← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 128

Sashe 78

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ashad ne ya shigo part din Gimbiya jalila yana sanye da jeans and Ash shirt fadawa yayi saman kujera yana cewa, "momi hidimar mi ake a gidan nan? gimbiya jalili dake cin kayan marmari tabe baki tayi tare da cewa, "kai ma dai ka gani matar sultan ce fa zata dawo shine dan fihila ake ta wannan ruguntsimin ba abinda ke ban haushi se kamar yadda minal keyi, tafi kowa rawar kai a kan sha'aninan mu nan da yara zasu dawo daga makaranta ba uwar da aka hada masu amma dayake matar dan gold ce ka ga rawar kafa" tsaki Ashad ya saki yana cewa, "karki ga laifin su yar matsiya tace shi shiyasa ake kokarin nuna mata arziki," ya ida zancan yana daukar Apple yana ci Gimbiya jalila ta cigaba da cewa, "ni bama hidimar ke kona min rai ba yadda Minal ke shige masu ko part din nan kafin ka ganta se Allah yayi ni dai Nadiya ta cuce ni wallahi..!
"hmmm ai bata da kishi ko kad'an yadda kika san zuciyar kare ni kaina tafi fifita sultan a kai na se kace ni ba wanta bane uwa daya uba daya ba anya minal ke kika haife ta kuwa, ko da yake shima Nasim din duk can suke," Gimbiya jalila tace, "da bani nayi cikin su ba da se na ce ba ya'ya na bane, da ba a ido na biyu na haife su ba naga abinda na Haifa ba, da se na ce anyimin musaya a asibiti wallahi," kwafa Ashad yayi tare da cewa, "se na fara cin uban su zasu san annabi ya faku, bari naje na shirya na zo na zauna naga yadda za'a kare indan ta kama na watsa taran da bakin ciki wani ya kara komawa asibiti," dariya Gimbiya jalila ta saki tana cewa, "son baka da dama wallahi kafi ni iya shege" dariya Ashad yayi tare da ficewa Gimbiya jalila na kara hura mashi kai.

