← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 128

Sashe 71

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

A cikin dajin motar sultan ta faka da sauri Sultan ya bud'e murfin mota ya fito DPO Bilal na kwalla mashi kira ko saurara shi beyi ba ya nufin gidan suka bishi a baya, DPO Bilal ne ya sha gaban sultan yana cewa, "Sultan ya kamata mu bi komai hankali be..! matsar da DPO Bilal yayi ya shige gidan zuciyar na tsana ta bugawa da karfi a hankali yasa hannun ya bud'e kofar gidan ya shiga, da kayan maye ya fara cin karo wuce parlour sultan yayi yana cewa, "Nihal..! Nihal..! da karfi yana bud'e daku na gidan a haka har ya karasa dakin da aka kule Nihal hijab din ta kawai ya gani da igiyar da aka daure ta, amma gida wayam ba mutane dukewa Sultan yayi kasan wajan hawaye Masu zafi na bin kuncin shi yana cewa, "Nihal duk Nina ja maki wannan wahala kwata-kwata baki dace zama da mutum irin na ba..! sultan yana maganar yana kuka haka sultan ya rinka sanbatu DPO Bilal ne ya riko Sultan dan da karya suka iya banbare shi daga gidan yana duke yana kuka rike da hijab din Nihal kamar karamin yaro, haka suka tura shi cikin mota yana suraitai kafin ka ce min zazzabi me zafi ya saukowa sultan haka suka karasa da sultan hotel kaitsaye daki aka kai shi aka kwantar da shi Ammar yaduba shi tare da yi mashi allura sannan ya kara mashi drip saboda rashin cin abinci da yake, Sultan na kwance hawaye na bi masha fuska yana sauke ajiyar zuciya jefi-jefi a haka allura baccin da Ammar ya mashi ta fara aiki a hankali bacci ya fara fizgar shi har bacci ya dauke shi.

A dai-dai kofar wani gida na katako ginin turawa cikin daji gidan yake ba motsin kowa se kukan tsintsaye dana shanu dake tashi motar su Tj ce ta faka, BS ya dauki Nihal a kafad'a ya shiga da ita gidan tare da shin fid'e ta saman kujera, Tj da shigowar shikenan harara ya maka wa Nihal kamar tana ganin shi yace ma BS, "dauke min wannan abar ka kai min ita ciki na tsani ganin ta wallahi, Nazili ta had'a ni da aiki gashi na kira wayar ta dan wulakanci taki dauka mtsww" simi-simi BS ya dauki Nihal ya shige da ita daki ya fito ya kule ta, a hankali Nihal ta bud'e lumsasun idanuwan ta dafe da goshi jikin ta yayi rau saboda zazzabin dake damun ta a haka ta mike kamar yar'maye tana bin bangwan dakin haskyen dakin Nihal ta kuna tare zuwa bakin window dakin tana jijigawa tana kuka tana cewa, "se na fita daga gidan nan" amma ta kasa bud'ewa se ma yankewa da Nihal tayi yar kara ta saki tare da kama hannun tana kallo babu abinda ya fadowa Nihal a rai se sultan duk rigimar da suke baya bari ta shiga wani hali tunawa tayi da ranar da ta bige da center table sultan duk ya bi ya damu ko ba komai Sultan na da kirki share hawayan ta Nihal tayi ta jingi da bango a hankali bacci ya fara dauka Nihal tana rawar sanyin.

