Sashe 82
Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Bangaran Nihal kuwa zama tayi saman gado tana kallan rigar siraran hawaye na zubo mata duk da ta san wacece zata iya aikata mata haka amma bata da tabas kan hakan, wai mi tayiwa Nazili ta tsane ta haka, idan ma kan sultan take mata haka ita sultan ba damun ta yayi ba kuma ai ba ce mata akayi arzikin gidan su ya d'ad'a ta da kasa ba ne da zata rinka wulakantata, ko da yake ba laifin ta bane rashin nuna tana da tushe ne ya janyo mata tsana wajan Nazili, amma ta kuji zuwa rafi wata rana tulu ze fashe jin kamar an tabata ne yasa Nihal juyowa a dan razane sultan ne tsaye kanta goge hawayan fuskar ta Nihal tayi da sauri ta rarumo hijab din dake kusa da ita, ta saka tana kokarin fita kama hannun Nihal sultan yayi ya tsare ta da sexy eyes ball din shi yace, "what's wrong with you, why those tear,? sultan ya jefawa Nihal tanbayar shuru Nihal tayi idanuwan ta taf da kwalla tana wasa da rigar hannu ta, matsowa sultan yayi gaban Nihal yace, "kinyi shuru Nihal waya bata maki rai? da kyar Nihal ta iya nunawa sultan rigar da aka kona mata tare da saki kuka tana cewa, "ban san waya min haka ba kawai naga rigar haka, yanzu ni shikenan bazani dinner ba tunda bani da ashobe" Nihal ta ida zancan a shagwabe hawaye na wanke mata fuska sultan ko a zuciyar shi yasan haka tana iya faruwa saboda ya lura yanzu kamar kan matar shi aka dawo dan a tarwatsa mata fari cikin ta, kamar ya sani ya dinka mata nashi dinki na daban murmushi sultan ya saki bin shi da kallo Nihal take sannan ta had'e rai tana cewa, "dadi ma ka ji..? ta ida zancan zata zame hannu ta daga rukwan da sultan ya mata janyo Nihal sultan yayi ta fada saman fafadan kirjin shi zaro ido Nihal tayi tana kokarin kwace kanta a hankali sultan yake magana kamar me rada yana cewa, "ba kina da karfi ba ki kwace kanki mana" sultan ya ida zancan yana kashe ma Nihal ido wiki-wiki Nihal tayi tana girgiza kai tace, "ya hakuri ka sake ni please" sasauta rungumar da sultan ya mata yayi da sauri Nihal ta ja baya ruko hannun Nihal sultan ta yayi, be zame da ita ko ina ba se bakin drewar Nihal na biye da shi, drewar ya bud'e tare da ciro gwon ya mikawa Nihal d'aga rigar Nihal tayi abin mamakin shine wannan riga ta fi wacan haduwa nesa ba kusa ba dinki ba karamin kyau yayi ba gaban dressing mirror Nihal ta tsaya tana kallan rigar wani irin murmushi ta saki da karfi Nihal ta furta, "wow..! dan bakin ta ya kasa rufuwa saboda murna, juyowa tayi tana kallan sultan cike da murna tace, "amma na gode wannan rigar tafi tawa kyau sosai sultan, duk wanda ya gani da wanna rigar se ya kalla ya kara kalla" Nihal ta ida zancan tana washe baki sultan yace, "saboda nasan zatayi ma princess kyau na aje mata dama can ita nake so ki sa" murmushi Nihal ta saki tare da shigewa toilet da sauri rigar kawai ta saka ta fito a hankali ta tako sultan dake zaune saman sofa bin ta yayi da kallo saboda kyan da rigar ta mata mikewa yayi a hankali ya tako gaban Nihal yana kallan ta wayar shi ce dake ruru ta katse mashi hanzari daukar wayar yayi tare da cewa, "kuna inayi shigowa" murda kofar da akayi ne yasa Nihal juyawa masu make up ne mata suka shigo washe baki Nihal tayi tana kallan su tana kallan sultan wani irin dadi na ratsa ta sultan ne ya katse mata tunani da cewa, "ki je suna jiran ki fa, bari naje na dawo" sultan ya fada tare da ficewa, cike da murna Nihal ta zauna anayi mata make up me kyan gaske tasha mamakin kyan data zuba su kan su masu make up din yaba kyan da Nihal tayi suke rose ce daya daga cikin masu make up din tace, "ran ki yadade wannan kyau da kikayi har kin so kifi amarya" murmushi Nihal ta saki tana cewa, "rufa min asirri ina ni ina fin amarya" dariya rose tayi tace, "toh shikenan haka dai kika ce amma ni gani nake ta kusa fin amarya ko Rachel," Rachel dake hada kayan su cikin jaka tace, "wallahi kuwa har da ita din me kyau ce" haka suka gama hada kayan su suka fice, fitar su da yan mintoci sultan ya shigo ya shirya cikin shadda shi light blue tasha aiki da dark blue zare ba karamin kyau ya zuba ba kan shi na sanye cikin dark blue hula sajan shi ya kwanta luf-luf red lips din shi se shining yake Nihal ko mutuwar tsaye tayi tana kallan sultan, saboda kyan da ya mata shima sultan din kallan Nihal yake yana sakar mata kill smile din shi me sace zuciyar yan'mata har ya tako gaban ta Nihal na kallan shi da jinjina irin kyan da manya kaya ke mashi, hura mata iskar bakin shi sultan yayi a ido, lumshe ido Nihal tayi a hankali ta sauke idanuwan ta saman fuskar sultan, sultan ne ya katse mata tunani da cewa, "kallan fa?, na canza maki ne? sultan ya fada yana daga ma Nihal gira, da sauri Nihal ta juya har tana bari da kayan dressing mirror cije hakora Nihal tayi cikin zuciyar ta tana cewa, "karfa wannan mutumin ya rai nani me yasa ma na tsaya ina kallan shi" bayan ta sultan ya dawo ya tsaya tana hango shi ta cikin mirror sarka sultan ya ciro a aljihun shi ya matsar da gashin Nihal ya fara saka mata kallan sarkar Nihal take se kyalkyali sarka take a hankali Nihal ta daura hannun ta saman sarkar tana kallo tace, "wannan sarkar fa sultan" murmushi sultan ya saki yana cewa, "Ammi ce ta bani na saka maki, idan baki so se na maida mata" turo baki Nihal tayi tana kara shafa sarkar tana smile tace, "ya za'ayi na ce bana so bayan sarkar ta min kyau, kuma fa ammi ce ta bani amma na gode sarkar na da kyau sosai dubi yadda ta min kyau" Nihal ta ida zancan tana washe baki sultan kuwa dadi yaji saboda shi ya siya mata sarkar ba wata Ammi ya fada ne kawai, hata dan kunna sarkar sultan ne yasa mata kallan juna suke ta cikin mirror kamar kar su daina cikin siririyar murya ta Nihal tace, "na gode sosai sultan ka sani farin ciki a wannan daran" Nihal ta fada tana smile, hugging din Nihal sultan yayi ta baya a hankali ya sakarwa Nihal kiss a wuya ya furta "kinyi kyau..! kasa da kai Nihal tayi zuciyar ta na tsana ta harbawa cike da tsoro tana wasa da yan yatsun hannun ta a haka suka fito. compound mota na fake tana jiran su murfin mota sultan ya bud'e mata sannan ya zagaya ya zauna driver ya ja mota.