Sashe 9
Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Suna isowa asibiti aka basu ɗaki kasancewar asibitin ƙauye ba wasu kayan aiki ke akwai ba gado aka bashi sai ƙarimn ruwa da aka ɗaura mai da allurar barci sannan doctor ya kira su office da sauri suka ƙarasa ya nuna masu wajan zama tare da gyara zama yace, "A gaskiya ina tunanin wannan ciwo bana nan asibitin bane saboda bamu da masaniyar kwaran daya cije shi kuma nan ba kayan aikin da dayawa kamar birni, sai dai ku je birni amma duk da haka zamu bashi magunguna da kulawa na kwana biyu idan har lokacin abin ya gagare mu zamu tura ku birni domin samamai lafiya" sannan ya gyara zaman glass din shi ya rubuta masu magunguna ya miƙawa Habu, kuɗin gado ya fara biya sannan ya wuce siyan magungunan ya bar yaya Tanimu yana kula da shi, ranar Habu yasha zarya sannan ya dawo asibiti ɗauke da ledojin magunguna dana fruit, da kulololin abinci ajewa yayi a gefe tare da shafa sumar husaini Wanda har yanzu bacci ga ƙarin ruwan da akayi mai idanuwa shi ne suka kawo ruwa da kyar ya samu ya saita kan shi ya zauna gefan gadon yana facing din yaya Tanimu Wanda tuni ya fara ƴan ciye-ciye, cikin sanyin murya Habu yace, "Allah yasa Husaini ya samu lafiya" "amin habu" "ina mamaki irin ciwo da sukeyi ka duba ka gani yaya haka fa shima Hassan rana ɗaya ya kamu da ciwo amma sai gashi yayi ajalin shi hankali na yana tashi yaya Tanimu, anya ba akwai sa hannu wani ba" Tanimu Wanda ya kai lomar shinkafa da wake tari ya shigayi da zazare ido saboda ƙwarewar da maganar Habu ta sasa da sauri Habu ya miƙa mai ruwa yana jera mai sannu sannan ya numfa sa yace, "Habu bai kamata kana irin wayan nan maganganun ba sai ka ce baka da ilimi, insha Allah zai samu sauƙi Husaini ya warware" daga kai Habu yayi tare da share ƴar ƙwallar data tarar mai a ido shi ko Tanimu ko wannan ƴar damuwar da Habu ya shiga daɗi ya ji, dan indai damuwa ce yanzu ya fara shiga.
Kwanan su Habu biyu a asibiti amma kullun ciwo Husaini ƙaruwa yake Dan har kafar ta fara Neman riɓewa, hakan ne ya zaburar da Habu ya nemi kuɗi masu yawa dan akai Husaini birni magani, dan ko yau Husaini na kwance kamar gawa dan be cewa ƙala sai in ciwo ya mai tsanani ya fara sanbatu yana kuka har sai anmai allura, shata mota habu yayi wadda zata kai su har kano dan duk ya gama tsare tsaran tafiya gobe insha Allah zasu wuce dan nemawa Husaini lafiya.
Kusan da yama likis ya dawo gida ya ɗaukar masu abinci ko da ya je asibiti su inna sun zo duba husaini, sai gab da magrib suka ɗau hanyar ƙauyen bayan sunyi sallah isha yayi ma Tanimu sallama saboda shi zai kwana da Husaini a asibiti ya wuce gida.
Cikin sallama ya shigo gida yara duk sunyi bacci sai Umma ka dai zaune a ɗaki tana jiran dawowar shi, murmushi ta saki tare da cewa, "sannu da zuwa abban Nihal" "yauwa matata" tashi tayi tana yunƙuri da komai kayan abincin riƙo hannu ta yayi yace, "Ina zuwa" murmushi Umman Nihal ta saki tace, abinci zan ɗaukoma nasan da yunwa ka dawo," ko daya bana jin yunwa naci abinci a asabiti" "to shikenan" gyara zama tayi tare da kallan shi kwana biyu duk yabi ya canza Allah sarki Habu akwai San ƴan uwa, a hankali ya ɗaura kan shi saman cinyar Umman Nihal yayi shuru wasa ta Shiga yi da sumar kanshi,cikin natsuwa cikin sigar lallashi tace, "abban Nihal" yace, "na'am" yana maiƙara gyara kwanciya a cinyar sahibar tashi "kwana biyun nan duk ka sauya saboda kasawa kanka damuwa miji na addu'a ya kama mu rinƙa yi ba tunani ba kaji miji na" ta faɗa cikin raunanniyar murya, dago idanuwashi yayi yana kallan Umman Nihal yace, "baza ki gane bane wannan abun yana ɗauremin kai yana bani tsoro, idan kika lura kamar ɗauki ɗai-ɗai akeyi mana umman Nihal inajin tsoran mu rasa Husaini," insha Allah ze warware kaji" Hirar su suka cigaba da yi maicike da so da ƙauna daga nan suka lula duniyar ma aurata.