A harabar gida motar sultan ta faka bud'e mashi murfin mota Alex yayi ya fito sannan ya zagoya gefan Nihal ya bud'e mata tare da mika mata hannu kallan sultan Nihal take tare da daura lallausan hannun ta saman na sultan gabaki dayan su shock suka ji lokaci daya, sannan Nihal ta kara fitowa daga cikin mota tana bin gidan da kallo sannan ta kalli sultan daya zagaye hannun shi a wast din ta ya kara Matso da ita jikin shi bugun zuciyar su na karuwa a hankali yayi mata rad'a kunne tare da cewa, "karki manta mun dawo gida idanuwan mutane na kan mu, duk abinda muke mu nayi ne saboda Ammi," murmushi yak'e Nihal tayi tare da cewa, "shine se ka hau kama ni da haka kake min koko wani saban salan ka bulo da shi na kamani anyhow ba zan dauka ba" Nihal ta ida zancan tana murmushi yake tana tsare sultan da ido kara dan matsa mata hips sultan yayi zaro ido Nihal tayi tana cewa, "me haka wai" dauke kai sultan yayi tare da had'e rai duk inda suka wuce bayi na masu sannu da zuwa da zubewa suna kwasar gaisuwa ganin yadda gidan ya canza yasa Nihal bin gidan da kallo duk a tunanin ta gyaran biki ne part din Ammi suka nufa a hankali Nihal ta zura kafafuwan ta main parlour wani abu ne ya fashe a raze Nihal ta rungume sultan cike da tsoro shima din rugunme ta yayi tsam a jikin shi yana shakar kamshi ta mai dadi, dariya mutanan parlour suka saki wani kyalkyali ne ya shiga zubo masu akai ita da sultan dago kai Nihal tayi tana bin kyalkyali da kallo tana sakin murmushi tana kallan yanayin decoration din da part din yasha daga jikin bango an rubuta welcome back home sultana, zamewa Nihal tayi taga jikin sultan tana bin ko ina da kallo tana murmushi minal da nawwara ne suka janyo hannu ta Ammi dake rike da plate din cake ta matso tare da gutsuro cake din tasa mata a baki tare da cewa, "barka da dawowa gida Gimbiya, Allah ya kara tsare mana ke" murmushi Nihal ta saki tare da rungume Ammi tana dariya idanuwan ta cike da kwalla ba abinda ya fado mata a rai se umma da Abba Allah ya ji kan su Nihal ta iya furtawa a ciki zuciyar ta haka mom ta Matso ta bata cake tare da bata gift murmushi Nihal tayi tare da amsa tace, "na gode mom" Gimbiya jalila ma gift ta bata murmushi Nihal tayi tare da cewa, "na gode Momi" Nazili dake gefe ta cika fam kamar ta fashe takowa tayi rike da gift tana murmushi rungume Nihal tayi dai-dai setin kunnan Nihal tace, "barka da dawowa almajira ba komai na sami cikin gift din nan ba se kudi na san shine burin almajiri" Nazili ta ida zancan tana murmushi tare da zame jikin ta a jikin Nihal kallan ta Nihal keyi tana murmushi yake sannan ta riko hannun Nazili tana cewa, "kuma a haka zan zama Gimbiya Nihal matar dan sarki na fari muna nan dake wata rana se kin zama baiwar almajira" Nihal ta ida zancan tana murmushi fisge hannun ta Nazili tayi daga rukwan da Nihal ta mata cikin zafin rai tana kallan Nihal dake murmushi, Minal da nawwara ne suka hada baki wajan cewa, "muma ga namu gift din" murmushi Nihal ta saki tare da sakar masu kiss a kumatu tana dariya sultan yana kallan Nihal dan gabaki daya ta tafi da imanin shi da salan ta, Nazili na lura da irin kallan da sultan ke bin Nihal da shi me cike da so da kauna, tsanar Nihal na kara shigar ta minal da nawwara ne suka ce, "saura na yaya ya kamata ya nuna mata nashi gift din ko Ammi ya fada mana yadda yayi missing nata da bata gida" minal da nawwara suka ida zancan suna janyo hannun sultan, dariya yayi yana ja masu kunne lokaci daya yar kara suka saki suna cewa, "wayo Allah yaya akwai zafi" cikin honey voice din shi sultan yace, "Allah ya ga abinda ya gani yasa kuke boarding da gida kuke da mun bani" dariya kowa na parlour ya saki yana cewa, "sun maida ka kakan su" sultan yace, "nima haka nagani" ya ida zancan tare da kiss kumatun su hadadan kit sultan ya ciro a aljihun shi karamin tare da bud'e kit din zube ne ciki mai kyau se kyalkyali yake zubawa a hankali ya kama hannun Nihal tsare shi da ido Nihal tayi shima din kallan ta yake yana sakin smile a hankali ya saka ma dan yatsan ta zoben wani irin kyau zoben ya kara yima hannun ta se sheki yake kallan zoben Nihal tayi tana murmushi dan zoben ba karamin kyau ya mata ba ko ba'a fada mata ba tasan me tsadane sosai saboda haskyan da shakin da yake zubawa, zame hannun ta Nihal tayi tare da dago Hannun tana murmushi tana nunawa muta nan parlour cike da jin dadi kuma tayi hakan dan ta gumama Nazili gabaki daya parlour ya dauka da "wow wannan zoben ya hadu" Basmal ta ce "gaskiya yayana ya iya siyayar masoya" dariya parlour kowa ya saki ban da Nihal dake kallan sultan dake kallan ta cikin siririyar muryata Nihal tace, "na gode sosai da wannan kyauta taka tafi ta kowa" Nihal ta fada tana murmushi yake maimartaba da shigowar shi kenan yace, "tawa kuma tafi tashi" dukawa Nihal tayi tare da gaishe da maimartaba kunya duk ta ishe ta da sauri da shige dakin ta mom tace, "ka kure ta kasa ta ji kunya" dariya maimartaba ya saki yana cewa, "nayi late har an gama tarbar diyar tawa idan ta fito ace na bata kyautar mota ga key din" cike da zumudi Basmal tace, yayana ya bita daki ya bata yanzu," Ammi tace, "haka ko za'ayi..! duk da sultan be so bin ta ba dan be san rai ni haka ya amshi key din.

Nihal na shiga daki jakarta ta dauka tare ciro hotan umma da Abba tana kallo a hankali ta shafa hotan hawaye Masu zafi suka zubo mata a hankali ta furta "I wish kuna tare dani duk wannan farin cikin da aka sani yau naso a ce su baffa ne suke bani shi, Abba ka yafe min a kan guduwar da nayi daga hannun baffa rungume hotan Nihal tayi tare da cigaba da cewa, "ina missing naku umma da Abba ku yafe min nayi aure ba tare da sanin wani nawa ba" Nihal ta ida zancan tana sakin kuka sultan dake bakin kofa yana jin duk abinda Nihal ke cewa tausayin tane ya kara lullube shi duk bakar wahala data sha hannun su baffa har yanzu tana ganin laifin ta na guduwar da tayi murda kofa sultan yayi ya shigo, da sauri Nihal ta mike tana goge hawayan ta tare da boye hotan a bayan ta a hankali sultan ya tako gaban ta tare da dago da fuskar Nihal sisiraran hawaye ne suka shiga zubo mata juya mashi baya Nihal tayi da sauri tana goge hawayan fuskar ta cikin honey voice din shi sultan yace, "Mi ya saki kuka wani ya bata maki rai ne sultan ya fada" juyowa Nihal tayi tana cewa, "ba Wanda ya bata min rai farin ciki ne yamin yawwa family din ka suna da kirki" Nihal ta ida zancan tana bud'e bedside drewar zata tura hotan hannu ta, hannun shi sultan ya daura saman nata yace, "idan nace wannan hotan ne ya saki kuka karki musamin kinyi missing umma da Abbas ne ko" zaro ido Nihal tayi a birkice ta juyo tana kallan sultan.

```Taku har kullun Salma mas'ud nadabo```[1/7, 10:14 AM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
*Story*
*And*
*Writing*✍🏾
*By*
*Salma mas'ud nadabo*👑

🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
(```We are the best among the rest```)

*Page: 99_100*
Chapter 78 · 0% Book details