Sashe 55
Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
A harabar asibiti Ammar yayi parking motar shi a parking lot suka fito kai tsaye Asibiti suka shige DPO Bilal dake zarya bakin emergency ne ya dago da jajayan idanuwan shi ganin su Ammar yasasa karasawa da sauri ya rungume Ammar tare da sakin kuka, jikin Ammar ne yayi sanyi, Nihal da sauri ta karasa baki kofar emergency tana leka sultan ta cikin glass d'in kofar yadda likitoci sukayi cha akan shi tausayi shi ya lulube Nihal tare da saki kuka wai me yasa duk Wanda ta sani se ta rasashi wannan wace irin rayuwa ce, ba komai ke sata kuka ba, se tunawa da mutuwar umma da Abba yau mutuwar su ta dawo mata sabuwa musanma yadda daga sultan na shan jiki zamewa tayi bakin kofa tana mai cigaba da kuka, ciki kuka Bilal yake cewa, "yanzu da wani ido zan kalli Sultan na kawo shi waje na keb'e dan kar a samu matsala se gashi an samu, na San Sultan ze kalle ni a matsayin Wanda aka had'a baki da shi dan a cutar da shi" Bilal ya ida zancan yana sheshekar kuka yana mai cigaba da cewa, "wallahi ban san an sa poinsin cikin AC ba, Dana sani ba zan kai sultan ba," shuru Ammar yayi yana shafa bayan Bilal alamar lalashi tare da zauna da Bilal saman chair din dake harabar wajan yana cewa, "be kamata kana tunanin Sultan ze ma wannan kallan ba, ya san ko kai wanene," Ammar be ida rufe bakin shi ba aka fito da Sultan daga emergency mikewa sukayi, direct waiting room aka wuce da Sultan hancin shi na manne da oxygen da Karin jini da ake mashi, da sauri su Ammar suka bi bayan doctor zuwa office se da suka samu waje suka zauna sannan suka shiga tanbayar shi ya jiki Sultan, gyara zaman glass d'in shi Doctor nafi'u yayi tare da cewa, "ya kamata Ku bashi kulawa sosai da tsaro saboda saura kad'an poisin din nan ya mashi ila kuma matsala da ake samu irin shi bin jini yake, yanzu baza mu gane ciwo ya sake shi ba se ya tashi amma ze dad'e yana fama da wahala numfashi d'an kankanin Abu yana iya sawa numfashin shi ya dauke saboda huhun shi ya matse, idan zaku bi shawara ta a fida shi waje a mashi checkup bayan wata daya ! sannan doctor yayi yan rubuce-rubuce ya mikawa Ammar paper godiya suka mashi DPO ya wuce bakin aikin shi saboda har yanzu yana kan bincikyan dalili da ya kawo poisin ciki AC, direct dakin da aka kwantar da Sultan ya wuce, zaune ya sami Nihal saman kujera tana facing gadan da Sultan ke kwance mikewa Nihal tayi tana cewa, "mi doctor yace maku" kakaro murmushi Ammar yayi yace, "jiki da sauki karki wani damu kanki kinji" daga kai Nihal tayi tare da furta "Alhamdulillah! shigowar su mom ne ya katsa masu tunani, murmushi Nihal ta saki tare da karasawa wajan mom da sauri kama hannun ta mom tayi ta zauna da ita tana me kalla sultan tace, "daughter mi yasa Baku fad'a mana halin da kuke ciki ba,? shuru Nihal tayi tana wasa da yan yatsun hannun ta tana cewa, "bamasu mu tada maku hankali ne shiyasa" Nihal da ida zancan a raunane shafa kumatunta mom tayi tace, "daughter kunyi tunanin mai kyau, amma nan gaba karku kara boye mana wani abu" daga kai Nihal tayi, maimartaba da Ammar fita waje sukayi Ammar ya fad'a mashi abinda doctor yace shuru yayi can kuma yace, "Allah ya ba Sultan lafiya"
"Amin! Ammar yace yana rufe bakin shi waziri da Adda suka karaso waziri ya mikawa maimartaba hannu suka gaisa yace, "inane dakin daka kwantar Sultan? maimartaba yace, "mu karasa tare muma ai yanzu zamu koma" suka shige cikin. Bayan sun gama duba sultan har a lokaci be tashi ba maimartaba yace ya kamata su koma gida tunda jikin da sauki se a bar matar shi da kula da shi mom tayi na'am da zancan shi haka suka baro Asibiti akan cewa za'a aiko Basmal da dinner.
