← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 128

Sashe 86

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*****
Yini yau duk yadda sultan yaso ya ga Nihal abun ya faskara dan kwata-kwata bata dawo part din su ba ganin baya iya jurewa rashin ganin nata, ya mike ya shirya cikin jeans and white shirt yayi kyau sosai har ya gaji se fitar da sanyayan kamshi yake kai tsaye part din Ammi ya wuce a parlour ya sami Ammi Dara nayi mata tausa dauke da fara'a sultan ya karasa tare da rungume Ammi ta baya ya mana mata pack a kumatu sannan ya dawo ya zauna yana kalle-kalle can kuma yace, "matar ina wife nane? tun safe ban kara sata a ido na ba," murmushi manya Ammi tayi tace, "tana garden dazu ina ji yara suna matsa mata suje garden tunda baka ganta ba to ta bisu" murmushi sultan ya saki tare da cewa, "bari na bi matata yaran nan basu bar min mata ta huta ko gajiyar biki bata sauke ba zasu daura mata tasu" sultan ya ida zancan tare da ficewa Dara dakeyiwa Ammi tausa wani irin dadi ne ya lullube tana jin dadin wannan kulawa da sultan yake nunawa Nihal Allah ya barsu tare ya tsare su daga sharin mahasada, Nazili dake bakin kofa tana kokarin fitowa magana data ji sultan yanayi ne ya sata juyawa ta fada saman gado tare da sakin kuka da tsinewa Nihal tana cewa, "se naga bayan ki Nihal natsane ki sai na raba ki da sultan har a bada" a haka baccin wahala ya dauke ta.

Dariya da Nihal keyi shi ze tabatar maka da tana cikin nishadi ita da su nawwara tiyo Nasim ya dauko naba shukoku garden ruwa yabi Minal da Nihal yana masu barin ruwa suna dariya suna boyewa bayan shukokin dake garden janyo Nasim Minal tayi tana mashi cakulkuli yana dariya da sauri Nihal ta dauko tiyo din ruwan tana wanke Nasim da ruwa joyuwa da zatayi da tiyo ta wanke nawwara da ruwa, ruwan basu sauka ko ina ba se jikin sultan lumshe ido sultan yayi tsayawa Nihal tayi tana kallan sultan daya tsare da rikitatun idanuwan shi sakin tiyo din ruwan Nihal tayi tana kallan sultan bugun zuciyar ta na karuwa shima sultan kallan ta yake yana kallan yadda ta jike rigar jikin ta ta wani manne a jikin ta gashin kanta duk ya like a jikin ta, ture Nihal Nasim yayi batayi masauki ko ina ba se saman chest din sultan gabaki dayan su kasa sukayi saman grass carpet dariya Minal da nawwara suka saki Nasim kuwa cigaba yayi da jikasu da ruwa lamo Nihal tayi saman fafadan kirjin sultan suna kallan juna a hankali sultan ya matsar da gashin kanta daya rufe mata fuska ya daura finger din shi saman lips din ta yana yawa da shi mirginawa Nihal tayi da sauri ta bar jikin sultan tana kallan shi ganin Nasim ya biyo ta da tiyo da gudu Nihal ta shiga zagaye garden tana dariya ita da su minal janyo Nasim sultan yayi tare dayi mashi rada a kunne dariya Nasim yayi tare da cewa, "give me five..! tafawa sultan da Nasim sukayi amsar tiyo din sultan yayi Nasim ya dauko wani da gudu suka shiga bin su Nihal suna gudu suna dariri ku, daga Nihal sultan yayi cak Nasim na jikasu da ruwa Nihal na dariya faranran hakuran ta na bayana yadda sultan ke juya Nihal abin sha'awa ne cike da tsantsar so da kauna, Gimbiya jalali da yakumbo dake kokarin wucewa fadda maimartaba lalacewa tayi tana kallan su kwafa ta saki tana cewa, "ka ci lokacin ka ina sane da kai ba matawa nayi da kai ba, iska na bari ka sha fata na daya Allah yasa bata dauki ciki ba," murmushi yakumbo ta saki tana cewa, "idan ma ta dauka zubar da shi abu ne mai sauki" murmushi Gimbiya jalila tayi tare da matsowa saitin kunnan yakumbo tana magana murmushi yakumbo take saki sannan Gimbiya jalila ta janye jikin ta tare dagawa yakumbo ido ta wuce part din maimartaba.

