← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 128

Sashe 84

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nihal ce ta shigo dakin Basmal tare da maida kofa ta kud'e da sauri ta jigina da kofar murmushi ta saki Basmal ce ta katse mata tunani da cewa, "Aunty Nihal me sirrin naga kin shigo kina murmushi," murmushi Nihal ta saki tace "ba komai kayan da zaki sa na amso maki"
"Hmmm idan tayi tsami zamu ji" aje kayan Hannun ta Nihal tayi tana cewa, "bama..! bata ida rufe bakin ta ba Minal ta shigo tana cewa, "aunty Nihal yaya na kiran ki yace ki same shi a part din ku," jum kad'an Nihal tayi tana cewa, "ni kuma..? Basmal tace, "toh wacece matar shi a nan dake yake ko dan kin ga idanuwan mutane" Basmal ta ida zancan tana kashe mata ido murgudawa Basmal baki Nihal tayi tana cewa "ban taba ganin amarya me sa'a ido irin naki ba" Nihal ta ida zancan tare da ficewa tana cewa, "shi kuma wannan ya fara shiga rayuwa ta, ko mi zan mashi oho bayan ya gama kunya tani cikin jama'a, duk wata tsirfa ya iyata gaban mutane kuma hakan bashi ze hana a san irin zaman da muke ba..! haka Nihal ta fito tana surutai har ta wuce part din su kaitsaye zaune a parlour ta sami sultan a dining area tsayawa Nihal tayi tana cewa, "gani..! cikin kosawa Nihal tayi maganar dago ido sultan yayi yana kallan ta can kuma yace, "ki zo ki zauna mu ci abinci, nasan baki ci komai ba tun safe..! galala Nihal tayi tana kallan sultan yanzu har shi ke damuwa da cin abincin ta cikin rashin kulawa Nihal tace, "na koshi bana jin yunwa," murmushi sultan ya saki yana cewa, "tunda kin koshi se kiyi feeding nawa..! ni yunwa nake ji" sultan ya ida zancan ba tare da ya kalli fuskar Nihal ba sakatarere Nihal tayi tare da cewa, "kai yaro ne da zanyi feeding naka da can ni ke baka abincin uhm ka ga tafiya ta" Nihal ta ida zancan tana nufar kofar fita da sauri sultan ya sha gaban Nihal tare da sama kofa key ya kule ya tura key din cikin aljuhu a hankali ya shiga takowa Nihal na matsawa har ya manna ta jikin bango rintse ido Nihal tayi jikin ta na rawa ta rasa wannan bibini da sultan ke mata indai haka abota take toh wallahi ta kusa yanke ta ina dalili, a hankali Nihal ta bude ido tana kallan sultan daya raba hannuwan shi a bango ya mata runfa cikin sweet voice din shi sultan yace, "zaki bani abincin ko...! sultan ya ida zancan yana kokarin hada bakin su waje daya rintse ido Nihal tayi ta kauda kai jikin ta na rawa ta kara shigewa jikin bango tace, "aah zan baka dan Allah ka matsa zan baka, wai me haka kake sultan, wai me ke damun ka ne zan baka" ja da baya sultan yayi yana murmushi tare da shafa sumar sa yace, "toh shikenan" ya koma dining ya zauna kallan shi Nihal keyi gaban ta na tsana ta faduwa da alajabin sauyin da sultan ya samu kamar ba miskilin data sani ba, suna hada ido ta kauda kai tana cewa cikin zuciyar ta, "wannan bibini har ina" haka Nihal tayi serving sultan shinkafa da miya taji naman rago da coslow da vegetable, spoon Nihal ta dauka tare da zama sultan na kallan ta ta kasan ido har ta kamala zubawa a hankali ta debo abincin ta nufo bakin sultan kauda kai sultan yayi yana cewa, "mi ya sami hannu ki? da hannu zaki bani" aje spoon din hannu ta Nihal tayi tare da sakin shumin murmushi watsa hannun ta Nihal tayi cikin abincin tana wani juya abinci kamar me dama fura da hannu sannan ta ciro hannu ta daga cikin plate din ta tura ciki bakin ta tana lashe hannu tana yi tana kallan sultan daya tsare ta da ido yayi tagumi yadda Nihal take ma abincin duk dan ta bata mashi rai, yace ta tashi ta bashi guri, bata san komai nata birge shi yake ba se da Nihal ta lashe hannun ta tas sannan ta dagawa sultan gira tare da debo abincin ta nufo bakin sultan da murmushi sultan ya bud'e bakin shi tsare shi da ido Nihal tayi tana cewa cikin zuciyar ta ci zeyi kenan wiki-wiki Nihal tayi da ido tana washe baki taba sultan abinci a baki lumshe ido sultan yayi tare da ware su yana cewa, "abincin yau yafi na kullun dadi, duk san da zan ci abinci ke zan kira kiyi feeding nawa" had'e rai Nihal tayi tare da cigaba da feeding din sultan yana ci abincin hankali shi kwance mamaki kuwa ya hana Nihal kwakwaran motsi, debo abinci Nihal tayi karo na uku ta kai bakin sultan wannan karan har da finger din ta ya hada ya ciza, cikin sigar wasa da jan hankali yar kara Nihal ta saki cike da shagwaba ta mike tana matsar kwalla zata bar wajan, hugging din ta sultan yayi ta baya tare da daura kanshi gefan kafadar ta wani irin shock suka ji lokaci daya daga sultan har Nihal rawa jikin Nihal ya dauka cikin honey voice din shi sultan yace, "am sorry" sultan ya ida zancan yana kama hannun Nihal a hankali ya shiga hura mata iskar bakin shi me sanyi a finger's din ta lumshe ido Nihal tayi wani saban yana yi na shigar ta juyo da ita sultan yayi ya rungume tsam a jikin shi ya lumshe ido yana sauke numfashin a hankali san Nihal na kara shigar shi da kaunar matar shi, lamo Nihal tayi a fafadan kirjin shi zuciyar ta na tsana ta harbawa da kyar ta iya janyo jarumtar ta, ta ture sultan saman kujera sultan ya fada yana kallan Nihal door key Nihal ta dagawa sultan hugging nata da yayi shi yabata damar zare key din a cikin aljihun shi da sauri ta bud'e kofar parlour zata fice ta kara waigowa murmushi sultan ya sakar mata harara Nihal ta maka mashi tare da ficewa da sauri.

