← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 119 OF 128

Sashe 119

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gabaki dayan su zaune suke a parlour anata raha kallo daya zaka masu kasan suna cikin farin cikin wasu na fira wasu na shan coffee kowa cikin fari ciki yake maimartaba da waziri suna gefe suna hira, sultan kuwa yana makale da Nihal sai alama take mashi da ido saboda rashin kunyar dayake zubawa dan shi ko a jikin shi kamar ba su mom a wajan yarda yake mata sai kace ita kadai ce mai miji, har d'an bige shi take tana ture shi idan ya kawo mata hannu duk abinda ke hannu ta sai ya kai bakin shi ya cinye sai dariya su Ashad suke mata yarda sultan ke mata sangarta sai ka ce karamin yaro, bango kofar da kayine ya sasu juyowa lokaci daya suna kallan Sara dake bakin kofa tana kuka da sauri Nihal ta aje cup din dake hannu ta ta karasa gaban Sara, kuka Sara ta saki ta fada jikin Nihal a rikice Nihal tace, "me ya faru kike irin wannan kukan Sara, wani abu ya same ki bayan tafiyar ki gida? Nihal ta ida zancan tana kallan kofa ta talabo da fuskar Sara da tayi shabe-shabe da hawaye cikin sarkewar harshe Sara tace, "ban taba ganin wulakanci da cin mutunci irin na yau ba, ban taba tunanin akwai rana irin ta yau ba" Sara ta ida zancan tana tsana ta kuka Nihal da ta rude itama ji take kamar tayi kuka saboda duk wanda yaci mutucin Sara tamkar yaci nata ne, cikin kuka Sara ta ce, "Allah yayiwa Baffa rasuwa amma gawar shi ta kasa samun arzikin sutura, kowa tir yake da gawas Baffa da tofin alatsine a kanta" Sara ta ida zancan tana kuka durkushewa Sara tayi gaban Nihal tace, "tun a duniya Allah ya fara hukunta Baffa dai-dai da laifin shi amma na rokeki ki yafewa Baffa ko ya samu sasauci ki daure ki yafewa Baffa ko nauyin muta nan daya zalunta zai ragu a kan shi..! Nihal da hawaye ke gangaro mata da gudu ta bar wajan kuka Sara ta saki tana cewa, "yanzu Nihal baza ki yafewa Baffa ba, karki manta hannu ka baya rubewa ka yanke Nihal..! Da sauri Sara ta rarafa wanjan maimartaba tace, "na rokeka ran ka ya dad'e a taimaka ayiwa Baffa sutura wallahi muta nan gari sun ki amsar gawar Baffa dan Allah a taimaka ayiwa Baffa sutura" tausayin Sara lullube maimartaba yayi sosai mom ce ta daga Sara tana lallashin ta sannan su maimartaba suka fice dan zuwa yimawa Baffa sutura a kai shi makwancin shi.

Nihal na shiga daki saman bed ta fada wani irin kuka ya kwance mata tana jin da kamar wuya ta iya yafewa Baffa shi da gwoggo, dan iya kar cutarwa sun mata sun rabata da Abba da umma anya kuwa zata iya furta kalmar ta yafewa daya daga cikin su, kuka Nihal ta kuma saki wani bari na zuciyar ta na cewa da Abba na da rai da tuni ya manta ya yafewa Baffa saboda dan uwan ka dan uwan ka ne, kuma hannu ka baya rubewa ka yanke duk abinda Baffa yayi ma Abba ya tsaya anyiwa Abba sutura da umma, kamar an mintsine ta mikewa Nihal tayi ta jawo hijab din ta ta saka tana kokarin fitowa taci karo da sultan zai shigo wani irin dadi ya ji ganin Nihal din ta fito bude mata hannu yayi ta shige jikin shi tana sauke a jiyar zuciya a hankali sultan ya furta "Allah yayi maki Allah albarka, Allah yana san masu yawai ta yafiya ki daure ki kasance a cikin muta nan da Allah ke so ki manta duk abinda yafaru ki yafewa Baffa" Nihal da tayi lamo a fafadan kirjin sultan tana jin kalaman shi, dai tace komai ba sannan suka fice a tare.

Ganin maimartaba yasa yan gari fitowa suma ba duka ba tsili-tsili liman ya zo yana ta yan kame-kame haka akayiwa Baffa sutura aka mashi sallah aka wuce da shi makwancin shi Nihal kuwa ganin gawar Baffa ta girgiza Nihal tabbas Baffa yayi wulakantaciyar mutuwa har cikin zuciyar ta take ji ta yafe mashi duniya da lahira haka aka cigaba da zaman makoki.

Bayan sadakar uku su Nihal suka koma kano har da Dara aka bar Sara na kula da gwoggo kullun haukar gwoggo kara tsanine ta ke ba alamar sauki, haka Sara ke daurewa tana kula da ita dan ba karamar fama dake da gwoggo ba hauka take tuburan, saukin ta daya kama daga kan abinci har zuwa na sha ba abinda Sara ta nema ta rasa ta kara natsuwa da hankali tana mai cigaba da kulla da gwoggo.

