← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 128

Sashe 49

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ritse idanuwa ta Nihal tayi sakwamakwan wani murdawa da mara ta tayi lokaci daya, ganin tsayuwa na neman gagarata yasa ta fashewa da kuka tare da rike cikin ta, cikin kuka Nihal tace, "Sultan ciki na,! durkushewa Nihal take neman yi a kasa Sultan ya riko ta tare da manna ta a jikin shi lafewa Nihal tayi a jiki sultan tana mai kara tsana ta kuka tana cewa, " Sultan mutuwa zanyi ciki na" rud'ewa Sultan yayi cikin sarkewar harshe a rud'e duk a lokaci daya musanman yadda Nihal ta cikwikwiye mashi suit tana rasgar kuka ciki ta, talabu da habar ta yayi har lokacin idanuwa ta na rintse tana kuka Sultan yace , "mi ya sami cikin naki Nihal kin ci wani Abu ne bayan fitata" sultan ya ida zancan a raunane kuka kawai Nihal take shekawa Sultan tana kara cikwikwiye mashi suit, Har a lokacin hannun su na mak'ale dana juna kwatar da Nihal yayi saman chest d'in shi yana shafa bayan ta a hankali kamar me rad'a yana cewa, "Sorry bari na baki magani ki daina kuka kin ji" Har a lokacin tana rike da cikin ta tana kuka tayi lamo a fafad'an kirjin Sultan, shurun da Sultan ya jine ya sasa d'ago da fuskar Nihal abin da ya ganine ya sasa razana wuyan Nihal ya taba wadda a lokaci bata dad'e da sumewa ba a jikin Sultan, daukar ta yayi a sume ya daura ta saman bed rest d'in office d'in shi a rud'e murza hannuwa ta Sultan ya shigayi Amma shuru har a lokacin Nihal bata numfashi bud'e drawer yayi Ciro alura guda biyu yayi ma Nihal a jijiya tare da bud'e idanuwan ta wayanda suke a lumshe kwanje-kwaje Sultan yayi ma Nihal tare da daura mata drip sannan ya fice daga office d'in, boutique ya wuce ya siyo mata kaya da pad da new pantries hankali shi duk yana kan Nihal duk se yaji tausayin ta ya kamashi, yasan idan ba magani take sha ba period wahala ze rika bata, har ya dawo bata tashi ba aje ledojin hannu shi yayi a hankali ya k'arasa bakin gadan yana karewa kyakyawar fuskar Nihal kallo a hankali ya kai hannu ze taba fuskar ta komiya tuna ya dauke hannu shi da sauri, komawa yayi ya zauna saman kujera yana fata Allah yasa data tashi ta ji ta normal babba abinda ke bashi mamaki Ashe Nihal din yarinya ce sosai tunda har wannan lokacin bata fara period ba, ringing d'in wayar shine ya katse mashi tunani a hankali ya sa hannu ya dauka suna dake jikin scream d'in ne ya sasa smile karawa yayi a kunne tare da cewa, "hello matar ba dai kishi kika fara ba" murmushi Ammi tayi daga dayan bangaran tace, "mun ji ku shuru ne Baku dawo ba naga har dare ya farayi baku dawo ba" jum kad'an Sultan yayi tare da kallan Nihal dake kwance yace, "Ammi bana tunani zamu dawo gida yau" murmushi Ammi tayi me sauti tace, "toh shikenan ina Nihal d'in? bani ita mu gaisa" kara kallan Nihal Sultan yayi tare da cewa, "Ammi tana toilet idan ta fito zan kira ki"
"Toh ammi tace tare da katse wayar Basmal dake gefe Ammi ce tana jin me Sultan ke cewa dariya ta saki tana cewa, "Ammi yayana yau soyayya ake ta sha kenan" duka Ammi ta kai basmal ta kauce Ammi na cewa, "toh uwar gulma bari dai maimartaba ya dawo daga kasa mai tsarki ce mashi zanyi ya mika ki kema kafi ki zama abin da kika zama" dariya Basmal ta saki tare Da rugawa da gudu d'aki tana cewa, "Kai Ammi har kin fara gajiya da ni, to yau part d'in mom zan kwana idan kin fara kewata na dawo" girgiza kai Ammi tayi tace, "Allah ya shirya ki.

Bangaran Nazili kowa tunda su Sultan suka fita ko wajan aiki ta kasa fita tana zaune gida tana faman leka window, ko zata ga motocin Sultan a compound amma shuru d'an siriri tsaki Nazili ta saki tare da zuge labilan d'akin ta, jin an murd'e kofa ne yasa ta juyowa a Hasale tana kallan kofar Aziza ce ta shigo dauke da tray d'in abinci ta aje saman stool har zata fita Nazili tace, "Sultan ya dawo shi da wannan Almajira koko,"
"Gimbiya har yanzu basu dawo ba,"
"mtsww kwashe kayan abincin ki bita da su bana jin yunwa" Nazili ta ida zancan a masifa ce jiki na rawa Aziza ta kwashe kayan abinci ta fice.

