Sashe 23
Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sanyi-sanyin Asubane yasa umma yin bacci gyara mata kwanciya Nihal tayi sannan ta fito ta dauro alwala ta koma ta gabatar da sallah bayan ta idar ne ta sake tab'a jikin umma har yanzu jikin da zafi amma ba kamar jiya da dare ba.
Fita tayi ta fara aika ce aika canta na yau da kullun kasancewa yau wanki jiya zata k'arasa dan haka yau ba talla, ruwan koko ta daura sannan ta koma bakin rijiya tana Jan ruwa, se da ta gama cika ko ina na gidan sannan ta shek'a koko ta juyewa su gwoggo nasu abokiti ta d'ibi nasu, ta d'umama tuwo ta aje da sauri ta kwashe Nasu ta kai daki tana fitowa suka hade da gwoggo ko kallo bata ishe ta ba ta dau kayan kalacin su ta shige daki, sauke ajiyar zuciya Nihal tayi ta koma dakin su lokaci umma ta tashi murmushi ta saki tare da jinginar da umma ta zuba koko a cup ta fara ba umma kurba d'aya zuwa biyu umma tayi fara kakarin amai sai da ta amaye kokon tas tana mai numfashi.
```Taku har kullun salma mas'ud nadabo```🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
*Story*
*And*
*Writing*✍🏾
*By*
*Salma mas'ud nadabo*👑
🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
(```We are the best among the rest```)
*Page: 45_46*
sannu Nihal ta shiga jirawa Umma da sauri fita ta dauko ruwa da tsunma ta goge ma umma jikin ta, sannan ta goge k'asan dakin tana cewa, "Umma sannu kin ji Allah ya baki lafiya, anjima ina samu dama na fita zanzo maki da maganin zazzabi ki samu ta sauka sannu," tana maganar tana taba goshin umma Wanda yayi zafi sosai har zata mik'e umma tace, "Nihal cikin raunaniyar muryar ta dawowa Nihal tayi ta zauna tana k'ak'aro murmushi da iyakar shi laban ta, cikin sanyin murya umma tace, "Allah yayi maki Albarka Nihal Allah yasa ki gama da duniya lafiya, insha Allah Nihal rayuwar bazata cigaba da zama a haka ba jiki na, na bani se kin zama wani Abu a duniya, ni fata na dake a duk inda kike ki zamo mai gaskiya da ruk'wan Amana, nasan cewa ke Nihal macece mai hakuri amma ina so ki k'ara a kan Wanda kike yi," jikin Nihal ne yayi sanyin wasu hawaye suka zuba mata cikin rawar murya tace, "umma na Dan Allah ki daina fad'a min irin wannan kalaman suna sani shiga rud'ani" Nihal ta ida zancan tare da sakin kuka ta k'ank'ame umma tana cewa, "insha Allah umma na zaki samu sauki wand'an kalaman da kike fadi tare zamu cigaba da yin su bani kad'ai ba tare zamu rayu" Nihal ta k'ara she maganar tare da fashewa da kuka, umma idanuwan ta taf da hawaye take girgizama Nihal kai alamar tayi shuru, tana cewa, "bana so naga kyakyawar d'iyata tana kuka umma na tare dake Rabin rai na kijin insha Allah zan samu sauki har na fara tafiya da k'afafuwa na kuma har naga jikoki na" dariya Nihal ta saki tana goge hawayan ta da bayan hannun ta umma kuma ta kafe ta da idanuwa tana murmushi, sannan Nihal ta tashi tare da daukar tsumma da robar ruwan ta fita, fitowar ta keda wuya aka wurgo mata wasu kaya masu cike da warin giya dana wiwi ko ba'a fad'a ba tasan na mudi ne, Sara ce rik'e da kugun tana yan' harare-harare tace, "malama ga kayan yaya se a samu damar wanke su, ba wai kije ki tsaya gaban shingin gawa ba," wani irin kallo Nihal ta watsawa Sara saboda bata had'a kowa da umma ba, itama gwoggo tana d'aga mata kafa ne saboda matsayin ta a gurin ta da kuma girman dake tsakanin su shiyasa idan ta taba umma take shuru, "keeee!! Malama wakike watsawa irin wannan kallan? karya nayi ne uwar taki ba shingin gawar bace," Nuna ta Nihal tayi da yatsa tana cewa, "duk irin rashin mutuncin da zaki min zan dauka, amma ban da ki tab'a min uwata shuru-shuru magana ce game hankali dan ina shuru ina kyale ki ba shi ze baki damar cima uwata mutunci ba," sannan Nihal ta matso daf da Sara idanuwan ta taf da k'wala sunyi jawur kamar gar washi, matsawa Sara tayi saboda abin da Nihal keyi ya fara bata tsoro sannan tace, "idan yau na so dole Ku had'a ina Ku ina Ku, ku barmin gida saboda gidan nan na uba nane bana uban ki ba, kuma kud'i na kika ci kika girma ba da kud'in uban ki ba idan baki sani ba yau ki sani shashashar banza" fitowar gwoggo daga kewaye ne yasa Nihal sakin kuka tana tatare kayan da Sara ta watso mata, mamaki cika Sara yayi bata tab'a tunanin Nihal na da baki ba se yau Ashe itama ta iya munafirci kenan tab akwai Jan aiki a gaban su, lalai kam ya kamata ta fad'awa gwoggo abin da Nihal ke cewa bayan idanuwan ta, tsawar da gwoggo ta dakawa Nihal ce ta dawo da Sara daga duniyar tunanin, gwoggo cike da masifa tace, "yau ga yar iska yarinya kuka uban mi kike tun da safe sai ka ce uban wani ya tab'a ki ko wanki mudin ne bakiyi yanzu inci uban ki la'ada waje" shuru Nihal tayi tare da aje kayan mudi bakin maguji.
