← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 128

Sashe 42

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ammi dake zaune a parlour tana kallan sunna TV kafin a gama breakfast jin motsi yasata juyowa kasancewa ko sallama Nazili ba tayi, sakin murmushi Ammi tayi tana cewa, "Nazili kin dawo? cire glass d'in idanuwa ta tayi tare da hard'e hannuwan ta a k'irji ta d'aga gira tace, "Eh na dawo Ashe kunyi bikin Sultan har an gama ba Wanda ya kirani ya fad'a min se dai naga pictures na yawo a media" Nazili ta ida zancan tana Jan fasali tana kallan Ammi ido cikin ido, Ammi ce ta sasauta muryar ta tana cewa, "Nazili ya kamata ki saurare ni first mana," Nazili tace "ko Ammi! sannan ta shige d'aki tana mai cigaba da cewa da karfi, "ina tunani Ammi ba ke kika haifi Abba na ba da ke kika haife shi ba za ayi bikin Sultan bana nan ba," tana shiga d'aki Nazili ta cire veil d'in kanta tare da rik'e kugu tana zagaye daki tana cewa, "se naga bayan koma wacece matar sultan, wace tsinaniyar ce ta aura shi" jin An murd'a kofa ne yasa Nazili juyowa hannuwa ta hard'e a kirjin ta cike da masifa tana kallan kofar ganin Aziza ne ya sata sakin tsaki ta d'aga kira tana cewa, "me? kada ki fad'a min cewa har yanzu Sultan na tare da Amaryar shi?
"Uhmm Gimbiya ke ma kin san" d'aga mata hannu Nazili tayi cikin masifa tace, "bana San jin komai, wanene uban ta !
"Gimbiya nima kawai na gan..... ! Daka mata tsawa Nazili tayi tace, "fitar min daga d'aki bana san ganin ki, bama na buk'tar ganin kowa yanzu ina buk'ar hutu" cikin daka tsawa Nazili ta ida zancan, da sauri Aziza na fita har tana tuntub'e ta fice, zaunawa Nazili tayi bakin gado tana kuka tana cewa, "shikenan suna can suna jin dad'i suna soyayya, idan na kama koma wacece se na shak'e mata wuya mtsww" tana ida zancan tana kuka tare da goge hawayan ta da tissue tana mai cigaba da kuka, Ammi ce ta shigo dakin tana kallan Nazili duk se taji ba dad'i kuma itama ba laifin ta bane ba irin kiran da ba'a mata ba wayar ta baya shiga kuma dama gashi ba a ja bikin da tsawo ba Nazili ce ta d'ago jajayan idanuwan ta hata hancin ta yayi ja saboda tsabar kuka cikin masifa tace, "Ammi bana san ganin ki bana san ganin kowa" ta fad'a tana mai cigaba da kuka a hankali Ammi ta k'araso tare rungume Nazili tsam ajikin ta, tana faman bata hakuri se sauke ajiyar zuciya Nazili take Ammi tace, "kiyi hakuri Nazili nasan bamu kyau ta ba Amma,!
"Amma mi ! Nazili ta fad'a tana Jan fasali tare da kafe Ammi da ido, ta cigaba da cewa, "mi yasa baza a jira na dawo ba, saboda bani da matsayi a cikin gidan saboda iyaye na basa raye ko Ammi, me yasa Sultan ze yi aure yanzu Ammi ! na fad'a maki bana buk'ar kowa a kusa dani yanzu, I wish iyayena na raye da baza a min haka ba" Nazili ta ida zancan tare da zuwa bakin kofa ta bud'e tace, "Ammi kina iya fita bana san ganin ki" idanuwan Ammi taf da kwalla suka ciko tana kallan Nazili wadda ta kauda kanta gefe a hankali Ammi ta tako har bakin kofa sannan ta fice tana fita Nazili ta maida kofar ta rufe da karfi sannan ta shiga zagaye d'aki tana tunanin ta inda zata bulo.

Ammi na fita taci karo da Basmal k'arasawa wajan Ammi tayi tana tanbayar ta lafiya, Basmal tace, "Ammi waya b'ata maki rai? ke dawa kike hayani? Basmal ta ida zancan tana zaunar da Ammi saman kujera ruwa ta d'ebo a cup me sanyi ta ba Ammi, ammi ta shanye ruwan tas tana sauke numfashi Basmal tace, "ke dawaye Ammi? a hankali Ammi tace, " Nazili ! Waro ido Basmal tayi tace, "ta dawo ne Ammi?
"Eh ta dawo tana ta fad'a a kan anyi bikin Sultan ba da sanin ta ba"
"Oh fu ! ai ba laifin mu bane laifin wayar tane how many time's na kira bata shiga bari naje na mata magana" rik'e hannun ta Ammi tayi tace, "ki kyale ta idan ta huce zata fito koma wa akayi ma haka dole ya ji haushi musanman yadda take ji da Sultan,
"Ammi Amma be kamata ta bata maki rai ba bayan tasan problem naki"
"Naji dawo ki zauna with time zata huce"
"OK"

