← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 128

Sashe 58

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Part din sultan Nihal ta wuce koda ta shige baya part din bathroom ta shiga ta watsa ruwa sanye da bathrobe ta fito kanta nanade da towel goge jikin ta tayi tare da shafa lotion me kamshi, shiryawa Nihal tayi cikin wata yellow gwon me dogwan hannu rigar na dauke da manyan flowers White, Riga ta mata kyau sosai ta kama jikin ta ga hips d'in ta daya fito d'as da shi na Fulani ta kamar su fasa gaban rigar su fito sakin gashin kanta tayi ya zubo har gadan bayan ta duk da ba wata kwaliya tayi ba tayi kyau sosai kamar ita tayi kanta, har zata fita ta hango wayar Sultan dake saman bedside drawer da sauri tasa hunnu ta dauka tare da bud'e Jakarta ta Ciro takada da aunty Aisha ta rubuta mata number ta Allah yaso wayar ba key, numbers din ta kwafa tare da kira ringing wayar ke tayi ba'a dauka ba Nihal se addu'a take Allah yasa a dauka katsewa tayi sannan ta kuma kira a karu na biyu, fisge wayar da akayi ne yasa Nihal dagowa a razane Sultan ne ya amshe wayar ran shi a had'e tare da karasa a kunne, mijin aunty Aisha dake zaune saman kujera ringing ya isheshi kuma aunty Aisha na kitchen hannu yasa ya dauka tare da karawa a kunne yace "hello! Hello! Sultan dake bin Nihal da kallo ya daskare waje daya yana wasu hadiye-hadiye zuciyar shi na tsanata bugawa yana jin wani irin zafi Wanda be taba jin shi ba, shuru yayi be ce kala ba har mijin aunty Aisha ya gaji da cewa hello ya kashe wayar zame wayar Sultan yayi a kunna shi ya tsare Nihal da ido yana hadiye-hadiye can kasan makoshi sultan yace tare da kankance idanuwan shi, " wanene wanda naji kina waya da shi kuma da waya ta! Sultan ya jefa wa Nihal tanbayar yana mai kara matsowa daf da Nihal, tsare Sultan da ido Nihal tayi tana kallo, tare da furta "wani kuma ni ba wani na kira da wayar ka ba" Nihal ta ida zancan tana kokarin rabawa ta gefan sultan ta wuce, daka mata tsawa sultan yayi yace, "Idan ina magana ba'a juya min baya! tanbayar ki nake wanene shi wannan da kike kira? ya fad'a a taikaice shuru Nihal tayi tana raba ido can kuma ta had'e rai tace, "wani kuma ai na fada ma ba wani na kira ba" Nihal ta ida zancan tana tsare Sultan da ido sultan yace, "Oh ko toh murya wa naji kike nufi? had'e rai Nihal tayi tana kokari rabawa ta gefen sultan ta wuce fisgo ta Sultan yayi ta fad'a saman fafad'e kirjin Sultan taga-taga suka tafi tare da fadawa saman bed rintse ido Nihal tayi tare da ware su saman kyakyawar fuskar Sultan gashin kanta ya rufewa Sultan fuska a hankali sultan ya sa hannu ya matsar da gashin tare da daura idanuwan shi saman fuskar Nihal kasa Nihal tayi da idanuwan ta, duka hannu ta na bisa fafadan kirjin Sultan kafe ta sultan yayi da ido yana bin kyakyawar fuskar Nihal da kallo ba komai ya fi tafiya da imanin Sultan ba se pink lips din ta lumshe ido Sultan yayi wani bakwan Alamari na shigar shi lokaci daya a hankali suke sauke numfashi, sun dau lokaci mai tsawo a haka a hankali sultan ya bud'e jajayan idanuwan shi ya sauke su kan Nihal data ware idanuwan ta, da sauri Nihal ta zame jikin ta zata sauka janyo ta Sultan ya kumayi ya matse ta ajikin shi, yar kara ta saki me cike da shagwaba can kasan makoshi kamar mai rad'a yace, "wanene kika kira da wayata? Sultan ya tsare Nihal da idanuwan shi wayanda suka rine ja shuru Nihal tayi tana mutsu-mutsu dan sultan ya sake ta, wata irin kasala ta sakarwa sultan lokaci daya kara matse ta yayi cikin jiki shi yana shakar kamshin ta me riki tashi, cike da tsiwa Nihal tace, "ka sake ni! ta ida zancan tana turo baki hannu Sultan yasa ya murd'e mata baki ihu Nihal ta saki tare da fashewa da kuka kwata-kwata Sultan be damu da kukan ba yace, "tanbayar ki nake ba kuka na ce kimin ba, dawa kike waya? ya nanata mata tanbayar yana tsare ta da ido ciki kuka Nihal tace, "to ka sake ni se na fada maka" can kasan makoshi sultan yace, "bazan sakeki ba se kin fada min dawa kike waya first" ya ida zancan yana kafe Nihal da ido da kyar Nihal take sauke Numfashi saboda matse ta da Sultan yayi a jikin shi, Nihal tace, "kanwar umma na kira" murmushi rainin hankali Sultan yayi yana matsar da gashin Nihal daya rufe mata fuska yana cewa, "Amma naji murya namiji! kuma sannan bani da labari cewa kina da wasu family" sultan ya ida zancan cikin kakausar murya rintse ido Nihal tayi tare da toshe kunne tana kuka tace, "Ni fa gaskiya na fad'a ma! da kyar Nihal ta fisge jikin ta tare da cewa cikin masifa, "danna ce ni almajira ce ba shi ze baka damar kallo na mara asali da tushe ba kamar yadda kake fadi, idan baka sani ba yau ka sani saboda su na zo birni, ba saboda na zo na zama matar ka ba, har ka samu damar kallo na mara tushe" Nihal ta ida zancan tare da ficewa daga dakin, Shuru Sultan yayi zuciyar shi nayi mashi suya mi yasa ma ze damu dan tana waya da wani wata zuciyar tace saboda matar ka ce, dole ka kare hakkin aure, wayar shi ya janyo tare da kallan number danna number yayi da niyar kira kuma se ya fasa tare da yin wurgi da wayar ya lumshe ido.