A hankali ya yaye lalausan blenket din dake jikin shi yana kallan sinbul da barma da suke gyara mashi wardrobe, a hankali ya sauko daga saman bed yana cewa Sinbul cikin muryar bacci da sauri suka k'araso gaban Sultan harara ya watsa masu, yayi ma barma nuni da ya matso kai a sunkuye ya matso kusa da Sultan nanade hannu riga gashi Sultan yayi yace, "duk'a" duk'awa Barma yayi Sultan ya saki karfin shi ya sakarwa barma k'uli yana cewa, "na hana ana shigo min bedroom lokaci da ina bacci Baku ji ko cikin masifa Sultan yace, "oya sinbul kai ma zo nan" raraba idanuwa sinbul yake yana cewa, "Ranka yada....! Janyo shi Sultan yayi ya sakar mashi k'uli tare da ja masu kunne yana cewa, "gobe ma idan ina bacci Ku shigo" ya jasu kiii!!! har bakin kofa ya wurgo su parlour kamar kayan wanki yace, "stupid kawai" sannan Sultan ya wuce bathroom ya dade yana wanka sannan ya fito sanye da bathrobe da d'an k'aramin towel yana goge jikin shi, direct gaban dressing mirror ya tsaya lotion ya fara shafawa sannan yasa hand dryer ya busar da gashin shin tare da shafa mashi mayuka masu kamshi da sa gashi kyali masu tsada, wardrobe ya bude ya curo kayan shi jeans n t-shirt, rigar Apple green colour se jeans blue cikin natsuwa ya shirya tare da gyara sajan shi ya kwanta luf-luf masha Allah tuni Sultan ya fito yayi kyau lips din nan na shi yayi kamar ansa Jan baki sannan ya saka booth nashi black masu kyau, masha Allah he looks handsome, a hankali ya bude handle din kofar Dara ya hango da sauran bayi suna jera mashi breakfast a dining kasancewa yau a part nashi zeyi break, suna ganin sultan suka fara zubewa suna kwasar gaisuwa har ya iso dining babu Wanda ya dago cikin su se jakadiya Dara, murmushi Sultan ya saki tare da jan kujera yana, "cewa ina kwana Dara," "Lafiya lau ranka yadade"
"Ina matar kina dai kula min da ita ko? Murmushi Dara ta saki tana saving Sultan chips with pepper soup din yan'ciki, tana cewa, "Eh amma yau se da nasha fama da ita kafin ta sha magani" tana fadin zancan tana turawa Sultan plate a gaban shi,
"Wannan tsohowar akwai rigima"Sultan ya fad'a yana amsar coffee a hannu Dara cikin natsuwa Sultan yake breakfast din shi suna tab'a hira da Dara kasancewar jinin su ya zo d'aya da jakadiya shiyasa har Sultan ke tsayawa suyi hira musanman yadda take kula mashi da ammi duk duniya bayan mahaifiyar shi to ammi ce mace ta farko da yafi so duk wani abin da take so Sultan na nema mata ko da hakan ze sa shi ya cutu musanman da take fama da hawan jini Abu kad'an ze b'ata mata rai jinin ta ya hau shiyasa Sultan ke nema mata farin ciki duk inda yake, bayan ya kalama breakfast din direct part din maimarta ba ya wuce.
Dauke da sallama a bakin shi ya shigo fadar maimartaba, maimartaba yana zaune da waziri suna tattaunawa murmushi sarki ya saki shi da waziri har k'asa Sultan ya tsugunna yana gaishe su, maimartaba yace, "yau kuma shigar yahudawan a kayi kenan" dariya Sultan ya saki tare da zama, waziri yace, "ai su basu ganewa manyan kaya sunfi yi masu kyau," Maimartaba yace, "Ai k'ara Ammar naga shi yana d'an k'ok'arin kamantawa amma shi wannan dayasa ze fara raki wai zafi, se kace kan shi turai ta dira," shi dai Sultan bin su kawai yake da idanuwa kawai se yasa manyan kaya se ka ce Wanda ze je sallah juma'a ko daurin aure saboda su kawai ya siyi manyan kaya, waziri ne ya katse mashi tanani da cewa, "tunda ammar yayi tafiya Sultan shima ya dauke k'afa a gida na Adda har tayi maganar ta gaji," Sosa keya Sultan yayi yana cewa, "Wallahi Abba aiki ne ke rik'e ni tun da nima na dawo yau ne d'ai na samu Hutu insha Allah zan shigo mu gaisa da Adda ka ce mata ta daina fushi dani" dariya waziri yayi yace, "ai kunfi kusa"
Maimarta ba yace, "aiko dana San Ammar zeyi wannan dad'ewar dana matsa wa governor sosai a kan maganar yin titi na akauyan nan dan gabaki d'aya titinan sun ji jiki"
"Kuma kaga ze tsaya har a gama ya dawo"
"Ai yanzu lokaci ya k'ure tun da naji ka ce jibi ze dawo" murmushi Sultan ya saki ji yayi kamar an zuba mashi ruwan sanyi da aka ce jibi ammar ze dawo, da har ya fara tunanin ya bishi yaga waca uwar yake a kauyan har kusan wata, har shi ya dawo shi yana can kauye, sun dad'e sosai suna hira sama-sama sannan Sultan ya masu sallama ya fita.