← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 116 OF 128

Sashe 116

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kasancewar ansan da zuwan nasu komai na gidan tsaf Nihal kuwa tayi lamo a jikin sultan tana sauke ajiyar zuciya up stairs sultan ya haye da Nihal bedroom ya shige da ita, ya shinfid'e ta saman bed rage kayan jikin shi yayi ya cire alkyabar jikin shi da babba riga da links din hannun rigar shi ya nanad'e hannu rigar, toilet ya shiga ya hadawa Nihal ruwan wanka masu dan dumi-dumi ya fito daga toilet ko daya fito har a lokacin kuka take jin motsin shine ya sata goge hawayan fuskar ta da sauri takowa sultan yayi gaban ta a hankali yake magana cikin lallashin yace, "please hayaty ki daina kukan nan, bana so ina gani kina zubar da hawayan ki, damuwar da kike sawa kanki ba ke kadai take shafa ba da ni dake da abinda ke cikin ki take shafa please ki daina, ko dan abinda ke cikin ki karya samu matsala please" sultan ya ida zancan yana rage mata kayan jikin ta ya dauke ta cak suka shige toilet.

Iyakar galabaita Sara ta galabaitu ga yunwa ga nakuda sai nishi take tana kuka dan ta riga da ta fara sadakarwa da zata rayu, hankali su Ammi da Adda ya tashi sosai sai addu'a suke Allah yasa ta iya haihuwa da kanta sai nishi take ganin sun Ammi sun kasa, yasa Ashad ya fita ya shiga cikin mota ya dauko kayan aikin da baza a rasa ba a mota ya dawo cikin gidan da taimakwan Ashad Sara ta haihu tare da saki wani irin nishi ta sume da sauri Dara ta dauke baby tana buga bayan ta amma sai dai me rai yayi halin shi, Dara ta rasa mi take dadi mutuwar baby take ji ko bakin ciki duk abinda Tanimu ya shuka hakan be sa taji tsanar ya'yan shi ba.

Bayan sultan ya gama ma Nihal wanka yana kokarin daukar ta nad'e ciki towel ya fara jin knocking ya dan basar jin wayar shi na ringing ne, yasa ya aje Nihal yana cewa, "hayaty bari naje na dawo ki fara yin alwala, zan aje maki komai da zaki bukata nayin sallah sai ki rama salollin ki, nima Dana dawo zanyi fresh up nayi sallah" to Nihal tace mashi cikin sanyi murya sannan ya fito bedroom ganin number Ammar ya sashi ficewa dan bude masu kofa, Nihal kuwa alwala ta dauro dan gabatar da sallah ko da ta fito sultan ya aje mata After dress da milk hijab babba ya shinfid'a mata prayer mat shiryawa tayi tsaf ta kabara sallah tun cikin sallah cikin ta ke juyawa daurewa kawai take ga wani irin jiri dake dibar ta har ta idar da sallah mikewar da zatayi jiri ya debe ta ba tayi masauki ko ina ba sai saman fafadan kirjin sultan a sume talabo sultan yayi a firgice yana cewa, "hayaty..! Hayaty..! Nihal..! yana jijiga ta iya kar rudewa sultan ya rude dan wannan karan kuka yake sosai tamkar karamin yaro ya rasa yarda ma zeyi da ita dan ya manta shi din likita ne, murya shi ne da su Ammar suka juyo a rikice ne ya sasu haurawa sama shi da Basmal hali da suka tsinci sultan a ciki da Nihal ya matukar razana su da kyar Ammar ya karaso gaban sultan dake kuka rike da Nihal a rikice Ammar yace, "sultan me ya same ta? kuka sultan yake yana cewa, "bata motsi zata mutu ta barni Ammar, help me Ammar" ganin yarda hankali sultan ya tashi yasa Ammar sasauta muryar shi dan ya kwantarwa sultan da hankali yace, "asibiti zamu kai ta yanzu-yanzu kaji" sultan da ya zama tamkar saban kamu d'agowa yayi da jajayan idanuwan shi yace, "bata mutu ba baza ta mutu ba ko Ammar eh zamu kai ta asibiti..! yana maganar yana shafa kumatun Nihal Basmal kuwa kuka ta saki Ammar da idanuwan shi sun cika da kwalla yace, "toh dauke ta muje kaji" kamar karamin yaro sultan ya dauki Nihal da sauri suka fice daga gidan cikin mota suka sa Nihal sultan na makale da ita Ammar ya ja mota da gudu zuwa asibitin kauyan.