"Momi har yanzu kin kasa gane Abu daya bana tunanin wata guba ko What ever da za'a sama Sultan cikin abinci ze kashe shi of coz Dr ne ya san abubuwan nan yana da brain sosai, Ni fa na riga dana gama shiri na time kawai nake jira na aika mugu lahira, kwata-kwata sa Nazili cikin wannan aiki be da anfani" Ashad ya ida zancan yana kora fresh milk d'in dake hannnu shi dan shuru Gimbiya jalila tayi can kuma tace, "ina da dalilin da yasa ni haka son, shiyasa na sako Nazili cikin har kanan ita kanta bata zan manufar mu ba, zan fi so ace Sultan ya mutu cikin ruwan sanyi, idan muka ka sheshi da makamin ana iya binci ke a gano cewa da sa hannun mu, kuma kasan aka gane kashin mu ya bushe"
"Momi kenan! ai mutanan da zan ba aiki ba zaune suke a Nigeria ba, babu abinda ze faru amma for now zan baku dama kuyi anfani da Nazili naga yadda zata kasance amma bana tunanin wannan aiki ze tafi dai-dai" yakumbo dake rabe ce tace, "Ai sultan ya yadda da Nazili ba ze taba kawo ma ran shi zata cuce shi ba, ita kuma sakaryar ba tasan gadazaran da muka k'ulla mata ba, ka ga zata je babu fargaba ko tsoran ze mutu, se dai farin ciki samun nasara soyayyar ta a gare shi" dariya Gimbiya jalila da Ashad suka saki sannan Ashad ya mike yana cewa, "momi gobe zan wuce Dubai kan maganar takadun dana sace a office d'in Sultan bana so kowa ya sani bana kasa idan Sultan ko maimartaba sun tanbaya ki, ki ce masu naje range, kan maganar gona ta, saboda ina so na shirya ma sultan tugun da ko be mutu ba zeyi shekara talatin a gidan yari" dariya Gimbiya jalali ta saki tana cewa, "Ok son shiyasa nake sanka saboda kasan kan wannan harka" Gimbiya jalila ta ida zancan tare da rako d'an nata har bakin kofa suna hira.

A hankali Nihal ke bud'e idanuwan ta k'ok'arin sakowa take daga gado Sultan ya k'arasa tare da rike ta, tsare shi Nihal tayi da lumsasun idanuwan ta tana kallan shi, dauke hannun shi yayi dake saman nata yana tanbayar ta ciki honey voice d'in shi yace, "mike maki ciwo yanzu" shagwabe fuska Nihal tayi tace, "ba komai"
"Ok" Sultan yace mata tare da cire mata drip d'in hannu ta, sannan yace, "tashi ki shiga toilet ki yi brush ki fito, ki sama cikin ki wani abu," daga mashi kai Nihal tayi a hankali ta sako daga saman bed d'in ta shige toilet abinda ta ganine ya sata zuduma ihu ta fito da gudu daga toilet jiki ta na rawa karasowa Sultan yayi gaban ta, Nihal tace, "karka kuskura ka matso kusa dani, mugu Azalimi," Nihal ta ida zancan tana kuka tace, "Me kamin Sultan mi ya kawo jini a panti d'in na? Nihal ta jefawa Sultan tanbayar idanuwan ta taf da kwala ta tsare shi da ido, had'e rai Sultan yayi a zuciyar shi yana cewa me wannan yarinyar ta dauke ni ko iskanci zanyi se na rasa da wa zanyi se da wannan abar mtsww, da kyar Sultan ya dane Zuciyar shi ya kara takowa ihu Nihal ta saki tana cewa, "karka zo kusa wallahi ka zo se na kashe ka" Nihal ta ida zancan ta mannewa da kofar toilet tana fama raba ido tana kuka riko hannun ta Sultan yayi Nihal ta fara fisge-fisge rungume ta tsam Sultan yayi a jikin shi Nihal na fama dukkan Chest d'in shi tana cewa, "ka sake ni malam" hura mata iska bakin shi Sultan ya shigayi a hankali cikin kunnan ta me sanyi, lokaci daya ya sakarwa Nihal da kasala lamo tayi a chest d'in shi tana fama sauke ajiyar zuciya tana dukkan chest d'in shi a hankali, cikin rad'a Sultan yace, "ba wani Abu na maki ba wannan ne dalilin da ya saki ciwo ciki, kuma ba kanki aka fara ba kowace mace ta kai age d'in ki tanayi," shuru Nihal tayi tana saurara Sultan ga wani irin dadi da voice d'in shi ya mata kamar karya daina magana, can kasan makoshi sultan ya cigaba cewa, "idan ma kina tunanin wata rana zaki bani sha'awa ko wani Abu to ya kamata ki farka daga wannan mafarkin babu abin da ze ba Sultan sha'awa a jikin ki, Sultan yafi karfin ki ta kowace kofe" sannan Sultan ya ture Nihal daga jikin shi yana jifan ta da mugun kallo, tsare shi da ido Nihal tayi tana jin tsanar Sultan na ratsata tare da jin kunyar zargin da tamai dole ya gasa mata magana tunda ita tajawa kanta, Leda sultan ya dauka ya mikawa Nihal tare da yima ta bayani ran shi a had'e duk se ta ji kunya ta kamata.
Chapter 49 · 0% Book details