******
Washe gari da safe bayan aunty Aisha ta gama kimtsawa tsaf ita da driver suka biya gidan yaya sani dan dauko hajiya farida ko da suka isa ta shirya su take zaman jira ita da Ahmad dan ta na fari amsar car key Ahmad yayi hannu driver suka dau hanya Shanono tare da yan'sanda, basu wani dade ba suka isa shanono a harabar kofar gidan tanimu Ahmad ya faka motar shi kallo daya zakayiwa gidan kaji baka marmarin sakeyi, Ahmad da aunty Aisha da hajiya farida a tare suka dunguma suka shiga cikin gidan a tsakar gida suka sami gwoggo da Sara gwoggo na dirkawa Sara magani zubar da cikin ganin su aunty Aisha yasa kwana sha dake hannu gwoggo sub'ucewa ya kife a kasa ba komai ya haifawa gwoggo haka ba se yan'sanda dake bayan su jiki na rawa gwoggo tace, "Allah yasa lafiya daga ina? tab'e baki aunty Aisha tayi tana cewa, "au baki gane mu ba kenan, tanimu na gida koko? bakin gwoggo na rawa tace, "yana cikin kurya amma baya jin dadi"
"wannan damuwar ku ce ki shiga ki taso mana keyar shi, ko mu mushiga" inji aunty Aisha gwoggo wadda ta kid'ime ta rude tace, "baya iya takawa ko nan da can se dai ku shiga ciki" labinlan daki aunty Aisha ta daga warin daya doki hancin tane ya sata ja baya hanci dod'e tace, "office ku dauko shi tunda yana da rai kuma bakin shi be mutu ba, dole ya gayamana inda ya kai mana diya" haka yan'sanda suka kunna kai dakin Baffa yana matsar kwalla suka kinkimo shi yana cewa, "wallahi ban san inda yarinyar nan take ba ni kai na neman ta nake ido rufe kuyiwa Allah kuyi hakuri, kubar ni naji da wannan azabar nasan cewa sakaya Allah ke bibiya ta..! ko saurara shi basuyi su kayi waje da Baffa aunty Aisha tace, "idan ka je can kayi bayani" ihu gwoggo ta zunduma tana rike kafafuwan Aunty Aisha tana cewa, "kuyiwa Allah ku sakar min miji wallahi ko kun je da shi can se dai su karasa shi dan bashi da masaniya a kan inda yarinya nan ta shiga, na shiga uku ni indo" hanbare gwoggo Aisha tayi da kafa rarafewa gwoggo da Sara sukayi kafar hajiya farida wani irin hanbari hajiya faridda tayi gwoggo har se da kanta ya daki bango suka fice, haka gwoggo ta fito tana zunduma ihu tana bin su tana cewa, "na shiga uku ni indo kin cuce mu Nihal wai yaushe ne zaki barmu mu huta" har mota su ta tashi take a nan ta yanke jiki ta fadi daura hannu a kai Sara tayi tare da kwarma ihu tana kwallawa gwoggo kira.....

```Taku har kullun salma mas'ud nadabo```
[1/14, 8:03 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
*Story*
*And*
*Writing*✍🏾
*By*
*Salma mas'ud nadabo*👑

🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
(```We are the best among the rest```)

*_A gaskiya ina jin dadin comments na Ku masoya SAUYIN RAYUWA kuna zugani iri sosai din nan 😍Allah ya bar kauna_*🤸🏾‍♀

*page: 105_106*

Haka Sara ta rinka zunduma ihu da kyar ta samu wani ya taimaka mata shima sai da ya gama yi mata tanadi har yana cewa Allah ne ya kama su, har aka kai gwoggo asibiti yana masu kunfar baki, tunda ya kai su ya juya gashi ba ko sisi a hannun ta nan zube aka bar gwoggo ba likitin daya bi ta kanta bale kuma a kai ga nurses, ganin ba sarki se Allah yasa Sara bin Layin kati ko Allah ze sa ta dace, har layi ya zo kanta mika hannu me raba kati tayi tace, "kudi? Cikin sanyin murya Sara tace, "Baiwar Allah bani da ko sisi dan Allah ki taimaka ki bani ko da bashi ne, ki taimake ni kamar yadda Allah ya taimake ki," wata uwar harara sister rabi ta watsa mata tace, "da can kin san baki da kudin kati kika kwaso uwar taki kuka zo, ai se ki kwashe ta ku tafi gida malama in ban da san banza irin na matsiya ta, d'an abinda zaku bada din shi kukewa bakin ciki bayan asibitin ma na gwabnati ne, malama kama gaban ki ko nasa security's suyi waje dake" hawayan idanuwan ta Sara ta goge tana cewa, "keko bawar Allah ki taimake ni bani da ko sisi wallahi da ina da su zan ba ki, ki dubi halin da mahaifiya ta ke ciki mana baiwar Allah kamar baki da imani, ko bashin ne ki bani katin fata na mahaifiya ta taga likita" wata irin shewa sister rabi ta saki tana cewa, "Ai da yake uwar taki imani ya ishe ta ince ba indo bace matar tanimu kin ga malama ja kazamar uwar ki ku bace min da gani, ku je kuyi mata maganin gargajiya tunda ba halin yin na asibiti, ko ina taimakwan kowa na duniya an fada maki zan taimake ku ne? Naira biyar mutum ya rage ta kwana shinkafa sai kunbi tun har gidan kun mashi tanadi" ganin dai da gaske ci masu mutunci sister rabi keyi yasa Sara komawa gefe tana tsiyaya hawaye ita yanzu ya zatayi da gwoggo ko motsawa batayi gashi wanda ya kawo su sai da ya gama masu diba albarka, sai da Sara ta kwashe kwana biyu a asibiti tana neman taimako ba wanda ya saurare ta, haka ta tataro gwoggo suka dawo gida tana mata maganin gargajiya kallan gwoggo Sara tayi hawaye masu zafi suka zubo mata ita yanzu ina zata samo kudi, babu wani abinda yayi saura wanda zata iya dagawa ta saida a gidan, gidan ya zama tamkar kango babu abinda ya rage sai yar ya loluwar tabarmar da gwoggo ke kai kwance ita kanta tana bukatar kulawa saboda cikin dake jikin ta ba karamin laulayi yake sata ba ta rame tayi dan kai ga wani fari da tayi na yunwa goge hawayan idanuwan ta Sara tayi ta gyarawa gwoggo kwanciya ta zabga uban tagumi.

******
Chapter 86 · 0% Book details