Sashe 47
Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Banko kofa Nihal tayi da karfi tana maida numfashi cikin d'aga murya tace, "Sultan! Sultan dake kokari kai spoon bakin shi ne ya lumshe ido yana k'ara jin tsanar Nihal yau kuma da wani iskanci ta zo na kiran suna shi da karfi gaban bayi, ware idanuwan shi yayi tare da k'ok'arin kai spoon bakin shi karo na biyu, da sauri Nihal ta warce spoon d'in hannun Sultan, tayi tsuru-tsuru dan ita kanta bata san ta ina zata fara bayani ba, Adama dake gefe in ban da tsuma ba abinda take, zufa se karyo mata yake, dubare ce ta faduwa Nihal tace, "tsaka na gani cikin tukunyar miyar yanzu" ta ida zancan tana tsare Sultan da ido duk tabi ta riki ce sultan yace, "Tsaka kuma ! Murmushi Sultan yayi na rainin wayau yace, " Dara kwashe abincin nan" gwagwamar ajiyar zuciya Adama ta saki tare da jin tsanar Nihal, haka suka washe abinci, k'ok'arin fita Nihal take Sultan ya ruko hannu ta, gaban tane ya yanke ya fad'i Allah yasa kar sultan ya gano cewa lab'e tayi har ta ji, Sultan ne yace, "Na san cewa babu wata tsaka data fad'a cikin tukunyar abinci da zanci, kuma kada kiyi tunanin dan kinyi wannan abun shi ze sa na yadda dake, idan kina tunanin haka gwara tun wuri ki canza tsari, tanbaya ta a nan ya akayi kika shiga babba kitchen har ki kaga tsaka cikin tukunya ko kuma nace suwa ki ka gani suna zuba min guba a abinci,? Idan ko har baki fad'a min ba nafi tunanin wannan shirin ki ne," juyowa Nihal tayi ta fisge hannun ta daga rukwan da Sultan ya mata idanuwa ta taf da kwala murmushi yak'e Nihal ta saki tace, "Ai dama ba tsakar data fad'a nayi hakan ne dan na haram tama abincin, kamar yadda ka haram tamin zuwa makaranta d'azo" Nihal ida zancan tare d'aga gira ta cigaba da cewa, "yanzu nasan duk halin da ake ciki an zubar da abinci se kasa a dafama wani ko ka kwana da yunwa na san kai ma yanzu ka ji yadda na ji" sannan Nihal ta fice, ciki sumar kan shi Sultan yasa hannu shi yana zagaye parlour shi kan shi yasan karya take kawai dai tasan an zuba guba ne cikin abinci kamar yadda zuciyar ke ba shi, wata zuciyar na cewa karka ga dan tayi ma haka ka yadda da Nihal itama Asiya haka tayi ta shigo rayuwar ka Sultan, fad'awa Sultan yayi saman kujera ya lumshe ido.
"Amma dai anyi tsinaniyar yariyar" Gimbiya jalila ta ida zancan tana huci kamar kumurci ta cigaba da cewa yarinyar nan Gona ta take so ta fara shiga in tasan wata bata san wata ba, ni mai iya sawa ce akawar da ita cikin d'an kankanin lokaci wannan Nihal d'in se naga bayan ta, ta fara shigar min hanci yakumbo " Gimbiya jalila ta ida zancan cikin d'aga murya, juyowa Gimbiya jalila tayi tace, "yama akayi tasan da an zuba guba cikin abinci? Gimbiya jalila ta watsawa yakumbo tanbayar, "nima wallahi Gimbiya abin da ke daure min kai kenan" murmushi Gimbiya jalila tayi tace, "ina so ki aika a kashe min Adama a daran nan" sannan Gimbiya jalila ta shiga d'aki ta bar yakumbo a parlour.
*Washe gari*
Shiryawa Nihal take cikin wata gwon maroon me dogwan hannu fuskar nan tata ba walwala tayi fayau da ita, bayan ta gama shiryawa ta fito parlour zaune ta samu Sultan saman kujera yana sanye da suit black yayi kyau sosai, cikin siriryar murya ta Nihal tace, " "ina kwana" tana k'ok'arin wuce shi ta fita, dan bata damu daya amsa ba da karya amsa, mik'ewa Sultan yayi yace, " ki jira ni mu fita tare akwai inda zamu" Sultan ya fad'a a tak'aice tsayawa Nihal tayi cak tana mai k'ara jin haushi Sultan da ya barta tana zuwa makaranta ai da yanzu tana can d'an siriri tsaki Nihal ta saki, k'arasowa da Sultan yayi ne yasa Nihal k'ara had'e rai kallan kasan ido sultan yake mata yana mamaki halin Nihal na karfin hali wani lokacin idan tana masifa ba abin da ke birge shi kamar yadda karamin bakin ta ke zakalkalewa kamar zata iya dukan shi, dan siriri tsaki Sultan ya saki tare da kauda kan shi, tafiya suke a jere gwanin ban sha'awa har suka karaso part d'in Ammi dauke da sallama a bakin su suka shiga Ammi da Basmal dake zauna ne suka washe baki Ammi tace, "Nihal ya akayi baki je makaranta ba, Ammi ta jefawa Nihal tanbayar, shuru Nihal tayi tana tsare Sultan da ido ja mata kujera sultan yayi yana murmushi yace, "Ammi bana so tana fita kullun ana gane min mata zan sama mata lesson teacher mace a gida" murmushi Ammi ta saki tana cewa, "hakan na da kyau sultan kayi tunanin mai kyau idan exam ya zo se taje ta zana"
"Ai dama haka na tsara" ya ida zancan yana kallan Nihal wadda ta had'e rai daura hannu shi yayi saman na Nihal yana mata kallan shi me rikita yan'mata shi ga munafi ki tunda gaban Ammi ne, murmushi yake Nihal ta saki tana mai kasa da kanta Basmal tace, "yayana soyayya ka da Aunty Nihal na birge ni, Nima Allah ya bani Wanda ze min haka," murmushi Sultan da Nihal sukayi suna kallan juna, Nihal ko a zuciyar ta cewa take da ban ji maki dadi ba Basmal, Ammi ce ta katse masu tunanin da cewa, "se naga kamar fita za kuyi? murmushi Sultan ya saki yana cewa, "uhmm wani waje zata rakani" Sultan yana maganar yana shan coffee, washe baki Ammi tayi tace "Allah ya baku zaman lafiya da fahimtar juna wannan soyayya taku tana tuna min da tsoho miji na margayi" Ammi ta fad'a tana kallan Basmal dariya gabaki d'ayan su suka saki ban da Sultan da ya had'e rai yana washe bakin karya, Basmal tace, aunty na ya kamata ki canza kaya tunda tare da yayana zaki fita ya kamata kiyi gayun da yafi haka," d'an daburcewa Nihal tayi tana cewa, "ki barni haka ma bana sa...!!!
