← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 128

Sashe 32

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amir na shigowa part d'in Sultan ammar ya fad'a jikin shi tare da sakin kuka yana cewa, "zasu kashe min Sultan wallahi na rasa Sultan na rasa good friend" kwalla dake idanuwan Amir yasa hannu ya goge yana shafa bayan Ammar yana cewa, "haba aboki na bi a strong man mana insha Allah Normal ze tashi ai Sultan namiji ne" Alex da kuka ke Neman kubuce mashi ne da sauri ya bar part d'in Sultan yana goge hawayan shi, kafin kace mi Ammar da Amir sun fara bama Sultan taikwan gagawa, banko kofar da kayi ne yasa Ammar d'agowa bashir ne tsaye murmushi Ammar ya saki yana cewa, "Leda nawa na jini ka bada bashir? yace "biyu! aje lider k'arin jini bashir yayi tare da k'arasowa ya taba jijiyar Sultan na hannu d'aga masu ammar hannu yayi alamar komai na tafiya dai-dai cigaba su kayi da aikin su cikin ikwan Allah suka kamala aikin sannan aka daura mashi k'arin jini, komawa gefe suka yi tare da zaunawa suna duba agogo, kowa cikin su fata yake Sultan ya mik'e lafiya lau.

*****

B'angaran Nazili ko business d'in ta na tafiya yadda ya kamata company d'in ta se k'ara samun cigaba yake, ta k'ara kyau tayi fresh wayewa se abinda ya k'aru musanman taje inda take da freedom amma se dai tunanin Sultan ya hana ta sakat da shi take kwana tana tashi, san shi se lunkuwa yake a zuciyar ta, duk ta matsu ta gama aikin ta dawo Nigeria taga sanyin idanuwa ta babba damuwar ta ko ta kira shi se yaga dama yake dauka, lumshe idanuwa Nazili tayi tare da ware su saman pic d'in dake manne a d'akin ta, iyayan tane murmushi ta saki tare da cewa, "I miss u," duk da iyayan Nazili sun rasu hakan baya hanata sauka gidan su idan ta zo uk, mahaifiyar Nazili baturiya ce sun had'u da k'anin maimartaba ne sanda ya zo karatu soyayya me karfi ta shiga tsanin su, sakwamakwan Auran su yasa family d'in mahaifiyarta musulinta , mamar ta na haihuwar ta, ta rasu haka Abban ta ya rink'a kula da ita yaki aure tana da shekara 14 mahaifinta shima ya rasu haka yasa ta dawo Nigeria hannu maimartaba yana kula da ita, tunda ta kyala idanuwa ta kan Sultan ta kamu da San shi, shi kuma matsayin kanwa ya aje ta kamar su basmal haka yake ganin ta sauke ajiyar zuciyar tayi Tara da kallan k'anwar mamatar lusi wadda ta dafa ta, murmushi lusi ta saki tare da cewa, "ya dai my baby" murmushi Nazili ta saki tare da cewa, "lafiya lau," zama lusi tayi tana cewa, "kin ki zuwa ki auri family d'in mahaifiyar ki ko Nazili? dariya Nazili ta saki tare da cewa, "Sultan yafi min kowa shi nake so shi nake tunani," tabe baki lusi tayi tana bin Nazili da kallo, car key d'in ta Nazili dauka tare da fita daga gidan.

***

Wata hadadiyar daguwar riga Dara ta dauko light blue se alkyabba dark blue tasha aiki da gold zare, cikin natsuwa ta shirya Nihal nanad'e mata gashin ta akayi ya zubu har gadan bayan ta bakin Nihal ko ya kasa rufuwa saboda kauyanci da murna, make up aka mata sosai sannan aka sa mata alkyabba tayi kyau sosai, wuyan nan nata yasha sakar gold hannu ta ko yasha zoben gold, tare suka fito da Nihal ammi dake saman kujera ce ta bud'e baki tana cewa, "masha Allah" gabaki d'ayan yaba kyan Nihal suke ammi tace, "Ku kaita wajan gimbiya Nadiya ta sa mata albarka," bayi na biye da Nihal tana tafiya a hankali har suka k'arasa part d'in umman Sultan Se da Gimbiya ta masu iso suka shigo a lokacin maimartaba ya bar part d'in murmushi mom ta saki tare da kallan Dara ta mike tsaye Gimbiya ta bin Nihal da kallo, zubewa Nihal tayi tana kwasar gaisuwa murmushi mom tayi tare da cewa cikin muryar ta mai dad'i da mulki tace, a bud'e mata fuskar Nihal wadda ke sunkuye cikin hula alkyabba a hankali Dara ta bud'e fuskar Nihal murmushi mom ta saki tare da d'ago da habar Nihal ta furta "masha Allah" da yaba kyau na Nihal, mom tace, "Na ba kyautar gold" mom ta fad'a tana kallan Dara sannan tace, "na k'ara mata bayi mata uku, wannan zab'i yayi ina nan shigowa na kawowa Ammi gworan godiya mun amsa hannu bibiyu" dariya Dara tayi me sauti, shuruka da Nasim da minal dake tsaye gafe d'aya a hankali Dara ta shiga nuna mata su da matsayin su, jikin Nihal ne yayi sanyi saboda alamarin su Ammi ya fara bata tsoro gaban ta se dukan uku-uku yake bata k'ara rudewa ba se da ta ga duk d'an da ka ce mashi ga Sultana se ya washe baki tare da kissing hannu ta, Nihal ji tayi kamar ancire mata laka, kyaututuka mom ta dauko da yawa taba Nihal tare da cewa, "na sa albarka a wannan abin jiki na na bani Alheri ne," murmushi Dara tayi tare da ruko hannu Nihal suka fita wadda ta kasa gane inda zancan nasu ya dosa.

