Sashe 63
Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Ba karamin dadi Nihal taji ba ganin Nazili ta bar garden rai bace ko ba komai itama ta kona mata rai kamar yadda take mata, murmushi Nihal ta saki tare da gyara gashin kanta dake kare mata fuska tare da daura hannun ta saman na Basmal tana mai cigaba da sakin lalausan murmushi, cigaba da tattaunawa suke kan yadda zasu tsara program's din biki tare da ware ranar da zasu je shopping na musanman, kiran sallah magrib ne ya tashi su Nihal a garden part din Ammi suka wuce Kaitsaye kasancewar Nihal bata sallah se ta wuce babba kitchen dauke da murmushi Nihal ta shiga da sallama dauke a bakin ta, gabaki daya bayin dake kitchen din suka zube suna kwasar gaisuwa ciki fara'a Nihal ta amsa tare da matsawa kusa da jakadiya ba komai yasa Nihal shigowa kitchen ba se dan ta cikawa mom burin ta, dan ta lura kwata-kwata mom bata so bayi da ma'aikata nayiwa sultan girki, murmushi Dara ta saki tana mai cigaba da cewa, "ke dai gimbiya bakya gajiya da shigowa kitchen, kuma haka na da kyau Nihal! ita kanta jakadiya tana ji dadi yadda Nihal ta amshi ragamar girkin Sultan a hannun ta dan kar Sultan ya shiga wani hali! murmushi Nihal tayi tana cewa, "umma gajiya nake da zama bana aiki, na saba a gida kullun ina aiki" Nihal ta ida Zancan tana daura tukuya a gas, cikin dankankanin lokaci Nihal ta daura cuscus jakadiya tana yanka mata vegetable suna girki suna taba hira miyar kabej da dankali Nihal tayi taji vegetables se kamshi take zubawa, bayan ta kamala suka juye komai a wermar direct dining area Dara da Nihal suka wuce suna jerawa washe baki Jakadiya tayi tare da cewa, "gaskiya Nihal bani da abinda zance se dai nace sultan yayi sa'ar mata a wannan zamani kafin a samu Gimbiya me shiga kitchen tayi girki se an tona,! shuru Nihal tayi tana kallan jakadiya tana murmushin yak'e, murmushi Dara tayi tana mai cigaba da cewa, "Gimbiya a gaskiya ke da Sultan kun dace da juna sosai a cikin ku na rasa wanene yafi halin dataku," matsowa Dara tayi kusa da Nihal tare da rike hannuwan Nihal ta zauna da ita daya daga cikin kujerin dining shafa kumatun Nihal Dara tayi tana murmushi tace, "Nihal duk abinda zan fad'a maki da shawara da zan baki ki dauka Nihal ina jin ki tamkar ya'ta ta cikina, Nihal kisan cewa uwa ce kadai ke fadawa ya'ya ta shawara wadda baza cutar da suba," Dara ta ida Zancan tana tsare Nihal da ido tana mai cigaba da cewa, "Bayan Ammi da mom Sultan bashi da kowa se ke Nihal, na lura har yanzu kin kasa sakin jikin da Sultan karki manta fa mijin kine Nihal ya Kamata ki rinka sakin jikin ki da mijin ki kina sanin damuwar shi, Nihal tunda Sultan ya ta so a rayuwar shi be san wani abu kwanciyar hankali ba, Nihal kullun farautar rayuwar shi ake duk wani Abu da Sultan ze maki na dan lokaci ne inada yakinin cewa Sultan na sanki Nihal babu namijin da Kika dace da shi saman da sultan Nihal, Sultan amana ne a gare ki Nihal ke kad'ai ce zaki iya bashi kariya, naji dadi sosai da kike bashi wannan kulawar, amma ya kamata ki kara a kan wace kikeyi" tsare ta da ido Nihal tayi take nan tausayin Sultan ya lulub'e ta, zancan zuci Nihal ta shigayi tana cewa, mi yasa ake farautar rayuwar sa ya za'ayi mutumin daya taso cikin gata ya zamana ana farautar rayuwar shi idan ta lura kowa na gidan na nuna ma shi so, kuma bata taba ganin shi cikin damuwa ba, maganar cewa Sultan na santa wannan tunani umma ne, bata tunani akwai ranar da Sultan ze so ta ko a mafarki haka itama bata jin zata so Sultan dai-dai da rana daya se dai kalaman jakadiya sun sa jikin ta yin sanyi, taba kumatun ta da Dara tayi ne yasa Nihal dawowa daga duniyar tunani, kama hannuwan Dara Nihal tayi dake saman kumatun ta suna kallan juna murmushi yake Nihal tayi tare da lumshe idanuwan ta cikin sanyi murya tace, "umma zan shiga ciki" sannan Nihal ta mike har ta je bakin kofar bedroom jakadiya tace, "Nihal kiyi nazari a kan magana ta kinfi kowa kusa da Sultan a yanzu yana bukatar kulawar ki sosai! tsayawa cak Nihal tayi tana saurara maganar da Dara ke mata sannan ta murda handle din k'ofa ta shige bedroom din ta, jingina Nihal tayi da bakin k'ofa maganar Dara na dawo mata kamar yanzu take fada mata, lumshe ido Nihal tayi tausayin sultan na shigar ta da kyar ta iya jan yan'matan kafafuwan ta ta shige toilet ta watsa ruwa sanye da bathrobe Nihal ta fito daga toilet tana goge jikin ta da karamin towel, dressing mirror ta nufa ta shafe jikin ta da lotion me kamshi da sanyin dadi shiryawa tayi cikin black wando me kamar bagi se shirt orange me budadiyar kafad'a kayan sun mata kyau sosai kamar dan ita akayi su turare me sanyi dadi ta feshe jikin ta da shi sannan ta baza gashin kanta har gadan baya se shining yake ya wani kwana a gadan bayan ta, duk da ba wata kwalliya tayi ba amma tayi kyau sannan ta fito.