Rayuwa ta cigaba da tafiya da dadi ba dadi wasu na fari cikin wasu akasin haka, Nihal kuwa sosai take samu kulawa da tatali wajan mijin ta yanzu haka cikin ta nada wata uku na Basmal wata shida tare suke renan cikin su, cikin gata da kulawa Nihal kuwa ta rasa wayafi wani nuna mata gata kama daga kan maimartaba har Gimbiya jalila wadda yanzu ta zubar da makaman ta musanman yarda taga darasi a kan Baffa wannan dalilin yasa ta natsu ta shiryu, Nazili kuwa tuni ta nemi gafara Nihal sun shirya, sai dai har yanzu ba ruwan ta da samari da kyar ta iya yaki da zuciyar ta ta cire san sultan a zuciyar ta acewar ta lokaci ne da Nihal zata samu gata da farin cikin, ba wace tafi dacewa da sultan sama da Nihal dama ba komai kake nema a duniya ka samu ba ta maida hankali ta kan kasuwancin ta dan ko zama batayi a kasar.

Bangaran karatun Nihal kuwa na tafiya yarda ya kamata yanzu haka shirye-shiryen zana wessce suke karatu suke ba kama hannu yaro dan ganin cewa sunci paper.

Nihal ce zaune saman three star a part din Ammi tana shan ice cream da alama tana jin dadi ice cream din musanman yarda take kad'a kai Ammi tana cewa, "bari dai sultan ya dawo ya same ki kina shan ice cream din nan yanzu ya fara fada," turo dan karamin bakin ta Nihal tayi tana cewa, "yanzu zan shanye kafin ya shigo ki dinga kallan min kofa Ammi,"
"ni ba ruwa na" sallama Ashad ne ya katsewa Ammi zancan gaishe da Ammi Ashad yayi tare da zama saman one star Ammi tace "yau ka dawo da wuri kenan? eh Ashad yace yana kallan Nihal yace, "big aunty dadi ake ta sha kenan? washe baki Nihal tayi tana kallan robar ice cream din dariya Ashad ya saki ya ce, "bari yaya ya dawo sai na tona kina shan sanyi bayan ya hana ki" zaro ido Nihal tayi can kuma ta saki dariya tana cewa, "kana tonawa nima gobe Monday ina zuwa makaranta zan bata maka wasa" Nihal ta ida zancan tana daga gira, zaro ido Ashad yayi yana cewa, "kar muyi haka aunty wasa nake maki kema kin san ba tonawa zanyi ba"
"na dauka da gaske" Nihal na magana tana dariya Ammi tace, "idan tayi tsami zamu ji na rasa mi ya aje a makarantar nan taki kullun sai ya zo nan gulma, yana maki ladabin yan kunama" dariya Ashad yayi Basmal da shigowar ta kenan ta ce, "ba kowa ke sashi ladabi ba sai..! da sauri Ashad ya toshe mata baki yana cewa, "to kazalaha me ya kawo ki nan part din ma for the first place," zame hannun ta Ashad Basmal tayi tana turo baki da tirtsetsan cikin ta tace, "toh kai me ya kawo ka? Basmal ta fada tana daga gira, "gaishe da Ammi ke kuma gulma ta kawo ki" dariya Basmal ta saki tana cewa, "ni ba shi ya kawo ni ba yaya dama chocolate cake nayi kuma nasan kana so shine na kawo ma naje part din ka baka nan na tanbayi momi tace min ka nan" Basmal ta ida zancan tana bud'e kwalin cake din washe baki Ashad yayi ya sa hannu ze ci Basmal ta balo ta bashi a baki yana ci har yana lumshe ido ya ce, "Darling kin kyauta kamar kin san na dade ban ci ba," murmushi Basmal tayi da cake din Basmal ta nufo Nihal da shi tana cewa, "kema ga naki"
"ki aje min sai na gama shan ice cream zan ci"

sultan ne ya shigo part din Ammi direct Nihal ya nufa Basmal sai alama take ma Nihal amma bata gani ba, rungume ta ta baya sultan yayi, har sai da Nihal ta razana saboda robar ice cream din dake Hannun ta, robar ice cream din da sultan ya ganine ya sashi hade rai tamkar bai ta ba dariya ba, amshe robar ice cream din yayi yana cewa, "wato na hana ki shan sanyi baza ki daina ba ko," shuru Nihal tayi tana raba ido a hankali tace, "am sorry bazan sake ba," sultan be ce komai ba ya kad'a kai tare da nufar Ammi yana cewa, "matar ya dai 2days naga sai wani fresh kike me sirrin far da ido Ammi tayi tace, "naki yin fresh tunda na sake miji, ni fa tuni na sake ku kai da Ammar saki uku uku na kama Ashad" dariya sultan ya saki yana cewa, "kin saki rashe kin kama ganye" dariya parlour aka dauka, Ashad na cewa, "kai yaya banda hadi mikake fadawa ammi wallahi bishiyar gabaki daya ta kama ba ganye ba" dariya kawai suke zubawa cikin fara'a amma har a lokacin sultan yaki kallan Nihal dan fushi yake da ita kan sanyin da take dirkawa kanta, salan ta samama baby su ciwan sanyi Nihal na lura da yanayi sultan duk sai taji bata kyauta ba tunda ya hanata ya kamata ta bari amma cikin nata ne yana masifar san sanyi, ita kanta tana mamakin yarda take ba sanyin mahimmaci yanzu ko bacci zasuyi sai ta kura AC koda sultan ya rage cikin dare sai ta lallaba ta kara.
Chapter 119 · 0% Book details