Da yamma aka shirya Amarya aka wuce da ita fadda maimartaba ya mata nasiha mai ratsa jiki tun a nan Basmal ta fara kuka haka aka fito da ita Ammi ta dasa nata ta ida zancan da cewa, "mom zaki ce wani abu? mom tace, "to ni se dai nace Allah ya bada zaman lafiya yi nayi bari na bari, se dai ko momi zata ce wani abu," Gimbiya jalila tace "bani da abin cewa Allah ya bada zaman lafiya ya nuna mana na Ashad" daga nan aka wuce da Basmal gidan Waziri hannun bibiyu Adda ta amshi amare, a nan aka basu daki kafin washe gari Ammar ya dauki amarya shi su tafi honeymoon US.

```Taku har kullun salma mas'ud nadabo```
[1/12, 7:41 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
*Story*
*And*
*Writing*✍🏾
*By*
*Salma mas'ud nadabo*👑

🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
(```We are the best among the rest```)

*Page: 103-104*

Washe gari da safe waziri yayi ma Ammar nasiha mai ratsa jiki tare da yi mashi Allah ya kiyaye hanya shi da Amarya, kaitsaye part din shi ya wuce a bedroom ya sami sultan yana hada mashi kaya cikin trolley, murmushi Ammar ya saki yana cewa, "kai amma fa na gode dude, se hidima kake tunda aka fara bikin nan baka samu hutu ba," rufe trolley sultan yayi yana cewa, "kasan bana san irin wannan abun me kuma abin godiya a nan, da kai da amarya ai duk nawa ne to me abin godiya, kara ka tafi kuna huta da kai" dariya Ammar ya saki yana cewa, "hmm zakayi missing nawa ne wallahi na tafi, dama kai har yanzu a bisa iska kake yawo kai da gwaro baku da maraba" pillow sultan ya janyo ya shiga makawa Ammar yana cewa, "ka rai nani wallahi karka manta ni yayan ka ne yanzu, kanwata fa kake aure amma duk wani iskanci ya iya fitowa daga bakin ka, ni dai yanzu kama girmana zan rink'ayi" dariya Ammar yake har da hawaye harara sultan ya sakarwa Ammar yana cewa, "Wai mi ka dauke ni ne d'an rai ni hankali zan rama ne Allah zan baka mamaki, baza ka daina min dariya ba" toshe bakin shi Ammar yayi yana kallan sultan yace, "gwaro..! da gudu ya fice da gudu sultan ya biyo shi Adda dake dauke da tray din abinci zata wuce part din Waziri kafin ya wuce fadda, da gudu Ammar ya boye bayan Adda da gudu sultan ya karaso zagaye Adda suka shigayi Adda tace, "wai yaushe zaku girma ne, har yanzu baku daina wannan yarintar ba ko se kun aje ya'ya zaku bari" tsayawa sultan yayi yana aikawa Ammar harara dake bayan Adda, Adda ta cigaba da cewa, "kai ko kunya baka ji amarya ka fa na cikin gidan nan amma maimakwan ka natsu amma se kara balewa kayi, kuma duk ta kare kai ne mara gaskiya, meya hada ku? Ammar ne ya bud'i baki zeyi magana sultan ya fisgo shi ya toshe mashi baki se kokarin banbare hannu sultan yake girgiza kai Adda tayi tace, "Allah ya shirye ku" sannan ta wuce part din waziri rankwashe sultan ya sakarwa Ammar a kai sosa kanshi Ammar ya shigayi sultan kuma ya had'e rai, a haka sultan da Ammar suka fito sultan yana rike da trolley har suka iso compound dago kan da sultan zeyi ya hango Nihal tare da Basmal ta rako ta suna ta dariya kallo daya Nihal tayi ma sultan ta kauda kai Ammar ne yace, "amma dai na gode Nihal da kokari ke da kanki ki dauko min Amarya ta, har da ina cewa wannan ya tsaya na dauko abita" murmushi Nihal tayi tana cewa, "laaa ba komai Allah ya kiyaye hanya" ta ida zancan tana budewa Basmal murfin mota tana mata bye-bye harara sultan ya watsawa Ammar yana cewa, "zaka dawo ka same ni" sultan ya ida zancan yana bude mashi murfin mota sinbul yasa trolley a booth driver ya ja mota Nihal ko ganin motar su Basmal ta bar harabar compound da sauri Nihal ta wuce part din mom dan gani take kamar sultan ze biyo ta saurin da sultan ya ga Nihal nayi ne ya hana shi bin ta.

***********
Chapter 84 · 0% Book details