Zagaye parlour Ashad yake yana cewa, "ban so sultan ya farfado ba wannan mutumin Allah ya mashi taurin rai," Ashad ya ida zancan yana wurgi da cup din glass dake hannun shi yana mai cigaba da cewa, "Momi ni fa ban k'i na aika har asibitin a kashe shi ba, amma wannan banzan yakubu yana fad'a min cewa akwai security a kofar dakin shi, ni wannan labari be min dadi ba" Ashad ya ida zancan yana zama saman kujera, Gimbiya jalila ta numfasa tace, "Ni bama wannan ya dameni ba yanzu idan aka gane dasa hannu ka ya zamuyi,? Wata iri dariya Ashad ya saki tare da cewa, "Momi kenan ke kika haife ni Amma har yanzu kin kasa sanin wanene a salin Ashad, duk abinda zanyi ina anfani da kwakwalwata ina anfani da takuna ! babu Wanda ze gane da sa hannu na of coz ina gida bani da lafiya sanda Nas ya canza alururi ba Wanda ya ganshi, kuma tare da shi akayi operation din kuma yanzu haka baya kasa ya tafi karo karatu ta karkashin gwabnati, document d'in dana sace tuntuni na kona, san da naje Dubai lokaci nayi document din safara kwayoyi da sunan Sultan sannan na koyi singing din shi nayi na aje mashi a office ba Wanda ya sani" ya ida zancan yana saki dariya "amma ki san wani Abu sultan nada wayau komi zeyi biyu yake ajewa nasan tabas yana da wasu documents din aje, dole sultan ya mutum momi na tsane shi" ya ida zancan yana furzar da iska me zafi.
Nazili ce ta shigo part din Ammi tana bin Gimbiya jalila da Ashad da kallo kasancewar suna part d'in Ammi a cewar suna kula da ita har zata Shiga dakin taci birki tana cewa, "lafiya na ganku yau a nan ina sauran mutanan gidan? Nazili ta fad'a tana tsare su da ido, lagwabe kai Gimbiya jalila tayi ta koma kala tausayi tare da kwashe duk abinda ya faru ta fad'awa Nazili bud'e baki Nazili tayi tace, "ya Allah ! da yaushe duk wannan Abu ya faru? juyuwo tayi da niyar ta wuce asibiti ganin sun mom sun shigo ya sata cewa, "kun dawo ina sultan ? Nazili ta fad'a tana leka bayan su Mom, mom tace, "Sultan na Asibiti,!
"Shine ba Wanda ya zauna da shi? Nazili ta ida zancan a raunane, maimartaba ne ya katse mata zance da cewa, "daughter dawo karki damu Sultan na tare da wife na shi nasan zata ba shi kulawa sosai, shiyasa nace a basu space" tsaye Nazili tayi tana had'iye wani kulutun bakin ciki tana kallan maimartaba wato shima fada mata yake wannan almajira ta fita dacewa ta kula da Sultan ba ita ba wannan jahila mima ta sani da za'a barta da sultan ganin tayi shuru yasa maimartaba hugging nata yana shafa bayan ta tunanin shi shock ne ya kamata be san tsanar Nihal ya kara dasa mata ba a hankali yake cewa , "daughter kirki damu insha Allah sultan ze warware" daga kai Nazili tayi tana wani sunne kai sannan ta ja kafafuwanta ta shige bedroom d'in Ammi Gimbiya jalila ko da Ashad ta ciki na ciki haka kowa ya wuce part nashi yana jimami shiko maimartaba sawa yayi a tsanata bincike a gano suwa ke da sa hannu.
*******************************