"Haba aunty please ki tashi muje mana" Ammi tace, "ki tashi mana Nihal nasan Dara ta maki make up se kin zama looking take away my dear," kallan da Sultan ya mata ne yasa Nihal mik'ewa bedroom d'in ta suka shiga, shirya Nihal akayi cikin dark blue gwon me dogwan hannu me flowers da stones se walwali kayan suke nanad'e mata gashin ta akayi aka sokeshi da wata yar kibiya lips d'in ta yasha maroon Jan baki ita kanta Nihal ta yaba kyan data zuba se dai takaicin ta d'aya saboda Sultan akayi shi mtsww, black veil ta dauka da fost silver me kyau suka fito, fitowarta tayi dai-dai da fitowar Nazili ta shirya cikin jeans and t-shirt ta saki gashin kanta kallo tabi Sultan da shi Wanda ke kallan Nihal yana yaba kyan ta a zuciyar shi da ko ganin Nazili beyi ba da take mashi magana cikin iyayi, juyawa Nazili tayi nata kallan inda Sultan ke kallo wani kulutun bakin ciki ne yayi mata tsaye tana bin su da kallo, Basmal ce ta katse mata tunani da cewa, "Aunty na kinyi kyau masha Allah," kallan Nazili Basmal tayi tace, "yau fa yayana ze fita da Aunty outing ya kikaga ni Nazili, dama tunda sukayi aure basu samu damar fita ba saboda aiki" wani miyau Nazili ta hadiye tana mamaki irin kyau na Nihal take a nan idanuwan ta suka fara kawo ruwan mik'a ma Nihal hannu Sultan yayi a hankali ta daura lalausan hannu ta saman na Sultan yana tsare ta idanuwa shi masu rikitata suka fice, Basmal sakin baki tayi tabin su da kallo dan wani irin mugun birge ta suke, tunanin Ammar ne fad'o mata a rai murmushi ta saki ta shiga daki dan yau itama se taga sanyin idaniyan ta Nazili da ta cika tam idanuwan ta taf da kwalla Ammi na lura da yanayin ta.
d'aki Nazili ta shiga da gudu tana kuka watsa kayan dressing mirror d'in ta Nazili take tana cewa, "se na kashe ki Nihal na tsane ki na tsane ki Nihal" tana kuka tana sanbatu Ammi ce ta turo kofa ta shigo taga yadda Nazili ke hauka rike ta Ammi tayi tana cewa, " Nazili! jikin Ammi Nazili ta fad'a tana cewa, "ta kwace min farin ciki na Ammi, ki na ganin irin kallan da Sultan ke mata me cike da so ko ganin mutane bayayi na tsane ta ammi, ta dauke min fari cikin Ammi," rugume ta ammi tayi tsam tana jin tausayin Nazili na shigar ta duk se ta ji ba dadi bata taba tunanin cewa Nazili nasan sultan ba ko tana san nashi ba tayi tunanin san ya kai haka ba, Amma yanzu lokacin ya riga ya kure se dai in shi sultan d'in ne yace yana san ta da kan shi.
fisge hannun ta Nihal tayi a compound can kasan makoshi tace. "Na fad'a ma babu inda zan bika, ka kyale ni na koma cikin gida dan fita da kai babu wani Anfani na fad'a ma sultan," Nihal ta ida zancan tana tsare Sultan da ido, ko saurara ta sultan beyi ba ya bud'e mata murfin mota ya tura ta ya zagaya Alex ya bud'e mashi suka bar harabar gidan.
Shiryawa Basmal tayi cikin wata brown gown me dan siriri hannu ta kama jikin ta parking gashin kanta tayi ta yafa veil tayi kyau sosai kallan mirror take tana cewa, "Allah yasa ya Ammar ya ga nayi kyau" wasu books ta dauka tana fitowa parlour ta had'e da Ammi murmushi Ammi ta saki tana cewa, "wannan gayun fa se ina? murmushi Basmal tayi tace, "gidan waziri zani ya Ammar ze koya min wani lesson," murmushi manya Ammi tayi tace, "yau be je office bane,?
"ina tunanin haka saboda naga motar shi a waje"
"Ok Allah ya taima ki gaishe min da Adda", sannan Basmal ta fice.