Aunty Aisha da fitowar ta daga kitchen kenan tana smile mijin ta yace, "honey yanzu nan aka kira ki da new number na dauka shuru ba ayi magana ba"
"May be network ne kasan haka suke"
"Bana tunanin haka ki sake kira ki ji" to Aunty Aisha tace tare da cigaba da cewa, "my love muje muyi lunch anjima ni da yaya sani zamu je police station kan maganar Nihal dole tanimu ya gane kuran shi na wufintar da Nihal da yayi" karawasa dining sukayi Abubakar na cewa, "Allah dai ya kyauta my dear, wani lokacin se ka rasa ina imanin muta ne yake zuwa Allah ya bayana ta" amin aunty Aisha tace tana feeding din mijin ta jallof din cuscus haka suka rinka maganar Nihal da yadda za su shawo kan alamarin.

*********

Basmal da Nihal ne zaune a garden saman grass carpet suna lisafa abubuwan da za'ayi da biki dan har program zasuyi kala-kala, murmushi Basmal tayi tana cewa, "Aunty na! na ji dadi sosai da kike bani sports naki," murmushi Nihal tayi Basmal ta cigaba da cewa tana lumshe ido hannu ta na rike dana Nihal, "Aunty zan kasan ce da fari ciki na soon na san nima ya Ammar ze bani kulawa kamar yadda yayana ke baki, soyayyar ki da yayana yana birge ni aunty cikin fa d'ankakanin lokaci kuka fara soyayya gashin har kun shaku" Basmal ta ida zancan tana washe baki tana tsare Nihal da ido murmushi yake Nihal tayi tana cewa, "Um! Tsakin da aka saki ne yasasu dagowa Nazili ce sanye ciki gown light brown dai-dai gwiwa tayi parking gashin kanta hannun ta dauke da newspaper zama tayi sama resting chair tana cewa, "Basmal ya kamata ace duk programs din bikin ki ki samu Wanda ya san kan abubuwa, ma'ana masu ilimi wayanda suka dade cikin shi," ta ida zancan tana gefa wa Nihal kallo me cike da tsana tana mai cigaba da cewa, "sister bana so ki rinka shawara da gidadawa, na san kina da friends wayayu ya'ya manya ba ya'ya almajirai ba, idan ko kika ce da ya'ya almajirai zaki rinka shawara bikin ki ba ze bata light ba, karki manta bikin diyar sarki za'ayi ba bikin almajira ba mara tushe ko asali" na Nazili ta ida zancan tana kallan Nihal tana murmushi tare da bud'e newspaper tana cigaba da karantawa, jiki Basmal ne yayi sanyi bata ji dadi abin Nazili ta fada ba kamar gasawa Nihal magana take cikin magana, daura hannuwan ta Basmal tayi saman na Nihal tana yak'e tace, "aunty na kiyi hakuri haka halin ta yake ba wai ta fada bane saboda cin fuska" Basmal ta ida zancan tana kwabe fuska, murmushi Nihal tayi tana cewa, "dama ni ban dauke shi wani abuba, tunda na zama matar sultan bani da wata damuwa ko Bacin rai ko da an bata min da muje bedroom ze faran ta mi shiyasa a kullun yaya ki ke samun guri na musanman a zuciya ta" Nihal ta ida zancan tana murmushi tana kallan Nazili, Wanda ta cika fam fuuu ta tashi ta bar wajan tana aikawa Nihal mugun kallo.

```Taku har kullun salma mas'ud nadabo```
[1/7, 2:29 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
*Story*
*And*
*Writing*✍🏾
*By*
*Salma mas'ud nadabo*👑

🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
(```We are the best among the rest```)

*Page: 89_90*

*ONE WEEK LETTER*

Bayan sati daya abubuwa da yawa sun faru ciki har da shirye-shiryen exam da Nihal keyi duk wani abu daza ta bukata Sultan ya tanadarmata su.
Chapter 58 · 0% Book details