← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 128

Sashe 72

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ringing din wayar sultan ce ta katsewa su DPO Bilal hira da suke a parlour daukar wayar DPO Bilal yayi tare da nufar dakin da Sultan yake ya mika mashi wayar a hankali yasa hannu ya amsa ya kara a kannu ne tare da cewa, "hello..! Tj dake kusa da Nihal yace, "sultan..! ya ida zancan yana shekewa da dariya ya cigaba da cewa, "idan kana san matar ka ka zo ka amshe ta amma se k zumin 20 million cash idan kuma baka san ta," Tj ya ida zancan yana jawa Nihal gashi ya kara wayar a dai-dai Nihal Sultan na jiyo ihu Nihal da kukan ta, Tj ya kara wayar a kunnan shi yana cewa, "mi ka ji..! cikin rawar murya Sultan yace, "please ku daina taba ta duk abinda kuke so zan baku amma karku salwantar da rayuwar ta please"
"Bazan mata komai ba idan zaka bada abinda muke bukata' amma idan baka kawo kudin ba se na kashe ta, sannan gargadi na biyu bana san ka zo min da police ko daya, ka zo min da police se na kashe ta nama fada ma," sannan Tj ya saki murmushi yana cigaba da cewa, "ko ban fada ma inda nake ba na san ka sani, saboda kana zagaye da police, na baka nan da 2 hours idan baka zo ba se na kashe ta..! Tj ya ida zancan tare da kashe wayar mikewa sultan yayi da sauri suka fice da DPO Bilal banking suka wuce su duka se da Sultan ya ciro kudin nan cas ya zubasu cikin briefcase din shi sannan yasa briefcase din a boot, DPO Bilal ya tari numfashin Sultan yana cewa, "Sultan ka kwantar da hankali ka muna biye da kai ga wannan abun kasa a kunnan ka duk abinda ke faruwa zamu sani," amsa sultan yayi yasa a kunne Ammar ya daga kafadar shi yace, "Allah ya maido ka lafiya" smile Sultan ya saki yana fatan Allah yasa ba abinda ya sami Nihal jin kamar idanuwan shi sun kawo ruwa yasa ya shige mota, tare da ja ya bar harabar Bank din DPO Bilal da yaran shi na biye da shi a haka Sultan ya karasa dajin ba motsin kowa se tsintsaye da bishuyoyi dake kadawa haka ya rinka shiga har se da hango gida sannan yayi parking motar shi ya tsaya, message Tj ya turo mashi yana cewa, "ka fito daga cikin motar kudin mu matar ka..! a hankali sultan ya fito daga mota ya bud'e boot ya fido briefcase din shi ya tsaya jikin mota yana waige-waige ina ze ga sun bulo , Tj ne ya damko Nihal fuskar shi a rufe ya tsare Nihal da bindiga suna tafiya tana mutsu-mutsu fuskar ta kumbura saboda tsabar duka uniform din jikin ta biyar baka siyan su saboda dati ga gefan bakin ta daya fashe jini kwance a bakin, sultan na hango ta ya taso da sauri kamar yayi kuka itama Nihal din kuka take ganin sultan, nuna shi da bindiga Tj yayi yace, "karka kara matsowa na fadama," daga hannun Sultan yayi yaci birki tare da aje briefcase din shi a kasa DPO Bilal da yaran shi na bayan bishiya suna kallan abinda ke faruwa sultan na aje kudin ya kara matsowa yana kallan Nihal dake shabar kuka shima da kyar yake controlling kanshi ji yake kamar yayi kuka alama Tj yayi BS dake gefe ya je ya dauki briefcase din da Sultan ya aje, rike da bindiga BS ya karasa ya dauki briefcase din big boy ya faka mota BS ya tura kudin cikin mota ya shige, tura Nihal Tj yayi ta tafi taga-taga zata fadi da kyar ta mike zata karasa wajan sultan tana kuka DPO Bilal da yaran shine suka fito da sauri kafin sunyi aune ji kake daram-daram harbin be sauka ko ina ba se gefan cikin Nihal tsayawa tayi cak hawaye azaba na bin kuncin ta Sultan dake jikin mota da karfi yace, "Nihal..! gabaki daya dajin se da ya amsa da gudu ya nufo Nihal gabaki daya yaran DPO Bilal fitowa sukayi suka bi Tj da yaran shi ji kake an kara dauke Nihal da wani harbin dukewa Nihal tayi dafe da ciki yana zubar jini, Sultan na karasowa Nihal ta fadi kasa dafe da ciki jini na bin bakin ta idanuwan ta na fidda ruwa janyo ta Sultan yayi jikin shi bakin shi na rawa yana shafa kumatu yace, "please Nihal ki bud'e idanuwan ki Nihal, dan Allah karki mutu " gabaki daya Sultan ya rud'e ya gigice idanuwan shi sunyi jawur jijiyoyi duk sun taso, a hankali Nihal ta bud'e idanuwan ta dake fidda hawayan wahala ta daura hannun ta saman fuskar sultan hawaye na bin kunci ta da kyar ta iya furta, "sultan bakin ta na rawa sannan ta saki smile a hankali idanuwan ta suka rufe wani ihu Sultan ya saki yana jijiga Nihal ganin bata motsi ya fashe da kuka.........

