Sashe 114
Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Nihal dake kwance saman fafadan kirjin sultan hayaniyar mutana kauye ne ya tashe ta daga baccin daya dauke ta, a hankali ta mike tana bin garin da kallo ta cikin window tunda suka iso jikin ta yayi sanyi tana tuna abubuwan da suka faru a da, kama Hannun ta sultan yayi ya sakar mata kiss murmushi yake Nihal ta sakar mashi tana kara kallan window mai agwaluma data ta hango ne yasa Nihal juyowa tana cewa, "love please a tsaya a siya min agwaluma ina san sha" ja mata hanci sultan yayi yana cewa, "wannan cikin naki ya fiye janye-janye hayaty yanzu kuma daga zuwan mu gari sai mu fara siyan agwaluma, ko kyankyami bakiyi" bata fuska Nihal tayi ganin haka yasa sultan cewa, "bala driver tsayar da mota ka karasa wajan me agwaluma can ka siyawa hayaty" to bala yace tare da cin birki ya faka mota gefe Nihal sai washe baki take, 1k sultan ya ciro a walad din shi ya mikawa bala sannan bala ya fice iska mai sanyin Nihal ta furzar tana cigaba da kallan window wata almajira ce tayi tsaye bakin window tana bara, kasancewar glass din motar tinted ne na waje baya ganin na ciki kwakwasa window tayi tana cewa, "sadaka sabo da Allah ku taimaka kuma Allah ya kara maku arziki" tirtsetan cikin ta kawai Nihal take gani sai muryar ta dake rawa tana cewa, "tun daran jiya rabo na da abinci ku taimaka, ko dan abinda ke ciki na," tausayin tane ya kama Nihal fost din ta Nihal ta bud ta zaro dubu daya ta zame window ta mika lallausan hannu ta, ta window tace, "gashi..! rankwafowa almajira tayi da niyar amsa abinda Nihal ta ganine yasa hannun ta daukar rawa tana kallan almajira bakin ta na rawa idanuwan ta cike da kwalla tace, "_Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un_..! sultan dake zaune ne ya mike ganin Nihal ta bude murfin mota da sauri ta fice shima ya bude ya bita jada baya Sara tayi a razane, hannun Nihal na rawa hawaye na bi mata kunci tana bin tirtsetan cikin Sara da kallo wanda haihuwa yau ko gobe Sara ma daskarewa tayi tana kallan zukekiyar Gimbiyar data fito dan kwata-kwata bata gane Nihal ba saboda Nihal ta tashi daga Nihal din da ta sani a baya kodada wadda yunwar duniya ta ishe ta, motocin dake bayan su ne suka faka lokaci guda suka bale murfin motocin ganin Nihal daskare dan yatsan ta na nuna Sara hawaye na mata anbaliya zagoyawa sultan yayi ya kama Nihal ya juyo da ita suna facing juna yace, "hayaty mi ta maki me hadaki da wanna almajira muje kin ji" sultan ya ida zancan yana jan hannu ta yana makawa Sara mugun kallo duk a tunanin sultan maya ce dan tafi kama da su, mutuwar tsaye Nihal tayi tana kallan Sara da tsoro ya kamata lokaci daya ganin fadawa na nufo ta ya sata cewa, "baiwar Allah daga bani sadaka sai ki fito kina kuka wallahi babu abinda na mata ran ka ya dad'e, ka ja matar ka ku tafi bana neman massifa, masifar data dame ni ma tamin yawa abinda zanci nake nema idan har bara danayi ya haifar mata da haka, ku yafe ni ran ka ya dad'e" Sara ta ida zancan zata juya Nihal tace, "Sara..! me ya same ki na ganni a cikin wannan halin ina gwoggo da Baffa da ya mudi kika fito cikin rana da tsohun ciki kina bara..! juyowa Sara tayi a razane tana kallan Nihal tana kara tantance muryar ta daskarewa tayi hawaye na bi mata kunci bakin ta na rawa tace, Nihal..! Karki ce min ke ce kika koma haka yar gayu yar huta yar mulki da sarauta..! kuka ne ya kwacewa Sara rike da kwana ta na bara da hakuran ta sun mata yellow tace, "kinga yar da Allah ya maidani Nihal, kin ga yarda sakayar Allah ta sauka a kai na duk abinda gwoggo ta lusafa zai same ki a rayuwa ni ya sama, naga SAUYIN RAYUWA dubi yarda na koma kalli abinda ke jiki