← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 128

Sashe 6

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ƴan mata da saukar da farantin gyaɗar kika yi sai muyi magana ko" fari tayi da idanuwan ta, tare da juya dan ƙugunta kamar marƙin lema ta duka, "yauwa ko ke fa nawa-nawa gyaɗar" yana faɗar zancan tare da kallon fuskar ta wadda taji hoda kamar an tono ta daga ƙasa, cikin kissa da kisisina tace, "naira biyar biyar," haka Tanimu ya zaro naira goma ya ba ido tare da jan ta surutu kasancewa ido irin yaran nan ƴan talla masu bin maza har suyi masu juye shiyasa ta saki jiki da Tanimu tana mai malƙwashe-malƙwashe, kuma dama tunda ta ganshin taji ya kwanta mata a rai.

Basu rabu ba har sai ta kwatanta mashi gidan su sannan yayi mata alƙawarin idan dare yayi zai zo zance, shi ko Habu mamakin irin wawtar da yayan nashi yayi yake dan shi ko a cikin kayan miya yaga mai kama da ido tsame ta zaiyi ya zubar, ko da yake hausawa sun cewa shan koko ɗaukar rai.

Tun daga wannan rana soyayya mai ƙarfi ta shiga tsakanin Tanimu da ido dan kusan duk kauyan ba Wanda be san soyayyar da ido ke zubawa da Tanimu ba, magana har taje ga iyaye, ko da Inna ta ji labari taji daɗi sosai koma dai yayane Tanimu zaiyi hankali amma ta so ace ya samu wadda tafi ido natsuwa da tarbiya, amma yaran yanzu baka iya masu shiyasa taja bakin ta tayi shuru tana fatan Allah ya tabbatar da alheri.

Habu ko babu abinda yake samu sai cigaba dan yanzu haka ya koma shanono da aikin kanikanci, duk wata mota ko mashin da zaizo daga birni talalace sai an kira habu injiniya sannan zata tashi cikin ikon Allah dan ya samu kuɗi sosai don yanzu haka yana da tumakai da yawa da ake mai kiwo da su a shanono, yanzu haka ya tare a shanono a ɗakin maigidan shi Balele, zaman lafiya suke sosai da Balele, gashi Balele mutumin kirki ne, sannan Allah ya ɗaura mai san Habu shiyasa Habu ke jin daɗin zama da balele.

Malam ko da labarin soyayya Tanimu ta same shi, cikin Gona kin shi ya dau ki daya yaba Tanimu sannan ya haɗa shi da dabbobi yayi kiwo, dan ya fara cin gashin kan sa tunda yanzu Shi ba yaro bane, Tanimu ko yaji daɗi haka sosai ko ba komai ya mallaki wani Abu daga gonar mahaifin shi.

*Bayan Watanni Uku (3)*

Shirye shiryen bikin ido da Tanimu ake kowani ɓangare ka leƙa hidimma ake.

Ɓangaran ido ko duk ta ruɗe saboda ta ɓarar da budurcin ta tun a wajan talla, shiyasa duk hankalin ta, a tashe yake.

Kamar kullun yauma tana ɗaki ta zabga uban ta gumi tani ta shigo, tana ta doka sallama amma kamar bayi take ba har sai da ta taɓo indo tace, "ke lafiyar ki kuwa indo kin zabga uban ta gumi, ke ɗaya kamata a gani kina murna indo,"
taɓe baki indo tayi tace, "ke dai bari Tani kema kin san ta tsuniyar gizo bata wuce ƙoƙi ke kan ki kinsan ba yau na fara bin maza wajan talla ba, gashi satin biki na ya matso, ban san da wace fuska zan kalli Tanimu ba, idan aka kaini gidan shi."

Tani ce tayi shewa tace, "yanzu saboda ɗan wannan abun kike tada hankalin ki Indo, to bari ki ji yanzu haka cikin gare ni, kuma ko za'a ɗauramin wuƙa a wuya bana iya cewa ga uban dan ko yar saboda kullan cikin harka nake, ki kwantar da hankalin ki dama yanzu gidan mai tafasa zani ta kulo min maganin zubar da ciki, sai muje tare idan akwai magani gyarawa ai sai a gyara nasan baza a rasa ba, tunda tasan har kar" shewa suka ɗauka tare da kashewa ido ta dauko maliliɓin ta suka fice da Tani.

Sun kuwa yi sa'a suna zuwa mai tafasa taba Indo kayan matsi wanda duk nacin mutum ba zai ya gano ta taba lalata ba, ita ko tani a nan aKa haɗa mata magungunan ta sha ko Minti goma ba tayi da shan maganin ba ta fare murqususu sai ga bari sannan suka curo mata kudin ta cas suka kamo hanyar gida cike da farin cikin.

Balele ne ya shigo ɗakin su da alamar gajiya a tattare da shi Kallon Habu yayi yace, "ina zuwa kuma Habu,? murmushi Habu ya saki yace , "kamanta jiya na sanar da kai gobe ake ɗaurin auran yaya na Tanimu ,"

"Kai amma Allah yasanya alheri wallahi na manta naso ace naje bikin ko dan yadda kake ji da yaya Tanimun nan," faɗaɗa murmushi Habu yayi yace, "ba komai oga ai nasan dalilin daya hana"
"toh shikenan ga dubu Biyar ka bashi gudumowa ta,"
"ah yallabai har da ɗawainiya ai ba komai duk yima kai," godiya habu yayi sosai sannan ya kama hanyar zuwa ƙauyen su.