A hankali yake bude idanuwan shi abinda ya faru dashi ne ya dawo mashi kamar yanzu akayi, a hankali ya maida idanuwan shi tare lumshe su yana nazari duk da kanshi na sara mashi, yana cewa yaushe ne ze samu peace of mind, ya kusa wata ba a kawo mashi hari ba, ta hanyar wa aka samu damar shigowa wajan wasa da dawaki, Nihal ce ta fado mashi a rai, tabas wannan yarinyar ce ta shigo yau cikin gidan kenan aiko ta akayi Dan taga bayan shi saboda ita ka dai ce ta shigo Bak'uwa, da ita akayi anfani aka shigo gidan kenan tana da had'in baki da masu cutar da shi acikin gidan tsanar Nihal ce ta k'ara ratsa zuciyar sultan da duk wata mace, ganin tunani na Neman dawo mashi da ciwo sabo yasa sultan ware idanuwan shi a hankali, ammar dake bakin gadan ne ya saki murmushi yana cewa. "Sultan ! murmushi Sultan ya saki da sauri Alex da Amir suka k'araso da bashir rungume Sultan sukayi suna murna shima dariya yake Dan ya kwantar masu da hankali.

Tsaki gimbiya Jalila ta saki tana cewa, "har yanzu ban fara jiyu sautin kukan Nadiya da Ammi ba ya kamata a binci ko mana gaskiya"
"Ki kwantar da hankali ki Gimbiya ni nasan an buga mashi iccan se dai in rufa-rufa za'a mana"
"Toh shikenan ki fita kije ki binci ko mana ya ake ciki Dan na fara gajiya da jiran gawar shanu" da Sauri yakumbo ta fita Dan itama tana so taji k'arin bayani.

Kwana biyu Sultan ya kwashe yana jinya ya warware sosai su Ammar sun ji dad'i Dan suke bashi kulawa har ya warware, kwata-kwata basu bari labari ya je cikin gida ba, se dai duk Wanda ya zo Neman Sultan se ace mashi yana wajan aiki haka suka rink'a rabawa su Gimbiya jalila hankali in ranta yayi dubu to ya baci, Ashad ko labari mutuwar jabir na zuwa mashi yayi bak'in ciki sosai tare da k'ara tsana Sultan da Alex Dan yasan su ne zasu kashe jabir tare daukar wa kan shi alk'awari wannan karan se Sultan ya mutu ko ana ha maza ha mata.

Had'a kayan shi Ammar yakeyi a trolley Adda ce ta shigo bedroom d'in tana murmushi tace, "Duk wannan sanmakwan na zuwa shanono ne Ammar? Sosa keya yayi yana dariya yace, "kawai Adda ina so na isa da wuri ne bana so dare yayimin a hanya,"
"Hakan na da kyau ai tafiya dare ba dad'i idan ka gama had'a kayan ka, ka zo breakfast na jiran ka" kai ammar ya d'aga tare da cigaba da had'a kayan shi Dan duk ya matsu yaga Nihal he Miss her so much.

Gyara Nihal take sha sosai duk wani abinda bata iya ba koyawa mata ake ta murje ta k'ara wani kyau kullun se an mata wanka so biyu kuma ko wani wanka da ruwan turare ake mata, k'afar ta ko tuni fasan k'afar ta sun bace, yau ma koya mata cin abinci ake da spoon da fork, da ta d'ebo abinci se ya zube, dariya Basmal take tana nuna Nihal da yatsa kuka Nihal ta fara tare da bin Basmal da gudu , gudu suke suna zagaye dakin ammi da shigowar ta kenan basmal ta boye bayan ta, tana yima Nihal gwolo, Ammi tace, "mi ta makin Sultana? kwabe fuskar Nihal tayi tana cewa, "Basmal ce da taga ana koyamin Abu se ta hau min dariya"
" rabu da ita kin ji Nihal" daga kai Nihal tayi ammi ta ruko hannun ta tare da rankwan shi Basmal, yar k'ara ta saki tana cewa, "zamu had'e ne anjima, " gwolo Nihal ta mata tare da bin ammi parlour, Dr Amir ne zaune Ammi tace, ga ta nan zaunawa Nihal tayi kusa da ammi Amir yayi murmushi gwaje-gwaje yayi ma Nihal tare da d'ibar jinin Nihal a Sirinji yasa a cikin jaka yana cewa, "na san insha Allah komai nata lafiya lau ne se dai muce Allah ya Nuna mana rana ammi," murmushi Ammi tayi me sauti tana shafa gefen fuskar Nihal wadda itama murmushi tayi duk da bata gane dalilin da yasa ake mata hakan ba, godiya ammi tayi ma Dr Amir sannan ya fita, sosai Nihal ke samun kulawa Matsala ta d'aya ce ilimin boko shima ammi tace se ta gama abinda take zata sama mata makaranta boko da islamiya.
Chapter 32 · 0% Book details