"Gimbiya ni fa ina ganin mun samu mafita tunda matar tashi kamar bata da wayau ko ya ki ka gani" d'an siriri tsaki Ashad ya saki yace, "dalla malama yi mana shuru ko breakfast ba muyi ba za'a fara bamu shawara mara anfan mtsw, kawai a aika yan' mashi su tare shi su kashe mu huta shine magana amma yanzu da yayi aure ya'ya ze fara jerawa fa" Gimbiya jalila ce ta numfasa tace, "da ina tunanin kamar maganar yakumbo ce mafita Amma na lura yarinyar kamar tana d'an banza wayau"
"Bana tunanin haka ranki ya dad'e"
"Allah yasa hak'ar mu tacima ruwa"
Ashad yace, "zama ta cine Ku bani lokaci" dariya suka saki Gimbiya jalila tace, "shiyasa nake sanka son aikin ka na kyau dan dai ma akwai yan hana ruwa gudu" haka suka rink'a kula makirci suna warwarewa.

A hankali Nihal ta mike daga saman sofa tana waige-waige bakin dressing mirror ta hango sultan yana shirya ciki wata suit yayi kyau har ya gaji ta dad'e tana kallan shi ganin ze juyo yasa tayi sauri mik'ewa tana k'ok'arin fita Sultan yace can k'asan makoshi, "ina zaki? Juyowa Nihal tayi tana kallan shi tare da cewa, "zan koma cikin gida ne" tsaki Sultan ya ja yace, "A haka zaki fita my friend dawo kiyi wanka sannan" ya ida zancan yana maka mata harara yace, "ko fita zakiyi tare zamu fita nama fad'a maki" sannan ya dauki bathrobe da towel ya watsa mata a fuska yace, "a wuce" gutun tsaki Nihal ta saki tare da shigewa toilet ta dad'e tana wanka tana gamawa tasa bathrobe ta daure gashin ta da towel kasancewa ta wanke shi, tana fitowa daga kwamin wanka santsin ya jata ta fad'i k'asa wata k'ara Nihal ta saki tare da sakin kuka Sultan dake zaune saman sofa yana latsa wayar shine ya ja tsaki wani ihun Nihal ta saki tana cewa, shikenan na kare kugu tana kuka, mikewa Sultan yayi a hasale ya nufi toilet d'in murd'a kofar yayi zaune yaga Nihal tayi zaman yan' buri had'e rai Sultan yayi yace, "lafiya kikewa mutane ihu? Kuka Nihal ta saki tare da cewa, " fad'uwa fa nayi na kasa ta shi" hannu sultan ya mik'a mata a hankali ta daura lalausan hunnan ta saman na Sultan, k'ara ta kuma saki ta koma ta zauna tare da cewa, "na kasa tashi" tsaki Sultan ya saki ya k'ara had'e rai, a hankali Sultan ya duka tare da daukar ta cak kamar baby, suna fitowa daga toilet lokacin yayi dai-dai da shigowar jakadiya tun a parlour ta fara jiyo ihun Nihal shine ta shigo tana ganin Sultan dauke da Nihal ta wani diririce zuciyar ta, tayi fes tunanin ta komai ya auko musanmam yadda taga Nihal d'in ta wani zagaye hannun ta a wuyan Sultan, shi ko sultan had'e rai yayi kamar gaske yana Smile saboda yasan halin gidan Sarauta dama da gangan ta shigo dan taga ya sukayi daran jiya, saman bed ya dire Nihal, kunya duk ta kamata ko gaishe da Jakadiya ta kasayi, sosa k'eya Sultan yayi tare da cewa, "Dara ina kwana" Amsawa tayi tana wurwurga idanuwa tana kalle-kalle cikin dak'in kamar barauniya Sultan ne ya katse mata tunani da cewa, "Nihal bata da lafiya bari na dubata idan na gama zan kira ki se ku fita tare" toh jakadiya tace tare da ficewa tana dariya k'asa-k'asa tana cewa, "d'an tselankwa duk ya gama zagayan ana kaita har ya ware," Dara na fita Sultan ya maka wa Nihal harara yace, Malama sako min daga gado" shuru Nihal tayi kamar bata jishi ba ta cigaba da matsar kwalla tana cewa, "kafata da kuguna zasu cire" tana maganar tana yarfe hannu bedside drewar Sultan ya bud'e ya juro wani magani a tuf yace, "gashi ki shafa" amsa Nihal tayi Sultan kuma ya koma saman sofa ya juya mata baya se da ta gama shafawa sannan ya juyo sannan bud'e drewar ya ciro wata jigida ta gold yace, "tashi ki sa wannan" tsoke fuska Nihal tayi tace, "mi zanyi da wannan" had'e rai Sultan yayi yace aladar gida nan ce duk wadda ta shigo part d'in mijin ta rana farko dole tasa kuma ki kula min da abuna dan bake na tana darwawa ba, kin gane malama idan kuma bazaki sa ba zan sa maki da kai na" Nihal na jin haka ta amshi jigidar ta da kanta sannan Sultan ya mik'a mata wata gwon green me zana flowers ta saka sannan ya kama hannu ta tana ingishi har suka iso parlour jakadiya na zaune murmushi ta saki tare da kallan k'afafuwan Nihal tana sakin Smile se sannu take jera mata haka shima Sultan d'in kamar gaske sannan suka fice.
Chapter 42 · 0% Book details