cewa, "karki wani damu Nihal na san aiki ne ya rike shi daya kunna waya ke ze fara kira, karki bari wanna matar ta ruda ki"
Murmusawa Nihal tayi tace, "nima nayi tunani haka" sannan Ammar ya wuce bedroom Basmal tace, "bari na bishi ciki"
"Toh shikenan" Nihal ta ida zancan tana mikewa, "Aunty Nihal ina zaki?
"Cikin gida yanzu na tuna da Assignment nawa da banyi ba"
"Toh shikenan Aunty Nihal ki gaishe min da Ammi da mom kafin na shigo"
"Za su ji" sannan Nihal ta fice,

Kaitsaye part din Ammi ta wuce koda ta shiga se da ta tanbaye ta ko sunyi waya da sultan tace a'a sannan ta kwantar Ammi da hankali ta ganin hankalin ta duk ya tashi, maimartaba ma ya kira sultan yafi a kirga musanman da mom take gwada mashi tsantsar damuwar ta rashin jin shi tun jiya yanke shawara maimartaba yayi mindin sultan be kira gobe ba dole su bi lafiyar dan su tafiya Moscow ta kama su sannan ya cigaba da lallashin mom kanta kwantar da hankali ta.

*****

Bangaran sultan kuwa har yanzu basu farka ba, dan basu san duniyar da suke ba se dai ana basu kyakyawar kulawa dan shugaban kasar Moscow yasa tsaro sosai a asibiti tare da tsana ta bincike, har sai an ganu mashi wayanda suka aikata wannan katobara yan'sanda kuwa suna iya bakin kokarin su wajan ganin cewa sun gano su musanman kowa burin shi be wuce ace ya gano ba, shugaban kasa ya kara mashi matsayi a wajan aiki ba, hakan ya sasu jajircewa da dagewa wajan kokarin gano su frank dan tunda abin ya faru an hana shige da fice, tare da tsana ta bincike da na'ururi computer.

*********

"Gabaki daya hankali na ya kasa kwanciya har yanzu frank be kira ni ba, ban ji labari wani jirgi daya taso daga Moscow zuwa Nigeria ba, komai ya kule min brain nawa tayi zafi, Gashi ba labarin cewa sultan ya mutu ko dana kuna news a CNN ban ji wani labari daya shafi sultan ba, idan ya mutu ya kamata ayi maganar a gida jan labarai saboda shugaban likito cin Africa ne, amma na kira wayar shi kashe hakan na nufin sun kashe shi ne an kamasu ko me, ko kuma ya ji rauni yana asibiti hakan ba zeyu ba," Ashad ya ida zancan yana watsi da kayan dining, Gimbiya jalila tace, "na rasa gane wannan ragwan a zancin naka gabaki daya ka tadawa kanka hankali ka tadamin, dubi yadda kake bari da kaya saboda Allah son, ya kamata ka kwantar da hankalin ka babu abinda ze faru Mara dadi mutuwa ce dai yanzu nasan sultan ya riga dayama mutu tunda ka kira wayar shi kashe" fadawa saman kujera Ashad yayi yana cewa, "baza ki gane bane Momi jiki na yana bani akwai matsala..!
"ka kwantar da hankali ka ba wata matsala my son" haka Gimbiya jalila ta rika kwantar Ashad da hankali da nuna mashi cewa sunyi nasara wannan karan.

Da daddare bayan Nihal ta gama shirin bacci ta kamar kullun part din Ammi ta wuce dan kwata-kwata part din nasu ba dadi ga kewar sultan da ta taru tayi mata yawa gashi ta kira wayar shi yafi a kirga kashe, da wannan tunanin ta wuce bedroom din ta na part din Ammi ta kwanta ta dade bacci be dauke ta ba, tana juyi da kyar ta samu bacci ya dauke.
Chapter 96 · 0% Book details