*Washe gari*

A hankali sultan ya bud'e idanuwan shi gami da zame blanket din jikin shi drip din da ya gani makale Hannun shi ya cire tare da sauke santala-sanlata kafafuwan kasa, kwata-kwata be jin kwarin jikin shi a haka ya mike ya nufi toilet har ze shiga ya sauke idanuwan shi saman center table dake dauke da tray din abinci saman, kallo daya yayi ma abincin tare da kauda kai ya shige toilet cikin kwamin wanka ya shiga ya lumshe idanuwan shi yana tuna abubuwan da suka faru jiya, a haka dai har ya kamala wankan ya fito sanye da bathrobe direct dressing mirror ya nufa ya shafe jikin shi da lotion sannan ya dau ash suit din shi da Ammar ya aje mashi saman sofa haka dai ya shirya babu wata walwala fatan shi daya yayi tozali da Nihal yana gyara necktie din shi aka turo kofar dakin a hankali ya dago ya sauke idanuwan saman fuskar Ammar da ya shigo, cikin sanyi murya Ammar yace, "ka tashi lafiya,? shuru sultan yayi dan be da amsar tanbayar da Ammar ke mashi wani irin ya tashi lafiya bayan yau kwana daya da bacewar yarinyar mutane har ya gama shiryawar shi be ce ma Ammar k'ala ba yana kokarin fita Ammar ya ruko hannun shi yace, "sultan ko break ba kayi ba ya kamata ka sama cikin ka wani abu be kamata ka zauna da yunwa ba please k a ci wani abu,"
"Ammar bana san cin komai bana jin yunwa,"
"kawai ka fada ne amma kana jin yunwa sultan jiya fa tea kawai ka sha bayan nan baka kara cin komai ba, I can't allow you with an empty stomach please ka daure ka ci wani abu" da ban baki da komai Ammar ya zaunar da sultan ya hada mashi tea mai kauri ya mika mashi tare da tura mashi plate din chips kad'an sultan ya ci abincin ya aje.

******

Turo ma Nihal plate din abincin BS yayi kallan abincin Nihal tayi tare da kauda kai wasu hawaye masu zafi suka sulalu mata a zuciyar tana cewa wannan wace irin rayuwa ce yaushe ne zata samu *SAUYIN RAYUWA* hannu tasa ta goge hawayan fuskar ta da bayan Hannun ta tsaki BS ya saki yana cewa, "ka ji min shegiya kin samu an kawo maki abincin ma har wani kauda kai zakiyi, oh ba irin shi kike ci ba ko, idan baza ki ci ba se in cinye dama wanda na ci be isheni ba," wayar shi dake ruri ce ta katse mashi tunanin sunan Nazili da ya ganine ya sasa ficewa da sauri dan ya mikawa Tjee zaune a parlour ya sami Tj tare da mika mashi waya yace, "Nazili ce..! hannu Tj ya sa ya amsa tare da cewa, "hello..! Nazili dake zaune Aziza na mata massage tana sanye cikin sleeping robe din ta white tace, "Tj Allah yasa lafiya ina tashi naga miss calls naka na kira wayar bata shiga ba," tsaki Tj ya saki yana cewa, "ke dai bari Gimbiya" nan da nan ya kwashe abinda ya faru ya fadawa Nazili mikewa tayi tsaye tana cewa, "amma dai anyi matsiyaciya idan ta san wata bata san wata ba, zan turo ma number sultan ka kira shi ka fada mashi inda kuke ka ce ya kawo 20 million kar ya zo da police yana zuwa ku kashe Nihal din a gaban shi ka ga shikenan na huta kuma kun huta" dariya Tj ya saki daga dayan bangaran yana cewa, "Gimbiya kin fini mugunta nima na so na gama da ita amma ba'a gaban shi ba amma tunda kin ce haka, to hakan za'ayi kin ga daga nan ze fidda rai a kanta tunda yaga gawar ta..! murmushi Nazili ta saki tare da katse wayar hannu ta tana murmushi a zuciyar ta tana cewa lokaci yayi da Nihal zata bakunci lahira ko tana so ko bata so dole da barmin sultan, sultan nawa ne ni kad'ai murmushi ta kuma saki tare bazar da gashin kanta sannan tace, "Aziza had'e min ruwan wanka yanzu zan fita ina da meeting" murmushi Aziza ta saki tare da shigewa toilet da sauri dan had'ewa Nazili ruwan wanka.

**********
Chapter 71 · 0% Book details