```Taku har kullun Salma mas'ud nadabo```
[1/7, 2:29 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
*Story*
*And*
*Writing*✍🏾
*By*
*Salma mas'ud nadabo*👑

🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
(```We are the best among the rest```)

*Page: 95_96*

Daukar Nihal sultan yayi cak ya karasa da ita bakin mota back sit ya bud'e ya kwantar da ita, shafa kumatun ta Sultan yayi tare da goge hawayan shi da bayan hannu maida kofar yayi da sauri ya rufe ya zagaya front sit ya zauna da gudu ya figi motar ya bar harabar dajin, yana gudu ya juyawa yana kallan Nihal hawaye na zubu mashi yana cewa, "baza ki mutu ba Nihal insha Allah baza ki mutu..! a haka ya karasa asibitin shi yana isa harabar asibitin yayi wani wawan parking da sauri ya zagayo ya dauki Nihal har a lokacin tana zubar jini bata motsi, da gudu nurses suka karaso da gado aka daura Nihal aka karasa shiga da ita cikin Asibiti har a lokacin sultan na makale da Hannun Nihal dayan hannu shi na zaman kanta, har se da aka karaso theater room sannan doctor amir yace, "sultan ka kwantar da hankali ka zamu duba ta insha Allah zata warware" goge hawayan idanuwan shi Sultan yayi yana cewa, "da gaske Nihal zata tashi.? bana so ta mutu amir, dan Allah karka bari Nihal ta mutu dan Allah amir, Nihal ta mutu bazan yafewa kai na ba Amir," sultan ya ida zancan yana sakin kuka zauna da shi Amir yayi yana lallashin shi yana cewa, "Insha Allah lafiya lau zamuyiwa Nihal aiki ta mike insha Allah zamu samu nasara ceto rayuwar matar ka" daga kai sultan yayi yana kokarin tsaida hawayan dake neman zuba mashi, sannan doctor Amir ya wuce office da sauri ya shirya cike da tausayin abokin nashi, da sauri ya wuce theater room sultan na bakin kofar yana zarya yana hango operation din da akewa Nihal ta glass door, white shirt din shi ko duk ta baci da jini jirin da yake ganine ya sasa samun waje ya zauna ya jingina da kujera, Ashad da fitowar shi daga office kenan ya hango sultan, ko ba'a fada mashi ba yasan yana cikin matsala har ya taka ya karasa wajan shi se kuma ya ci birki, yana cewa, "to ina ruwa na da matsalar shi, nurse din da ya ganine zata wuce yasa Ashad cewa, "sister naja..! Juyowa sister naja tayi Ashad ya karaso wajan ta yana cewa , "Sister naja mike faruwa da yayana.! Ashad ya fada cikin sigar damuwa nan da nan sister naja ta kwashe abinda ya faru ta fadawa Ashad ta ida zancan tana cewa, "Boss ya bani tausayin yana san matar nan ta shi koma waye ya aika ta masu haka Allah se ya toni asirri shi" sister naja ta fada idanuwan cike da kwalla sannan ta wuce Ashad wani irin dadi ne ya lullube Ashad shafa gemun shi yayi yana cewa cikin zuciyar shi daga gira Ashad yayi yana cewa, to waye ze aika ta haka dama bamu kad'ai ke farautar rayuwar wannan shashashan nan ba, tura hannuwan shi Ashad yayi cikin aljuhu yana cewa, Amma na san wannan aiki Momi ce zata aika ta ba tare da ta sanar da ni ba yaushe ta fara abu ba tare da shawara ta ba? i wish tare dani aka shiga da ba abinda ze hanani aikata lahira se ya ida haukacewa gabaki daya, Ashad ya ida zancan yana ficewa daga asibitin da sauri dan be so Sultan ya ganshi ya katse mashi hanzari parking space ya wuce tare da shigewa back sit driver ya ja suka bar harabar asibitin zuciyar shi cike da gulma.

Bangaran su DPO Bilal yankawa sukayi jeji suna bin su Tj kasancewar Tj be samu nasara shiga mota ba, gudu ya shigayi cikin jejin amma se dai kash su DPO Bilal sun cin mashi birki ya ci tare daga Hannun shi sama DPO Bilal yace, karka kara ko motsi daya ka tsaya inda kake" murmushi Tj ya saki yace, "A kan wani dalilin zan tsaya na tsaya a sani gidan yari tsawan shekaru har se na jigata kwata-kwata rayuwa ta bata dace da gidan yari ba ni bazani gidan yari ba na samu SAUYIN RAYUWA" juyawa Tj yayi ya cigaba da gudu DPO Bilal beyi kasa a gwigwa ba ya dauke Tj da harbi dukewa Tj yayi yana kallan DPO Bilal da kyar ya iya daga hannu ya nuna idan shi dana DPO Bilal take a nan ya sulale sumame yaran shi DPO Bilal yasa suka dauki Tj suka tura a mota dan wuce wa da shi asibitin, su BS da suke cikin mota suna jin saukar Harbin rintsi ido BS yayi yana cewa, "shit..! Ya ida zancan ya dukan sitiyarin mota yana cewa, "an gama da mu ya kamata na kira Nazili ta san halin da ake ciki..! har motar su DPO Bilal ta wuce motar su na fake a karkashin bishiya iyakar rud'ewa sun rud'e fisgar motar su sukayi da karfin dan barin wajan.
Chapter 72 · 0% Book details