na" numfasawa Sara tayi tace, "ke dake talla safe da rana baki kwaso abin kunya ba sai ni, ke dake talla baki wulakanta a duniya ba sai ni" durkoshewa Sara tayi duk da cikin dake rinjayar ta ta hada hannuwan biyu tace, "na rokeki Nihal ki yafe mana abinda muka aikata maki idan kikaga yarda rayuwa ta lallace mana saboda tozar taki da mukayi ke da umma, zaki tausaya mana idan kika ga halin da muke ciki" Nihal dake kuka da sauri ta karasa ta daga Sara yan kauye na gefe sunyi cirko-cirko suna kallan su haka su maimartaba cikin kuka Nihal tace, "bana fata ko makiyi na na ganshi a cikin wannan hali Sara na yafemaki koda can ban rike ki a rai na ba" Nihal ta ida zancan tana rungume Sara duk da tsami da warin da take zubawa Nihal bata damu ba Dara ma fitowa tayi tana kallan Sara nan Nihal tayi ma Sara bayani Dara washe baki Sara tayi tana share hawayan fuskar ta, ta gaishe da Dara cikin sakin fuska Dara ta amsa, amshe robar hannu Sara Nihal tayi tace, "muje gida ko" Nihal na maganar tana smile, motar su Nihal Sara ta shiga ta zauna gaban mota sannan driver ya ja mota warin Sara nata kunbura mashi ciki sultan kuwa daura kanshi yayi saman kafadar Nihal yana shakar kamshi ta.
```Taku har kullun salma mas'ud nadabo```🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
*Story*
*And*
*Writing*✍🏾
*By*
*Salma mas'ud nadabo*👑
🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
(```We are the best among the rest```)
*Page: 131_132*
Tunda suka doso harabar gidan Nihal ke kallan gidan yarda ya lallace a da ba gidan daya kai nasu kyau da tsaruwa, Amma a yanzu babu gidan daya kai shi lallacewa murfi mota suka bale gabaki daya suka fito Sara tayi masu jagora shiga ciki.
Gwoggo dake kokarin fitowa daga kurya tana yafa zani kodadiyar atamfar ta saboda labari ya zo mata cewa, Sara tayima maimartaba ba dai-dai ba daga zuwan shi rangani da iyalan shi, sallama Sara ce ta katsewa gwoggo hanzari da sauri ta fito daga daki tayi hanyar zaure muta nan data ganine tare da Sara yasa gwoggo makalewa tsaye tana bin su da kallo baki sake, da karkatacan bakin ta kaya a kode sun sha ruwa sunyi daud'a hannu rike da zani, Sara ce ta katse mata tunanin da cewa, "gwoggo kalli ki gani Nihal ce fa ta zo tare da su maimartaba sarkin kano kin ga yarda Nihal ta zama duk abinda muka mata hakan be hana ta neman mu ba Gwoggo" Sara ta ida zancan idanuwan ta taf da hawaye, Baffa dake kwance a tsakar gida yana juyo murya Sara tana fadin wannan zancan hawaye ne suka sulalo mashi.
Kallo daya zakayiwa Baffa kaji baka marmarin sake wa saboda yarda jikin shi ya koma tamkar yayi gobara ya kone ya lallace yayi baki ga wani ruwa mai wari dake fita daga jikin shi, bakin shine kawai ke motsawa shima da kyar amma duka jikin shi ya lallace.
Dafe kirji gwoggo tayi tana nuna Nihal da yatsa tana girgiza kai tana ja da baya tana cewa, "inaaaaa bazeyu ba Nihal ce ta koma haka tana yawo da manyan mutane wayanda sai a TV kake ganin su, jini Habu ce ta koma haka inaaaaa, inaaaaa wallahi da sake" dariya ta tintsire da ita tana cewa, "ah bazeyu ba duk abinda muka aikata ni da malam dan gani cewa basu ci gababa shi ne yanzu take tare da sarki inaaa hahha," hauka gwoggo take tuburan cirko-cirko su maimartaba sukayi da Nihal din ita kanta ganin yarda gwoggo ke hauka tana dariri ku, kuka Sara ta saki tana cewa, "innalillahi wa'inna ilaihi raju'un me haka kike gwoggo me nake gani haka" Sara ta ida zancan tana kama gwoggo dake kokarin yage kayan jikin ta ta dankara a guje, da kyar aka kama gwoggo tana shure-shure aka tura ta daki aka kule da kwado amma har a lokacin tana dukan kofar dakin almarin su Nihal karasawa yayi jikin su maimartaba yin sanyi.