Ko da ya isa gida cike yake da ƴan biki duk sun hallara, da zuwansa bai ko huta ba yaya Tanimu ya shiga tanbaya Inna tace mai yana ɗakin dake kusa da waje nan zai gyara masu shida matar shi , kai tsaye ɗakin ya nufa, cikin daya ne sai dai babban ne sosai sannan gefen ɗakin akwai dan ƙaramin ɗaki wadda bai kai Girman wancan ba, ko da Habu yaga gyaran da akayiwa ɗakin bai mai ba dan haka ya ciro kuɗi masu yawan gaske ya ba masu gyara su gyara ɗakin ya fito sosai, Tanimu sai gadiya yake, duk da shi za'ayiwa aikin sai da yayi hassada da baƙin cikin yau habu ya fishi abun hannu, sannan ya bashi gudumuwar da ogan shi ya bashi, shima ya ƙara masa goma akai.

Masha Allah ɗaki yayi kyau duk Wanda ya kalli ɗakin sai ya yaba da namijn ƙoƙarin da Habu yayi wajen kashe maƙudan kuɗaɗe.

*Washe Gari*

A yaune ɗunbin mutane suka sheda ɗaurin auren *Muhammad (Tanimu) Ja'far* *Da Aisha (Indo) Kabiru (Malan Bala)* sai dai muce Allah ya bada zaman lafiya..

```Taku har kullun Salma Mas'ud Nadabo ```✍🏻🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊

💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞

*Story*
*And*
*Writing*✍🏽
*By*
*Salma Mas'ud Nadabo*👑

*Edit by*:
*Aliyu Miko Muhammad*

https://mobile.Facebook.com/Real-hausa-fulani-Writers-forum-RHFWF-17394973194167/?refid=52&red=opera-speed-dial&-tn_-H-R

*Email*:[email protected]

*Facebook*:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.com

*Page:15_16*

*A gaskiya ina jin daɗin yadda kuke comment kan wannan labarin wannan shafi naku ne masoyya SAUYIN RAYUWA ina yin Ku irin sosai ɗin nan* ❤

An kai amarya ɗakin mijin ta lafiya, inda Tanimu ya zuba wa amaryar sa soyayya duk da gaban Indo yana faɗuwa saboda bata da tabbacin maganin mai tafasa yayi aiki, jin Tanimu bai mata magana ba, kuma bai mata Kallon banza ba yasa ta sauke ajiyar zuciya ta cigaba da zuba masa shagwaɓa.

Kafin Habu ya koma shanono sai da ya tabbatar yasa su Hassan a makarantar boko tare da siya masu sabon keke, sannan ya tabbatar masu da cewa, idan suna da matsala su same shi a gareji inna tayi murna sosai da jin daɗin irin yadda Habu ke kula da ƴan uwan sa, sannan ya siyowa Haulatu kayan wasa kafin itama lokacin fara zuwa makarantar ta yayi, bai tafi ba sai da ya aje masu shatara na arziki, Malam sanya masa al'barka sosai, ba'a wani jima ba Habu ya koma shanono.

Ko da ya koma shanono aikin tuƙuru yake yana samun buɗi don yanzu har mashin ya siya mai kyau na zamani,

Bangaran amarya da ango ko sai zuba soyayya suke yayin da Tanimu ke tattalin Indo ita kuma tana ƙara narke masa, tunda akayi auren ya rage zuwa gona da kiwo, malam ko zuba masa idanuwa yayi har sai ya gama cin amarcin sa.

Kwanci tashi asarar mai rai yau dai Indo tashi akayi da masassara ko tsakar gida ta kasa fitowa, shurun da Inna taji ne ya sata, leƙa ɗakin kwance ta hango Indo sai kyar ma take inna ce tace, "a'a Indo ba lafiya ne" ta ƙaraso ɗakin tare da taimakawa Indo har sai da Indo taji dama-dama sannan Inna ta fita, ta damomata fura ta kawo mata, kurba ɗaya zuwa biyu tayo aman ta saboda tashin zuciyar da take fama da ita, inna ce ta gyara gurin tsaf ta taimaka mata da ruwan wanka, ko ba'a fada mata ba ta gano Indo juna biyu gare ta, wani irin daɗi ne ya lulluɓe Inna dan haka ta zage tana tattalin Indo, ko da Tanimu ya dawo Inna ta bashi labari ya ji daɗi sosai yayin da ya cigaba da kulawa da Indo.

Kamar kullun suna zaune a tsakar gida Indo na gefe tana Kallan su Hassan yana karatun boko sai taɓe baki take, sallamar Habu ce tasa yara miƙewa da sauri suka rungume shi hannu shi dauke da baƙaƙyen ledoji, Indo ce ta kwaɓe baki tana zancen zuciya, "hmm aikin banza kawai da yake shi yana da abin duniya tunda ya dawo ai dole su rinƙa rawar ƙafa a kanshi shi kuma Tanimu ko irin kishin nan beyi," Habu ne ya katse mata tunanin da cewa, "yaya ina wuni mun same ku lafiya," washe baki Indo tayi tace, "lafiya lau Habu" yar baƙar ledar dake hannu sa ya miƙa mata "gashi wannan naku ne" "a'a har da mu a tsarabar Habu aiko mun gode" "ba komai yaya" jin irin godiyar da Indo ke zubawa Habu ne yasa Inna fitowa tana washe baki, "Habu sannu da zuwa," "yauwa Inna" sannan yabi inna ɗaki shida yara aka bar Indo a tsakar gida dogon tsaki taja tare da shigewa ɗaki ta wurgar da tsarabar cikin ɗaki.
Chapter 6 · 0% Book details