Suna zuwa asibiti da sauri nurses suka fito amsar Nihal har a lokacin sultan na kuka wasu kuwa sakin baki sukayi babban likitin da suke gani a TV yau gashi cikin asibitin garin su da Ammar aka shiga da Nihal dan bata taimakwan gagawa, zama sultan yayi yana ta kuka a hankali Basmal ta rungume shi tsam a jikin ta tana shafa bayan shi tana cewa, "kukan ya isa haka yayana insha Allah Nihal zata samu sauki, ban san ka da rashin juriya ba Allah yana tare da kai yayana" jan numfashi sultan yayi yana cewa, "insha Allah hayaty tana tare da ni idan na rasa hayaty binta zanyi na fada maki bazan iya rayuwa babu Nihal ba am gonna die if I loose her"
"Calm down..! Basmal take cewa tana shafa bayan sultan cikin sigar lallashi fitowar su Ammar ne ya katse masu hanzari mikewa sukayi a tare suka nufi Ammar jiki a mace suna cewa, "ya jikin nata? shuru Ammar yayi yana kallan sultan da zuciyar shi ke kara tsinkewa murmushi ya saki yana yace, "da sauki yanzu haka tana waiting room" dariya sultan ya saki mai had'e ta kuka da sauri ya kaiwa Ammar hug yana dariya ya zame jikin shi da sauri ya karasa dakin yana murda kofar ya hango Nihal kwance murmushi yake ta saki har dimple din shi na lomawa.

```Taku har kullun salma mas'ud nadabo```🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
*Story*
*And*
*Writing*✍🏾
*By*
*Salma mas'ud nadabo*👑

🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
(```We are the best among the rest```)

*_Assalamu alaikum masoya SAUYIN RAYUWA ba zan gaji da baku hakuri a kan jina shuru ba network ne ke bani problem shiyasa, ko message basa shigo min sai a hankali ina ganin messages naku fan's ba damar reply ko nayi baya zuwa ina yin ku irin sosai din nan_*

*Page: 133_134*

A hankali sultan ya karaso gaban gadan da Nihal ke kwance har a lokacin yana sakin murmushi siraran hawaye na bi mashi kumatu, kama hannu Nihal yayi wanda ke makale da drip ya sakar mata kiss dayan hannu shi yana shafa cikin ta da shi, kneel down sultan yayi yana shafa kanta, a hankali Nihal dake kwance take bud'e lumsasun idanuwan ta ta sauke su kan sultan kallan shi take hawaye na gangaro mata, girgiza mata kai sultan yayi alamar ta daina kuka tare da sa hannu yana goge mata hawayan fuskar ta, nuna idanu Nihal sultan yayi da finger din shi yana cewa, "me nake gani kamar..! Sultan ya fada a dan razane a rud'e Nihal take kokarin taba kumatun ta dariya sultan ya saki har dimple din shi na lomawa ya hada hanci su waje daya dariya Nihal take cikin sanyin murya tace, "ka bani tsoro love na dauka wani abu ya sami fuska ta" ta ida zancan tana shafa gefan fuskar sultan murmushi ya saki ya daura hannu shi saman nata yana cewa, "ke din ce kinki daina kuka bana so kina kuka hayaty ina jin kukan har cikin zuciya ta hayaty a duk lokacin da kike zubar da hawayan ki zuciya ta kona take tana tafarfasa" shuru Nihal tayi tana bin sultan da idanuwan ta a hankali ya daura labban sa saman lips din Nihal yana kissing nata, gyaran murya da akayi ne yasa Nihal rintse ido cike da kunya shima din yaji kunya yar dariya Ammar ya saki yana cewa, "lafiya ta samu sai a basu takadar sallama ko habibty? sun bar mu waje jiki a mace ashe su suna nan suna shan soyayya," dariya Basmal ta saki tana cewa, "masha Allah tunda lafiya ta samu dama fatan mu kenan ko sweetheart" Nihal kuwa tayi shuru sai sultan dake ta wasa ta yatsun hannun ta yana ta smile, Ammar ne ya ce, "dude bari naje nayi sallah ko sallah ban samu damar yi ba tunda muka iso garin nan,"
"Nima banyi ba muje muyi" sultan ya ida zancan yana sakarwa Nihal pack a kumatu ya ce, "me zaki ci? na taho maki da shi" lallausan murmushi ta saki tana kallan sultan tace, "komai..!
"are you sure"
"Yes" sannan sultan ya fice, yar dariya Basmal ta saki tare da sa hannu ta a fuskar Nihal tana cewa, "ya tafi kallan kofar ya isa haka sai a maido hankali waje na" murmushi Nihal ta saki tana cewa, "to yar sa ido wallahi sa idan ki ya fiye yawa" far da ido Basmal tayi tace, "daga fadin gaskiya sai ace sa ido to a daina yi a gaba na sai na daina gani"
"Tab di jam sai dai ki rintse ido kuwa" dariya mai sauti Basmal ta saki tare da ciro wayar ta dake cikin handbag ta kira su mom ta sheda masu suna asibiti Nihal ba lafiya hankali su ya tashi sosai amma Basmal ta kwantar masu da hankali da cewa da sauki su kwantar da hankali su.

Bangaran su Dara bayan Sara ta sauka lafiya sai dai abinda ta haifa bai zo da rai ba wanka akayiwa jaririyar aka mata sutura aka sata cikin kwali liman da su maimartaba suka mata sallah aka wuce da ita makabarta da tsirarin muta nan kauyan kowa na tofa albarkacin bakin shi.
Chapter 116 · 0% Book details