Tun da safe Habu ya fara shiri bayan Umman Nihal ta shirya shi sannan ta shirya yara zuwa makaranta kusan a tare suka fita, be zame ko ina ba sai tasha, yana zuwa ya iske Badamasi har ya iso motar kawai ya shiga suka wuce asibiti Dan ɗauko Husaini,suna Shiga asibitin dakin da aka kwantar da Husaini ya nufa yana shiga yayi turus, sakwamakwan ganin doctor kan Husaini ana ƙoƙarin ceto ran shi yunƙurin ƙarasawa yake Tanimu ya riƙe shi gam in ban da jijjiga babu abin Husaini keyi can yayi shiru girgiza kai doctor yayi tare da rufe husaini da mayafi, zaro ido Habu yayi yana girkiza kai cikin ruɗewa yace, "karka faɗa min shima ya mutu Dan Allah yaya Tanimu ka ce ƙarya ne Husaini na da rai" kuka ne ya kubuce mai ya sulale a kasa yana zabgar kuka, zuciyar Tanimu fes take dan ji ya ke kamar ya rage mugun iri a ganin shi, lallashin Habu ya shigayi shima yana matsar kwalla, shurun da badamasi yaji ne yasasa ya shugo ganin halin da suke cike yasa badamasi jikin shi yayi sanyi haka aka tattaro gawar Husaini aka sa a motar Badamasi sai ƙauye , suna isa gida ya ruɗe da koke-koke, ko da labari ya sami Umma tataro su Nihal tayi daga makaranta suka wuce ƙauye, ba Wanda beyi kukan mutur husaini ba, inna ko hada sanbatu sai da tasha rubutu aka samu sauƙin sunbatun, bayan sadakar uku ƴan uwa da abokan arziki kowa ya koma gida, gidan ya ƙara shuru, Allah sarki malam yana ƙara tsufa yaran nashi masu ƙarfi suna tafiya yayi kuka sosai ya share hawayan shi.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, anata shirye shiryen bikin Haulatu, lokacin Mudi ya kammala secondary ya dawo gida hutu, kafin ya cigaba shine ya fara taimakawa malam da kiwo, dan kusan tare suke zuwa.
Bangaran Habu suna zaune lafiya sai buɗi da yake ƙara samu, duk wata soyayya da gata Nihal na samu gashi kullun ƙara kyau take, duk Wanda ya kalleta sai ya ƙara saboda yarin yar akwai kyau da Shiga rai gata kullun tsaf da ita.
Yau ta kama laraba bikin Haulatu saura kwana uku gyara amarya ake sosai tunda satin bikin ya tsaya umma ko har sun iso suma anata haɗa hada su Gwoggo ko sai Kai kawo ake kowa ka gani cikin farin ciki yake, daran da yayi ne yasa kowa ya natsu ya samu makwaci ana sa ran gobe za'a sa amarya a lalle.
Haulatu dake kwance kusa da Umma ji tayi kamar anmintsine ta tashi tayi tare da miƙewa kiran sunan ta ake, kantane yayi mata nauyi ko mayafi bata dauka ba ta fita daga gidan da gudu ba Wanda ya sani.
*Asuba Ta Gari*
Tashi akayi ba amarya ba dalilin ta abin kamar wasa ya zama gaske sama da ƙasa ba amarya, ne manta aka fara tare da sanar da su Habu tashin hankali, haka aka bazu dangin amarya Dana ango neman amarya inna ko sulalewa tayi ta sume gida ya ɗau salati sauran mazan dake gidan ne suka ƙaraso cikin gida saboda ruɗewar da matan sukayi ɗaukar inna akayi aka shin fide saman gado yayyafa mata ruwa akayi ko da ta farfaɗo hawanjinin ta ya tashi sakwamakwan faɗuwar da tayi idanuwan ta suka makance bari daya na jikin ta ya murgude, kuka gidan ya dauka ƴan biki da ƴan uwa malam a rikice ya shigo yana Kiran inna saboda gabaki ɗaya ya ruɗe, inna ko anmakance ga idanuwa bude amma ba'a gani, malam ruɗewa yayi da kyar aka samu ya dawo hayyacin sa.
Birni da ƙauye babu inda ba'a je neman Haulatu ba harda police station anje ba labarin Haulatu haka su Habu suka dawo gida, duk ba daɗi suna isowa suka fara jin koke-koke a riki ce suka shige gida mi zasu gani inna ba idanuwa gashi ta murguɗe, Habu gabaki ɗaya komai ya mai cak kwakwalwarshi ce kawai ke juyawa wani irin jiri ke dibar shi da kyar ya samu wuri ya zame ya zauna hawaye suna sulalo mai, azuciyar shi yace, "wai meke faruwa da sune wannan wace irin ƙaddara ce ta sauko masu Haulatu ta ɓace inna ta makance gefen jikin ta ya murgude.
Tanimu ɗaki ya shige ya rinƙa kawar dariya shi Gwoggo " kai maigida wallahi kai mugune na ƙarshe dubu Dan Allah yadda ka tarwatsa su kamar kiyashi, ni wallahi inna duk tafi ban dariya kaga yadda ta burgude ne," Tanimu yace, "saima kin ga ta mutu murus," ya ƙara kwashewa da dariya
```Taku har kullun Salma mas'ud nadabo``` ✍🏻
[1/7, 2:24 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
*Story*
*And*
*Writing*✍🏽
*By*
*Salma mas'ud nadabo*👑
*Edit by*
*Aliyu miko Muhammad*
https://mobile.Facebook.com/Real-hausa-fulani-writers-forum-RHFWF-17394973194167/?refid=52&red=opera-speed-dial&-tn_-H-R
*Email*:[email protected]
*Facebook*:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERFORUM.com
*Page: 23_24*
Haka ƴan biki suka watse saboda har yau ba'a ga amarya ba, sai inna dake ta faman jinya komai ya tsakulewa dangin yanzu ba'a wani samun nutsuwa, duk dako har yanzu Habu yana samun rufin asiri amma duk wata walwala da jin daɗi ya daina kullum cikin tunanin halin da Inna ta shiga yake, ko da suka je asibiti magunguna aka basu amma har yanzu jiya a yau, Tanimu ko da Gwoggo duniya ta masu daɗi saura mutum ɗaya su rage mugun iri.